Chapter 98
Chapter 98
ya damk'o wuyan hannunta ya kuma fizgeta ya jata zuwa b'angaren Mama, har saida Mama da Nahidt suka bi bayansu a dan guje dan a yadda ya damki hannun nata ta yiwu bai fahimci ba da ita ake damben ba, ita kuwa matarsa ba ta daina kallon hanyar da ya bi ba, wato a banzar bazara ya d'auketa? Ko ya ma kalli fuskarta kamar dai babu halittarta a wurin? Me kenan? Uwar gidan Father ce ta fara k'are mata kallo kamar ta fashe da dariya sannan ta juya ta bar su nan, Umma ma mik'ewa tayi tsaye ta kalleta tana share hawaye, wani murmushin mugunta ta mata tace "Kin gani ko? Ke da banza duk d'aya, gwara ma ni tunda na samu alfarmarsa, kuma baki ga an min auren ba tukunnan, komai na iya faruwa tunda bai cikashe ta hudu ba " Wata dariya ta bushe da ita ta wuce ta barta nan tsaye, haushi, takaici, bak'in ciki duk sai ya nemi halakata daga tsaye, a gaskiya ba dan ba dan ba sai ta ce Muhyeedeen bashi da mutumci, yanzu ita ya watsar haka? Ka rantse da Allah bai tab'a ganinta ba sai yau, ai ko yau ne had'uwarsu ta farko ya dai kalleta dan ya ga yaya kamanninta suke, sannu a hankali ta fara ji a zuciyarta anya kuwa ba za ta taya gayyatar da ake mata akan farautar rayuwarsa ba? Dan inhar abinda ta gani yanzun zata iya kiransa da kishin amaryarsa yake, to fa kenan ita za ta tashi a tutar babu, da kuma ta rasa shi wallahil azim gwara kowace 'y'a mace a duniya ta rasa, ba za ta jura ba ko kad'an, a sukwane ta nufi na ta b'angaren tana share k'wallar da suka taru a idonta tsabar b'acin rai ga na dakuwa da aka yi jiki duk ya jijjiga Murmushi babar Ummie ta yi tana girgiza kanta ta juya ta koma dakinta tana neman wayarta dan kiran gidansu, domin ita abinda ya dameta daban sai ta ga ashe su shirme ne a gabansu Suna shiga d'akin baccinsu ya tura k'ofar ya jefata ciki sannan ya shiga a matuk'ar kausashe yana nunata da yatsa yace "Menene na fita waje a haka? Akan wane dalili ne nan ma sai kin sanar da kowa wacece ke? Hijab d'in ya b'ata ne ko kuma hannayenki ke ciwo da kika gagara sakawa?" Tsatsareshi tayi da ido tana kallonshi da yanayi na tsoro da mamakin me kuma ta aikata ita? Ta ga dai ai ba da ita ake fad'an ba ko? Katse mata tunani yayi ta hanyar wata tsawa da ya mata yace" Ke! Wallahi idan na k'ara ganinki haka ko..." Kwafa yayi mai k'arfin gaske tare da d'orawa yace" Ina zaman zamana tashin hankali ke ta kawo min farmaki kuma duk a dalilinki, tunda kika shigo rayuwata d'abi'ata ta shiru ke neman barina, a da na kan iya k'idaya adadin kalaman da nake furtawa a wuni, amma daga sanda kika tunkaroni komai....ya lalace min, ba gaira babu dalili ki dinga sakani ina tafasa, me nai miki, ke ko kece babar maciyar dake sarata kina nokewa ne? Na kula raina kike so karfi da yaji wani ya aiko ki ne? Ke azaluma ce?" Tafin hannunshi ya saka ya rufe bakinshi har zuwa hancinshi ya dinga sauke numfashi a k'alla sau uku sannan ya d'auke a sanyaye kuma a nutse yace" Na gaji, na gaji da wannan firgici, ba zan iya da wannan tashin hankalin ba, gwara kawai kowa ya kama gabansa daga ni har ke din kin ga na..." Hankali tashe Mama ta banko kai d'akin cike da tsoron furta kalmar da zata sakata sadda kai a gaban