Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 71

Chapter 71

Alkalamin Kaddarata Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

take so ta kwatanta mata dala dala waye MUHAY ne?, Da yaya take so ta kwatanta mata shi din ba kalar maza yan soyaya bane? MUHAY bai yi kama da wanda zai iya tatalin mace ko ya nuna mata yana sonta ba, domin shi matan suke yiwa haka ta yaya shi zai fara yiwa wata? Shikenan ita sai ta zama banza a banza kenan? Ta zauna da k'aton sai dai ita ta ringa rarashinsa shi ba zai rarasheta ba? Ai ba haka bane rayuwa gaba daya ba haka bane ba, ita burinta ta samu namijin da zai kasance mai yawan maimaita mata kalmar so, wanda zai ringa fada mata ba dare ba rana cewar itace so dinsa, wanda zai zama tamkar redio idan tana gefensa, aman wanna mutumen idan ya budi baki dan ya mata masifa ne, a kwana biyun nan da ta yi da shi zata iya cewa kyautata masa b'ata masa rai yake! A hankali Nahidt ta ce" Da kin san abinda ya koro ni gidan nan da sasafe da baki nemi na koma ba, dan na san ranki sai ya baci Shuwwa." Shuwwar ta cire taguminta tana kallonta ta ce" Wani abu aka yi maki?" Nahidt ta sauke ajiyar zuciya tana aron jarumta zata fara magana wayarta ta shiga kuka. Kin dubawa ta yi domin a tunaninta yayansu ne ko Fauziya, bata san cewa Malan bane, da ta dauka ta gindaya masa sharudan da ta gama zanawa ranta sannan ta fada masa ya ji kunya wollah, ta danne wayar ta hade hannayenta ta ce" Abanki, Shuwwa Abanki ne ya ba matarsa waya ta zageni ta ce min karuwa?" Gaban SHUWWAR ne ya fadi tana kallonta ta ce" Aunty, kalle ni, kalle ni, dan Allah ki fada min gaskiya kin ji? Aban nawa?" Nahidt ta taba hannu tana fadin" To karya zan maki ne?, Na rantse da Allah tsakiyar dare muna maganarki da shi jiya kawai ya tashi ya kai mata wayar dakinta ta aniya duran ashar harda mamanmu da abanmu ta zaga, ta kuma ce min karuwa wai ina kiran mijinta tsakiyar dare!" Zuciyarta ce ta fara tafasa a zaunen da take tana kallon auntynta ta dan wara zamanta tana kallonta ta ce" Nahidht, dan Allah ki rufa min asiri ki fada min yadda abin ya kasance kin ji? Kar ki saka na aikata abin kunya, domin idan matar nan ta taba ni ta kwana lafiya banda ke, bana tunanin zan iya kyaleta a yau Nahidt, me ya hadda ku waya da Abahna? Kin tabata shi ya kai mata waya? Abana ba zai aikata haka ba Nahidt, ki fadan yadda abun ya kasance." D'auke hannunta ta yi daga na ta hannun da mamaki ta kalleta tace "Kai! Shuwwa a ganinki k'arya na fad'a? Zan miki karya ne dama ? Wallahi gaskiya nake fad'a miki, ke abun kunya fa Abanki ya riga daya aikatashi, sai dai fatan kiyaye na gaba kawai." A zafafe take kallonta har ta muskuta ta gyara zamanta, wara k'afafunta tayi sosai irin zaman nan wanda ko masifa kake za ka ji dad'in jijjiga jikinka yanda kake so, hannun rigarta d'aya ya fad'i har ya sauko kan damtsenta, ba wai dan ta mata yawa ba sai dan kalar zaman da ta yi ta dafe hannunta d'aya akan cinye. Kafin ta ce wani abu suka ji takon saukowarshi daga sama, da d'an sauri sauri yake saukowa saboda wasu takardu da ya ke son ba wa d'aya a cikin yaransa ya kai masa ofice. Sam bai kula da tsiyarsu dan yi yayi kamar bai gansu ba ya nufi hanyar ficewa daga falon gaba d'aya, a yanayin neman fitina da rigima ba tare data gyara zamanta ba tace "Ji mana." Har