Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 163

Chapter 163

Alkalamin Kaddarata Book 1 Complete Hausa Novel 1,196 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

basa so a kai ga saka karfi a wajen Da sauri ya ce" Kunna iya tafiya" Du sara masa suka yi sannan suka juya da saurin summa suka bar falon Sake juyowa ya yi dan sake bama idannuwansa kalaci A lokacin ita dinma shi take kallo da yannayi na matsanancin begen ganninsa cikin manyan kaya , wanda bata taba ganninsa da su ba Yana tsayen ya kasa motsawa dan ta gama summar da shi da ruwan kyan da ta yi ta karaso a hankali ta tsaya tana dan murmushi tana kallonsa Fuskarsa ya shagwabe a dan rikice ya ce" Anya kuwa zaki je wajen nan? Ko kuma mu je mu samu katon hijab da nikaf ne? Ni ni ni......" A hankali ta langwabar da kanta tana murmushi da son jin ya furta soyayarta da kishinta zasu iya saka shi hannata zuwa wajen daurin auren yar uwarta, sai kuma ya yi shiru yana sake takwakwabe fuskarsa Dan murmushin ta kuma yi a sanyaye ta ce" Ni na ce me?" Sake kallonta ya yi shima yana so ta bashi haske, aman yar mutuniyar tasa sai ta tsaya iya nan Hakan ya saka shi fadin" Nine a wahalce, nine zan fi jigatuwa....... IBTISAM kin yi kyau har kamar na ce kin fi kyau kyau" Kwarai ta yi mamakin jin furucinsa, sai dai kwanakin nan ta gama gane yana da magana a gaban abinda ya yarda da shi, dan haka sai ta yi luuuu da idannuwanta ta ajiye mayafinta tana fadin" Dan haka bara na lulubewa maza gannina a bagas......." Kyakyawan murmushi ya kasheta da shi yana kallon bayanta har ta shige dakinta kafin yake juyawa ya yi nasa dakin da gagawa shima Bindigarsa ya daure a jikinsa da alburushi sannan ya rufe ya dauko hularsa ya sake bade jikinsa da mahaukacin turarensa ya fitowa fito yana kanga waya a kunnensa dan jin idan sarkin rawanin ya karaso yana yiwa Aba kuwa? Sake zuba mata ido ya yi, ta saka abaya bak'a sidik ta nada mayafinta a kan kayan da ta saka , abayan bata da ado ko diz a jikinta sannan budadiya ce sosai, haka kuma nadin da ta yiwa dan kwalin abayar ya amsheta harma ya so ya fi shigar ta dazu kyau Ajiyar Zuciya ya sauke yana ayana' kyanki ki yi zamanki a dakina na yi ta kallonki ba dare ba rana, idan na fita na dawo na tardo ki, ni kuma sai na je na maki neman dan walahi ko dako zan yi ba zan yarda ki fita ba IBTISAM zan yi na faranta maki mudin raina' A bayane kuwa sai ya gyara tsayuwarsa ya daga hannunsa wajen kansa ya sarra mata, wanda hakan sai da ya saka ta saki murmushin ba shiri kafin ta sara masa itama Hannayensa ya bude mata ta zo da dan sauri ta fara ciki, ya mayar ya rufe ruffff a hankali ya furta" Mu je mu daura auren y'armu" Itama a hankalin ta ce" Aa mu je mu daura auren Abanmu da y'armu" Murmushi sukai suka fice dan an jima da gyara abin daukansu su din kadai ake jira Sai da ta shiga ya rage tsayinsa ya gyara mata abayarta sannan ya rufe ya zagaya ya bude ya shiga shima kafin suke dagawa Tun daga kan kwanar gidan Dad ta ringa gannin tarin sojawan da suke shawagi aka zuba ta ko'ina, sannan lamari na bikin manya tunni baki sun fara yiwa gidan caaaa Kasancewar da kansa ya dora dokar duk wanda ya zo ko waye daga bakin gate din da suka saka zai sauka ya karasa gidan a kafa a dole doka