Chapter 147
Chapter 147
sai dai da yawancin lokuta nakan tsinci koke irin na jaje da nuni a kan wani dalili mahaifinsu ya fi son mahaifina a kansu? Sukan nuna abin bama dan yana d'ansa na farko bane, kiri kiri ya fi sonsa da su ne, sukan nuna hakan baya yi masu dadi sam, harma baban limamin masalacin masarautar ya taba yin zama da su da Sarkin garinsu watau yayansu, da mahaifansu ya yi masu nasiha mai ratsa jiki da zuciya, bayan sun bar wajen ya fuskanci iyayensu ni kuma ina zaune a saman cinyar mahaifiyar dan uwan mahaifina domin a duniya matar na shagwabani na nunan soyaya tamkar itace kakata ya yi masu nuni da tabas maganar y'ayansu gaskiya ce, a yanzu sun kai gabar tsufa ya dace tun sunna iya dajatar da abin su dakatar su kuma daidaita tsakanin, su boye soyayar yaronsu na farko a gaban sauran yayansu ko dan su sama masu zaman lafiya da jituwa a tsakaninsu, sai dai kashhhhhh , lamarin samun cenji bai samu ba, domin da tsufa ya sake kama su harma suka zamto tamkar yara ko abinci basa yarda su ci in ba shine ya basu da kansa ba, dama dama sukan yarda da uncle dina wanda suke uba daya da mahaifina wani sa'in, a haka rasuwarsu ta zo a jejere domin kuwa maman Uncle Ibrahim ta fara rasuwa, sai maman su mahaifina ta rasu, sai kuma mahaifinsu ya bi matansa............" Ya hadiyi yawu yana kallonsu ya ce" Daga nan girman da komai ya sake hawa kan Takawa, gashi mutun mai son mutane domin ba lokaci Takawa yana amsar baki, ba bambancin kai na kasarsa ne ko bako yakan karama kowa ne shi, haka Allah ya yoshi mutun mai son mutane,............" Ya fuskancesu ya ce" Mahaifina nada cutar zuciya, wace iya mu ne muka san da wannan rashin lafiya, rashin lafiyar dake hanna mahaifiyata nutsuwar zuciya domin shi ke dauke da cutarsa aman ita ke nisa rashin lafiyarsa, har abin yai mata ilar da babu maganar waiwaye sai dai hakuri da daukan danganaa na rashinta a ranar juma'a da sanyin safiya inda ciwonsa ya tashi sosai ita kuma ta yanke jiki ta fadi, daga wannan lokacin na fara maraicin uwa,............ Sannu a hankali na saba da rashin ganninta na kuma dauki dangana domin ko a lokacin shekaruna sun kai na nema na ciyar da kaina, dan dai na tashi a gida na sarauta ne ya zamto a boye nake , a kilace nake tamkar kwai, bale da kowa ya san cewa nine zan mulki kasata, harma an rigai an min sunna SULTAN tun ban kai ko'ina ba, hakan ya sa ake kakau da ni , balema dan uwan mahaifina Uncle Ibrahim wanda bawan Allahn ke koya min dukan wasu abubuwa da ya dace ace na iya na gidan sarauta ba tare da na fuskanci komai na tsana a tare da shi ba, shi kuma uncle Khamis damaa mutun ne mai matukar iza da sarauta a jikinsa, domin bana tunanin idan har sarkin dake saman sarautar kasata a yanzu ko da matansa yana hira bale y'ayansa harma a zo kaina, shi yasa ni dinma idan da halin mu zanta muke zantawa idan kuma ba halin hakan bana takurawa........" Ya dafe gaban goshinsa ya ce" Mahaifina ya rasu ne a sanadiyar tashin ciwonsa a daren litinin wayewar talata, wanda muka tashi da gawarsa a gabanmu ana ta yi masa shinfidar kabari........" Ya jimke hannunsa yana kallonsu ya ce" kamar yadda yake kaida haka aka bi da ni, ana dawowa daga suturar sarkina a cen cikin makabartar