Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 118

Chapter 118

Alkalamin Kaddarata Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ce MUHAY kai din son zuciyata ne na yarda wanda kike so ki baje a saman bed dinki zan yarda aman ba kice min ni kadararki bane, ni son zuciyarki ne Useina wanda aikata aikin banza ya saka kike jin sha'awata, ilar aikata aikin banzan da kike yi kennan Allah ya saka maki kwadayin abinda yake guba a gareki, Babar matsalar kuma bayan shirme kin fara hauka a kan lamarinki, USEINA ba zan taba kasancewa mai yi maki biyaya ba ko ki fahimta ta laluma ko duniya ta ganar da ke!" Daga haka ya matsa ya juya ya barta a wajen, wanda barin nata da ya yi ya sakata dukewa a wajen tana cire dan kwalinta hadi da sakin kuka tana mai rukunkume hannun nata a jikinta Da dan karfi ta ce" Sai dai ka kashe ni, kana tunanin tunda na tunkari kowa da maganarka zan ji tsoron birgarka ne?, Kennan har dauka kake soyayarka da bukatar da nake biyawa kaina da wasu mazan daya ne?, Zaka gani, yadda ka kawo har yanzu baka mu'amalanci mace ba, ba zaka taba mu'amulantar wata ba, ko yar gidan uban waye!" Sai da ta ci kukanta sannan ta mike da dan kwalin ta nufi ciki ta nemi wajen ruwa ta kunna ta wanke fuskarta sosai ta gyara daurin dan kwalinta sannan ta juya da niyar fara isar da sakonta a yau yau ba sai gobe ba! A lokacin da ta shigo Mama ta gama sallar la'asar kennan Shuwwa na tsakar yi ta karaso da sauri ta zauna a kusa da yar uwarta ta riko hanneyenta ta fashe da kuka Kukan da ya saka Mama zabura a tsorace tana kallonta A gigice Mama ta shiga fadin" USEINA menene? Tun dazu na fita na nemeku sama ko kasa ban ganku ba menene? Kukan me kike? Ina yake ne?" Useina ta sake waigawa wajen da SHUWWA ta kai sujadarta ta karshe ta ce" Yanzu Hasana dama SON zai yi auren matar da saboda ita zai nuna min komai na iya faruwa idan har ban fita a harkarta ba?, Dama zan ga irin ranar nan?" Mama ta kalleta a hankalce ta ce" Useina kin ga, ki nutsu dan Allah ki fada min me yake faruwa yau kuma?" Useina ta sake yin yadda ta saba dan ta hauda Maman da sirikanta, ba kunya ba jin tsoron Allah bale na Muhay da ya gama ja mata kashedi ta ce" Tunda na shigo dakin nan yarinyar nan ke kin wani irin kallo, tunda ta ji kin yi maganar rigar jikina ta dameni tana gannin kin fita ta ce da ni kamar yar bariki?, Ta dora da fadin bama kama bane yar bariki ce ni, raina ya bace na budi baki da niyar yi mata magana shikenan Son ya tare ya hanna, hakan ya bani mamaki na tsatsareshi da ido uwa uba a gabana ya rukunkumeta ya shiga kissing dinta, Hasana da kika shigo ya saketa ya jani ya gindaya min kashedin a kan matarsa yana iya yanke zumunci da ni kwata kwata, cewar a kanta babu abinda ba zai iya yiwa kowa ba ciki kuwa harda ke da kika haife shi, ya ce yana iya zabarta ya bar kowa, in ina gardama na tambaya ina tsohuwar matarsa?, Hasana kina kallo ya sake auro mana masifa?" Irin kallon da Mama ke yi mata dole ya saka mutun a cikin tunanin fasarar kallon Mama ta tsareta da duban nan ne tamkar tana son gane ita din wata irin halita ce? Tsoro, tashin hankali kala kala suka ziyarceta, Tabas abinda Shuwwa ta fada bata yarda da shi ba domin maganar