ta hau shi Dan haka ya zagaya ya bude mata a hankali ya furta" Bismillah Madam MUHYIDEEN MUHAY" Idannuwanta ta lumshe sannan ta dora hannun nata saman nasa ta fito lokaci daya ya saka hannunsa yana rike mata jakar tata ,ya kasance hannunta na dana na cikin hannunsa na hagu datan hannun nasa kuwa yana rike da yar pos din tata suka ringa takawa a hankali, shi ya saka farar shada ne kal ita kuma da abayarta a saman shadarta, a jikinta tafukan hannayenta da fuskarta ne kawai ba a lulube ba, ga sojojin dake sanye da kaki sun zagaye su a dole ko baka san da zuwansu ba yadda ake kakauda mutane zai sa ka juyo dan gannin ko su wanene , hakan ya sa kallo ya dawo kansu, aka kuma yi mamaki da kuma rakasu da kallon sha'awa da adu'a , masu daukansu hoto na watsawa haka maroka na ta kokarin kawo gaisuwa , shi kuma burinsa ya kaita ciki ya cireta daga dumbin kartin nan ko zai samu nutsuwa Sai da ya sadata da cikin gida har kofar baban falon Mahaifiyarsa wanda ya tabata a ciki suke ya ja ya tsaya ya nemi izinin shiga Ana basu dama ya fara shiga da salama a bakinsa kasa kasa da kuma miskilancinsa Sai dai mutanen da ya gani da irin shigarsu ta alkyaba ta saka shi dole sakin murmushi yana karra kallon su Nahidt dake rike da Alkyabarta tunda garin Allah ya waye ce ta mikawa mamansa da ta miko hannu idannuwanta na cika da kwalar farin cikin gannin yau MUHYIDEEN ne ya shigo da macen dake tasa ya yi mata jagora ya rakota da dukan alamu na yana kishin a tatare da shi! Lalle d'anta ya zaka cikaken namiji baban burinta kuma ya cika ita kam, domin haihuwa ai ta Allah ce idan ya samu kafin ta mutu alhmdulilah idanma bata gani ba alhmdulilah, ita kam da ta ga cewa yaronta ba abinda take tsoro bane yake damunsa ta fi kowa farin ciki, yanzu haka yar uwarta na gidan tunda safe ta zo itama tana dakinta barci take bata farka ba, bata nuna mata komai ba aman kuma bata nuna mata yannayin da take nuna mata a da na kaka naka yi da lamarin yaron nata ba, ko da ta kwatanta rabonta da shi tun a asibiti sai ta yi murmushi ta ce ai kin san yaron naki yanzun sai a hankali, bale an shiga babi na iyali? Kin san sun tare da matarsa ga baban matsayin nan da ya sake hawa kansa, dole sai da auzuri wani lokacin......... Ai kam tunda ta ji haka ta yi gummm ta shiga barcin karya, domin ba barci take ba tana fama da tukukin zuciya da tuna kamanin yarinyar da shayinta a zuciyarta, ita tsoroma take kar ta fito su hadu da yarinyar ta yi mata wani abin daban.....aman ta ji wani iri jin wai ya tare da wata? Du irin abinda ta kula? Me kennan? Tana son samun informations na abinda ya faru Alkyabar dake hannun Maman MUHYIDEEN ta mika masa tana murmushi hawayen dake cikin idannuwanta suka zubo Daidia maman Shuwwa din ta fito daga bangaren kicin ita kam ba Alkyabar a jikinta domin an ce ba yanzu ba mijinta ne zai dorata a kan matsayin da yake nata nan ba da jimawa ba, itama bata damu ba ta baki take yi iyayen Hamza sun zo, danginta sun zo, duda basu yi wani zama ba aman du kowa kokarin kamanta kyautatawa dan uwansa yake yi Murmushi ta saki gannin MUHYIDEEN ya yiwa mahaifiyarsa murmushi sannan ya shafa gefen fuskarta ya share

Table of Contents

Chapters

188 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});