Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Alkalamin Kaddarata Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da me zan biya wuta, ruwa, da hayar gidan nan da muke ciki? Kin fini kyau da komai aman na haramta maki yi, ni zan yi na cida ke na shayar da ke na tufatar da ke, yaya kike so na yi ne? Bamu da dangi, iyayenmu sun je cen sun hadu sun yi aure sun zubo mu uwa tumakai sun je sun mace a wajen arfa yanzu kuma ni ce mamanki nice babanki, ni kadai na ragee maki shine zaki kashe ni? Lalle ke yar agula ce *SHUWWAR!*" Gajiya ta yi da zagayen ta yar da icen ta yi ciki da gudu tana gurnanin kukanta ,balema da ta yi arba da akwatunnan lefenta da komai da komai sai kawai ta zube a gabansu tana rusa wani kukan tana dora kanta a saman daya daga cikin akwatunnan ta ce" Haka salisu ya sakeni saboda yayata bata jin magana, Aka zo kan Mus'ab yana kuka ina kuka aka rabani da shi dan kawai yayata budurwar mijin mamansa ce, yanzun kuma Elhaj ya sake ni dan matarsa ta ce masa mamana karuwa ce? Yayata ce ma fa Elhaj ba mahaifiyata bace, wayyo *ALKALAMIN KADARATA MAI CIKE DA RUWAN TAWADA NE, ZANNA NI YAKE YI A GIGICE, TSARANI YAKE YI A HAUTSINE, RUBUTANI YAKE YI A KARKACE, GAMU A KASAR DA BAMU SAN AINAHIN ITACE TA IYAYENMU BA, GAMU A ZAUNE MUNA RAYUWA TAMKAR TUMAKI.......SHIN WANENE WANNAN WANDA TAKE CEWA ZAI ZAUNA DA NI BA RUWANSA DA WANDA YAKE RIKONA? SAI DAI IDAN DAN BARIKIN NE SHIMA, SAI DAI IDAN BASHI DA MAFADA A DUNIYA NE*....." Ta idasa maganar kasa kasa sosai ta yadda zaka gane daga kasan zuciyarta take jin ciwon abinda yake damunta, a nan tana kwoncen nan hawaye wani na korar wani ta sauke dara daran idannuwanta a saman kunshin da akai mata mai ruwan maroon wanda ya wani irin daukan kalar fatarta ya haskata tamkar kwai Da karfi ta budi bakinta tana ambatar sunnan yayarta wace ke tsaye a kofa sun yi cirko cirko ita da Fauziya A tare suka kalli Junna ta daga kafarta zata shiga Fauziya ta yi saurin rikota tana fadin" Kar ki je NAHIDT, kin fa san idan ranta ya bace komai yi take yi" Nahidt din ta share kwalar da bata so kowa ya gani tana fadin" Yaya kike so na yi Fauziya? Zuwa zan yi, ba zata iya ilatani ba, ranta ne a bace zata sauko in sha Allah, ko yanzun da ta kama sunnana na san ta fara saukowa ne kin fa santa sarai" Fauziyar dai na bayanta a hankali har suka idasa shiga dakin A yadda suka sameta sai da su dukansu suka kamu da tausayinta mai matukar yawan gaske A hankali yayar tata take dan matsawa tana fadin" Na'am?" Shiru ta yi mata bata amsata ba, hakan ya sa ta sake matsawa sosai muryarta a sanyaye matuka ta ce" *SHUWAR* gani na zo, ji na yi kamar kin kirayeni" Wace aka yi kira da SHUWAR din ce ta dan miko hannunta idannuwanta a rintse muryarta na rawa ta ce" NAHIDT, kunshin nan ki goge min shi kin ji? Na tsane shi. Bana son ganninsa a hannuna........" Da sauri ta zauna tana birkito kanwar tata jikinta ta ce" To yanzu kuwa, SHUWAR yanzu kuwa, Fauzy je ciki hado min abubuwan da zan mata anfani da su na wanke mata kunshin kin ji?" Da sauri Fauzyn ta yi ciki dan daukowar ita kuma SHUWAR din kanta a saman kirjinta muryarta cen ciki ta sake bude bakinta ta ce" Sunna