da ta fada sam karyar bata tsaru ba, ta dai hakura ta bar maganar a haka ne dan ta cire wasi wasi da shakun dake cikin zuciyarta Sai dai a yanzu wanda kanwarta ta fada ya sakata a cikin tashin hankali Gaba daya maganar da ta fada tana iya zamtowa gaskiya duba da a saman Shuwwa din ta shigo ta same shi, sannan a gaban idannuwanta ya damki hannun yar uwarta ya fita da ita, bayanma wannan a kan wani dalili zata yi masu karya ne? Shin da gaske ne abinda ta fada cewar MUHAY ya fada a kan Yarinyar nan? Hankalinta idan ya yi dubu ya tashi har kunnayenta suka jiyo mata salamewar sallar Shuwwa ta juyo da sauri baki da hanci a bude tamkar zata hadiye su da su tana kallonsu da mahaukacin mamakin da ya ki buya Ta san bata da bakin da zata taro maganar nan, da farkoma ita ta saka kanta a cikin ramin nan, anya kuwa tana iya fitar da kanta? Mama dake kallonsu jin zuciyarta zata buga ya saka ta mike da sauri ta nufi hanyar fita ba tare da ta yiwa kowa magana ba, wanda hakan ya daka Shuwwa mikewa da sauri da niyar bin bayanta, sai dai riko mata mayafi da akai aka dawo da ita ya sakata juyowa da sauri tana kallon matar nan da fuskarta ta zame mata tamkar ta kumurci Yar dariya ta yi tana kallonta ta ce" Dama kin yi hakuri kin anfani kyanki ta hanyar da ta dace da ke, da kin guji zakin da ba mahadin Barewa ba to da ina iya yi maki hanyar da zaki mori kyan naki......kina neman yiwa al'amarin da baki da ci a cikinsa shishigi? Meye mahadin hanyar mai cin ciyawa da mai cin nama? Uban dawa yake sai zakanya zata iya da shi ba ke ba!" Tana gama fada ta zo da niyar wuceta ta tafi, sai dai abinda ya dakatar da ita jin muryar Shuwwa wace ta cika da mamaki da bugawar zuciya tana kallonta ta ce" Ji mana?" Dan dakatawa ta yi ta juyo tana kallonta da cikaken rashin tsoro irin na rikakiyar yar bariki tana kallon Shuwwa din da jin wata magana ta rainin wayau tana neman yi mata wai ji mana? Shuwwa ta dan sake dubanta tana kiyasta shekarunta a zuciyarta a nutse ta ce" Mama?, Sorry wacece zakanyar? Wacece barewar?" USEINA ta yi wani yannayi na ta dan shaka kadan kafin ta dan girgiza kanta a kausashe ta ce" Kece Barewar, da kike nama a gaban zakanya, watau ni!, Da zaki yi biyaya zaki iya tsira da mutuncinki?" Tabas bata yi hasashen jin cewa Useina ce zakanyar ba, ta zata ko y'arta take YIWA yaki, sai dai da ta fadi hakan kamar ta gaura mata mari ne, domin sai da ta ji kamar zata kifa kafin take iya rike kanta tana kallonta ta ce" Mama, wai ke Zakanya a matsayin uwar zaki kike nufi bakya so danki zaki ya rabi Barewa ko yaya fahimtar da ni?" Haushi ya saka Useina nunata da yatsa ta ce" Ke saurara min, ba shirme ya tsayar da ni a nan ba, idan baki fahimta ba zaki gane !" Da sauri Shuwwa ta bi bayanta gannin ta sake juyawa zata tafi da sauri ta saka hannunta ta janyota baya ta yada ta juyo a haukace da mamaki tana kallonta Tun daga kasa har sama Shuwwa ta daukota da kallo kafin ta sauke a saman fuskarta Yar yatsarta manuniya ta nuna mata zaryan tana kallonta a kausashe ta ce" Ki cewa haukan dake kullawa ko kuncewa a cikin kwakwaluwarki cewar na amshi tayin,

Table of Contents

Chapters

188 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});