yaran da ta fara gani jiya jiya, cike da muryar k'aguwa tace" Kul! Kul Muhay, kar ka kuma furta wani abun bayan wanda ka fad'a, ya isa haka, yanzu fita anan, fita kawai" Yanda ya zuba mata ido kamar baya gane yarenta yasa ta d'an d'aure fuskarta ta nuna masa k'ofa tace" Fita na ce, zan sameka yanzu " Cike da tsoron lamarin da rawar murya Shuwwar ta matsa kusan Mama ta rik'o hannunta gam kamar za ta fashe da kuka tace" Mama, ai kinsan ban yi komai ba ko? Ni ba da ni ake fad'a ba, ban ga abin..." A tsananin tsawace wanda har Nahidt dake k'ofar d'akin sai da ta razana ya juya tare da d'ora yatsarshi a baki yace" Shiru malama!!!" K'am ta sake rik'e hannun Mama tana shigewa jikinta dan ba iya dodon kunnenta ya fasa mata ba har da hantarta ya tarwatsa da kad'uwa, Mama kanta saida ta rintse ido tana salallami dan ta san kam zuciyarta ta taso, ita dama tasan tunda ta ganshi garin nan bilhaki fitina yake nema. Basu bud'a idonsu ba sai da suka ji ya banko k'ofar da mugun k'arfi, a tare suka kalli k'ofar sai kuma Nahidt da ta shigo da mamaki tana sake waigawa tana bin inda ya wuce da kallo. Murmusawa Mama tayi dan kar su fahimci damuwarta ta d'ago d'aya hannunta ta shafi kuncin Shuwwar tace " Y'ata, karki damu kan ki kin ji, ku je yanzu ku yi wanka ku fito za mu ci abinci, idan mun idar sai mu shiga kasuwar ko?" A hankali Shuwwar ta jinjina kanta ta saki hannun Mama, cikin dattako ta fara takawa dan barin d'akin, da kallo suka bita har ta fice wanda hakan yasa Shuwwar sakin wata nauyayyar ajiyar zuciya tana fadin" Allah ga marainiyarka nan dai gareka, Allah ka hanna shi karya ni, idan ya karya ni Nahidt aurenta zata yi ba zata yi jinyata ba" Sai a lokacin Nahidt ta zarro ido da gudu ta nufi wajen wayarta da ta kashe sakamakon mesage din da Malan ya turo mata wanda ya sakata jin matsananciyar kunya da tunanin dama bata da hankali? Ta dauko tana kunnawa da fadin" Allah rufa min asiri kar ya gaji da wulakamcina ya fasa" (😂😂😂😂😂😂😂😂 Da mun shiga uku mu ahalin gidan ALK'ALAMIN KADARATAH) ________________ Indai ya ce zai zauna a gidan wannan lokacin to tabbas yau sai an yi b'atacciya, dan haka ya karb'i makullin mota a hannun wani soja ya figi motar bak'a k'irar crv Honda ya fita a gidan, saida ya fita ya kad'a kan motar zuwa babban titi dan da fari bai san ina ya nufa ba, tafiya kawai yake kamar ya zumduma ihu ko ya ji dama dama, sai ya ji komai cakule masa yake, wata sabuwar d'abi'ar da ba ta sa ba ke son shigar sa ko kuma yace yake son ara, shin hakan na da alak'a da shigowar yarinyar nan rayuwarsa? Ko kuma dai sanin mai kawo masa farmaki kuma kunya da kawaici yasa yake d'aga masa k'afa ne ke hadasa masa haka? Gijimmm! Wannan sautin ya shiga kunnuwansa yayin da nisa da yayi a tunani da b'acin rai ya haddasa masa had'ari, da mugun sauri ya taka birki ya bud'e motar ya fito a sukwane hankalinshi kuma a tashe, duk da yasan hankalinsa baya wurin amma kuma komai zai iya faruwa, ba zai ji mamaki ba idan har aka ce masa wannan had'arin zai iya zama tarko na masu bibiyar rayuwarsa da son ganin bayanshi, amma haka ya dake ya sunkuya kan matar da zai iya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188