dake cikin gidanmu aka nadani a sarautar kasata da kannanun shekaruna ko auren fari ban yi ba, sannan aka saka ranar da za'a daura min aure da wace za'a binciko a ga ta dace da ni............." " Na rikice, na dimauce na rasa ina zan dosa na nuna tsantsar tashin hankalina a kan ranar da na wayi gari ake kirana sarki maimakun sarkin garina kuma mahaifina, wace zan je na yiwa kukan ta rigashi kaura, hakan ya sa na kwana cir a saman salaya ina kuka ina fadawa mai duniyar da kiyama cewar zabinsa nake so, karfin gwuiwa nake so daga gareshi,na sake dora kaina na yi kuka na fada masa cewar ba zan iya ba, bani da karfin hakan, aman idan hakan ne zanen rubutun ALK'ALAMIN KADARATAH ya bani ikon cinye jarabawar cikin sauki..............., Ni dai zan iya cewa daga wannan ranar sai samun kaina na yi a garin Manzo, shin ta yaya na zo? Ni na biya ko biya min aka yi?, Ni dai na samu kaina a garin da nake jin nutsuwa a jikina, ta yiwu rabon na hadu da gimbiyar da zan dora kaina a jikinta nai mata kuka ne? Ni dai zan iya cewa babu abinda ya fi daga min hankali irin maganar waye ni, ko kuma a kai ga maganar kasata, harma a san waye asalin ni din, sai kuma ta yarda, ta amince bayan ta fada min abinda ya cirota daga gidansu itama na ji kuma na amince da hakan sai mukai aure muke zaune da junna " Ya lumshe idannuwansa ya ci gaba da fadin" Shin wanene a cikinsu?, Me yasa ya min haka? Ina cen dinma a labe ya bini ya sake dawo da ni ya rufeni a dakin duhu ya ci gaba da azabtar da ni , ya rabani da y'ayana mata biyu masu kananun shekaru, ya kuma wulakantar min da iyalina .....ya kalleni a hali na hauka , ya ki ya kasheni da wuri wuri ya ci gaba da kallona, ko duk dan Allah ya yi da sauran shan ruwana a doron kasa ne?.............ni dai gani a zaune ina tunanin ina Uncle dina Ibrahim da yake gaba da uncle din Khamis ?, , Yaya aka yi uncle Khamis yake saman karagar mulki bayan Babu wanda ya ji mutuwar IBRAHIM?, shin me yake faruwa a Baban gidanmu?"...........ya idasa yana sake kallon su Dad da Muhay da kowa ya shige a hali na rashin dadin zuciya A sanyaye Dad ya ce" Ai uncle dinka IBRAHIM yana rufe a gidan mahaukata, zan iya cewa a kadan ya dauki shekara ashirin da bakwai a ciki, domin wayar gari aka yi yana hauka jajir, maganar da nake maka d'ansa daya kawai ke cikin gidan sarautar a yanzu , matansama sun yi wani aurensu sauran y'ayansa mata kuma du basa kasar sai dansa dayan nan , ai yanzu inaga shima ya tara iyali kam" Sultan ya dan girgiza kansa yana ta ambaton sunnan Allah, sai kuma ya dube shi da dan sauri ya ce" Ko dai Muhsin ne d'an nasa?" Da sauri Dad ya amsa shi cewar kwarai kuwaa Muhsin sunnansa Sultan ya fuskanci Tinana da ta yi mutuwar zaune ya ce" An maya, kina tune da wanda ya kawo mana sutura ya bude mana hanya cewa ya yi sunnansa Muhsin? Ko dai shine?" Tinana ta sauke gwauron numfashi tana sake kallonsa da mamakin wai dama mijinta sarki ne? Sarkinma mai daraja? Ta gyada kanta a sanyaye ta ce" Eh haka yace" MUHAY ya ce" Koma menene in sha Allah zai fito, a gobe da sasafe zamu juya da LIEUTENANT GANARAL MUJAHEED, option ta gaba da ya gabatar mana shine za'a dauki hoton ABA da rawani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188