da gaskiya da suka ce ba zan ce kadara ce ta saka ki haka ba, NAHIDT son rai ya shiga cikin lamarin, aman mazan kansu kin san sun zama yan iska ko? Me na yi zasu ringa sako ni bayan kafin su samu soyayata sai sun yi kamar zasu yi hauka?" Nahidt a sanyaye ta ce" SHUWAR dukankima shekarunki nawa? Just 22 fa, SHUWAR sai kina cewa mace tsufa take ke aure kike so, SHUWAR na san aure kike so aman kina da damar jan ko dan uban wanene a kasa yadda kike so, SHUWAR ki bari mai mutuncin da ya san mutunci dan mutuci mai daraja ya bayanar maki a lokacin da ya dace, ki daina gagawar nan, SHUWAR ke matar sarki ce ko gwamna, SHUWAR ki daina kukan haka a kan d'a namiji , ya jima bai sake ki ba wani zai kama ki ya so ki ai!" Kanta ta dago tana kallon kyakyawar fuskar yayar tata mai shekara talatin da daya a duniya , aman kula da kai ya saka freshhh take da ita, sai dai duda wannan kamaninta ba nutsatsen kamar mai Nutsuwa bane sakamakon kauce hanyar da ta dauka sana'a A hankali ta ce" Kina nufin na ci gaba da cin haram?, Na ci gaba da gannin kin shigo a talatainin dare kin shiga kin wanke najasa kin zo kin kwonta a kusa da ni? Kina nufin haka zamu ci gaba da rayuwa da wanda ya isa da wanda bai isa ba ya dubeni ya zagar min ke dan kin wulakantar da kanki? Wai Kinma san me Elhaj mai shinkafa ya ce da ke ne? Dalilin zagin da ya maki na rantse da Allah gobe sai na gigita rayuwarsa fiye da tunaninsa, haka kike so kina amso ni a police station kamar barauniya? ......" Dubanta ta maida kan Fauziya da ta gama zuba Dop a cikin ruwan dumin da ta tafasa ta ce" Fauziya, kin san da sai na halaka farin cikin Mai shinkafa?, mai shinkafa ya taka wuta bai sani ba, da ace hakurin da na bashi kar ya yanka min tikitin zawarci a karro na uku ya saurareni ne da na sasauta masa, aman walahi a yanzun ko sai kun yi belina, ina ji a jikina zan janyo maku magana ne" Hankali a tashe Fauziya ta ce" Kin ga ki rufa mana asiri, baki ji ba za'a yi taron nan na shugaban kasa? Kin san waye ya sauka a garin nan? Ki bari bayan taron nan sai mu je mu samu mai shinkafa mu koya masa hankali, aman a yanzu ki rufa mana asiri da bawan Allahn nan, cewa aka yi mahaukaci ne, kurmane, makaho ne a gaban wanda bashi da gaskiya, ki yi hakuri kar ki dago *ALKALAMIN KADARARSA TA BI TA SAMAN KANKI* sannan ta biyo ta kanmu SHUWAR!" SHUWAR ta lumshe idannuwanta masu shige da na mashayiya luuuuuuuuuuuuu tana saka kafafuwanta da hannayenta a cikin ruwan yayarta na anfani da lemun tsami ta fara darje mata kunshin ta ce" Baki sani bane, kin ga tun daga ranar da wannan basamuden ya damki kugun auntyna ya riketa dam ya jamu ya maka mu a gidan da aka kwaso mu ba ko sisi aka zubo mu kasar nan? Na tsani du wani halitar da zai amsa kiran mai anfani da kaki, bana jin tsoron mai rigar soja, bana jin shayin kai masa wargi, ko uban waye shi ni SHUWAR zan iya dubansa ido cikin ido na ce da shi Jaki , idan shi dan iska ne dan Allah ya yi gigin taba ni, ni kuma sai na karar da jikokinsa a wahala sai dai idan kasa ta lulube idannuwana kafin mu kai lokacin!" "Ikon Allah"

Table of Contents

Chapters

188 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});