zuciyarshi bai yarda da shi take ba, dan haka ya wuce abinsa har ya kama k'ofa zai fita ta d'aga muryarta yanda zai ji ta ya kuma fahimceta tace "Ji mana malam soja." Cak ya tsaya hannunshi na kan hannun k'ofar amma ya kasa jawowa ya bud'e, a saib'ance ya juyo ya zuba idanunsa akan ta. Nahidt da ke kallon Shuwwa da mamaki ta rarako ido ta rufe baki mamaki na neman kasheta tace "Muhammadu Rasulillahi sallalahu alaihi wa sallam! Allah ka jik'aina tun man mutu ba." Sassauta muryarta tayi a hankali tace "Shuwwa ashe dai haukan da na ji ana rad'e rad'i a kan ki gaskiya ne? Yanzu ke dan ubanki wannan d'in ne daga zaune kike kira da ji mana...Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Zunbur ta mik'e ta d'auki mayafinta tace "Bari in koma d'akina, wannan lamari na ki sai addu'a." Kallon fuskar Nahidt yayi sanda ta kawo kusa da shi, d'an kaucewa yayi kad'an tare da sakin hannun k'ofar ta rab'a ta fita, saida ya ji ta rufe k'ofar ya dawo da dubanshi a kan ta. Tasowa tayi tana gyara hannun rigarta daya fad'i ta kai kusa da shi sannan ta tsaya, kallon fuskarshi tayi tace "Dama ina so zan fita ne anjima, zan je wajen Abana." Gefensa ya d'an kalla yana sakin murmushin gefen labb'a mai ciwon gaske, yayin da zuciyarsa ke ci gaba da raya masa duk Dady ne ya ja masa wannan wak'i'ar, amma yanzu zai wa tubkar hanci ta yadda za ta banbance aya da tsakuwa. Damatsenta ya damk'a da k'arfin da ya san za ta iya d'auka, ihu ta saki na balakin daya ziyarceta amma sai ta ji bakinta ya sake yin d'uff ta kasa furta komai. Gaba d'ayanta ya d'agata, irin d'agawar nan dake raba mutum da k'asa, kuma gata a hannayenshi ya rik'e damatsenta, wutsil wutsil da ta ji k'afafunta na yi a doron k'asa yasa ta duk'ar da kanta dan ta tabbatar wai gaske d'agata ya yi, duk'awar da ta yi ce ta sa hular kanta fad'owa har saida ta shafi fuskarshi kafin ta dire k'asa. A kid'ime ta d'ago dan ta kalli fuskarshi ta rok'eshi Allah Annabi ya sauketa k'asa dan yanzu ta tabbatar a sama take. D'agowar da ta yi da sauri ta sa gashinta daya fincike tsabar jijjigar daya fara mata ya rufe masa fuska, iskar bakinshi ya huro da k'arfi ya hure gashin daga fuskarshi, hakan yasa ta rintse ido saboda iskan daya huro mata a fuska. Ido cikin ido suka kalli junansu wanda ita na ta suka rarako waje su d'an d'auki launin ja, bakinta dake bud'e alamar tsoro da firgita yake kallo, d'an tsurut da shi amma a haka take iya yanko masa magana iri iri. Jijjigata yayi, kamar dai yanda zaka zazzage shinkafa ko dankali a cikin buhu, hakan yasa Shuwwa rintse ido kan ta ya shiga gigil gigil gaba d'aya jikinta na d'aukar jijjigar musamman k'afafunta dake sama, a k'asan mak'oshinta ta dinga fad'in "Aaaaaa! Kakkkkk...sssory." Dakatawa yayi daga jijjigar da ya ke mata yana kallon fuskarta dan samun gamsuwar ta jijjigu ko da saura, daga tsayen nan ba tare da ya rusuna ba ya saketa da tunanin ta fad'o yanda zata d'an samu karaya ko shida ce a k'afa, amma ikon Allah sai ta fad'a kan k'afafunta amma rashin k'warin jiki da kuma dawowar da bata yi ba daidai saboda wannan shocking da ya bata, sai kawai ta yi zaman yan bori k'asa har saida ta sake lik'e idanunta gam ta dafe k'ugunta tace "Washhhhh!" A hankali

Table of Contents

Chapters

188 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});