Chapter 144
Chapter 144
da shi, malamin na daneka yana tofa maka abubuwan alkhairi yana so ya kwontar da iskokan, wani sa'in akan yi dace Allah ya yiwa abin tsawa, wani sa'in kuma dacen kan hadewa da ALK'ALAMIN kadararka wanda ya riga ya zanna tun kafin a haliceka cewa ta wannan dalili zaka dawo mahaukaci ko ka rasa rayuwarka, ko kuma ka ga baban tashin hankalin da baka taba tunanin akoyshi a cikin duniya ba......kadan daga aikin zafin zazabin nan, baban matsalarsa shine yawanci idan hankalinka ya dauke din nan dukkan wani abu na sirrin ratuwarka ke dagowa ya bayana da bakinka, alkhairi ne ko shari ne, ko menene da bakinka ne zaka fadi cewa ni da nake yin kaza da kaza? ......... Ku tambayi likitoci zasu baku bayani dala dala cewar tabas haka ne kuma hakan ke faruwa Da wannan lamari aka taki rashin sa'a ya fado a kanta, a daidai wannan gaba, a irin wannan babar rana da mijinta ya wayi gari ya sauke dukkan wani nauyi da yake ji ya masa girma a saman kansa, sai ga matsala ta rashin lafiya ta fado, ta kuma zo da karfi, cikin kudurar ubangiji irin wannan, Da karfi suka kakamata bayan an gyara mata hijabinta Allah ya taimaketa da masu rufe mata suturarta a kusa, suka samu suka daureta a jikin gadon da take kwonce, irin daurin da ba zata iya jima kanta rauni ko ta daki wanda ke gefenta ba, karfi ne tamkar na aljannu ke jan mutun, domin kana iya watsar da mutanen dake gefenka idan abin ya motsa, yana yi ne kuma yana kwociya "Walahi walahi sai na kashe MUHYIDEEN da hannuna, sai na kashe shi , yadda yaron nan da uwarsa suka shigo min rayuwar gidana da mijina ina mulkina son raina aman suka zo suka fi karfina ya zamto mijina ya samu yaron nan a matsayin dan da yake fatan samu namiji aman bai samu ba, shine komai nawa da na y'ayana ya dawo hannunsa harta da shawarar abinda ya shafemu sai ya nema a wajensa uwarsa ta ciri ta kullu tabi bokaye ta shanye mini mijina sai yarda ta yi da shi ita karuwar algunguma mai........" Da sauri ta karasa wajen ya dora hannunsa na hagu a saman bakinta ya damke da mugun karfin da ya sa ta hade da fatar tafin hannun nasa ta gala wani wawan cizon da ya ratsa dukan gaban jikinsa dan azabar zafi harma ya fara ji zufa na neman karyo masa, aman ya danne ya sake dora dayan ya danne bakin nata sosai yana rintse idannuwansa wani irin tsoron Allah na shiga dukkan sasan jikinsa da tsoron haduwa da shi a gobe kiyama da wani laifin, sannan ya sake yarda cewa ko me bawa yake yi a duniya dama Allah ke ara masa , kalilan ke samun dama irin wannan wace zasu bayana kafin su koma ga mahalicinsu, in ka yafe masu to, in baka yafe bama to, dama damarsu basu je a makance ba, watau sunna aikata aikinsu a boye da mugun nufinsu a zukatansu ba Kallon da Dad ke yi masa, da Mahaifiyarsa ke yi masa, da kuma matar mahaifinsa ke yi masa, a gangaro kan sarakuwarsa dake tare da su, da sirikinsa dake gefe yana tofa mata adu'a a bayan an sake suturtata da hijabinta ya shigo shima yana tofa mata adu'a da nema mata sauki a wajen Allah, gaba daya suka zuba masa ido kowane da yannayi na firgicin furucin bakinta da kuma irin yadda ya damke bakin ya rike kam ya kuma hannata karasa furucinta, aman kuma a yadda take kokowar sai ua saketa zaka tabata da zarar ya saki bakin nan komai na iya faruwa ya saka shi sake gyara tsayuwarsa yana sake damkar bakin nata da hannunsa yana rintse idannuwansa ya ce" Kun san zafin ciwon nan babu abinda baya hadasawa, ciki harda dumumuwa kamar yadda likita ya sheda mana yanzu, dan haka nake so dan Allah ku fita ku dukanku waje har ta samu lafiya" Dad kallonsa yake yi jikinsa na neman fara bari Muryarsa na rawa ya ce" Mu fita waje ko ka saki bakinta?, MUHYIDEEN MUHAY, sake min bakinta now!" MUHYIDEEN ya sada kansa yana girgiza kansa a sanyaye ya ce" Ka yi hakuri Dad, ba zan iya sakin bakinta ba" Mahaifiyarsa da ta yi baya baya a hankali ta rike garun dakin ta sake zuba masa ido, sannan ta zubawa matar nan dake kwonce ido, kafin ta lumshe idannuwanta hawayen da take ta sharewa na tausayinta tun dazun wasu suka sake zubo mata masu daci sosai sai kuma ta rike hannun Tinana da ta sake rike hannunta a hankali ta shiga bin bayanta suka fice a dakin kwata kwata suka fice a wajen har suka hade da y'ayanta mata da suka yi zuru zuru an hanna su shiga wajen , Suka wuce su ba tare da sun iya kula tambayoyinsu a kan jikin mahaifiyarsu ba, ya rage sauran mace daya da kuma su Dad, wace itama ta sauke ajiyar zuciya ta girgiza kanta ta juya ta wuce a dakin tana tunanin tabas son zuciya da rashin godiyar Allah sun kai matar nan sun barota , hakan ya rage daga Dad sai Sultan, sai Muhyideen da ya ki sakin bakin nata Da karfi Dad ya shamace shi ya warce hannunsa a saman bakinta, kamar jira take ta dora da fadin" Ke kuma Salma yadda na haife ki da cikina aman kike juya min baya a kan kudirina da shirina na son kashe dan iskan yaron nan ba damuwa, ai gari da yawa maye ba zai ci kansa ba, da kudina a jakata na tabata zan janyo da yawa da zasu kama min, sai na ga an fita da gawarsa a makara a wulakance zan samu nutsuwar zuciyata, mijina na ni kadai ne sai ko y'ayana, du wanda ya ratso duniyata da mijina sai ya shiga uku wannan alkawarina ne!, Sannan da mijinki ke maganar karra aure ki sani ba zan taba bari a maki kishiya ba, yar iska mai zuciyar mahaukata da baki san ciwon kanki ba bale na uwarki! Ana wulakantani kina nanuke da su ke ga ta kirki ko? In dai mutun ne mugun ice ne,, su ji suke tamkar ki mutu su karra yawon kudin gadon ubanki a kanki............., Ita kuma uwar Uma itama sai na................" Bakin ya sake damkewa bayan ya bi Father da kallon tausayi yana girgiza kansa ya waiga gannin Aban Shuwwa na kokarin barin dakin a birkice ya ce" Sultan " Wani irin birki mahaifin Shuwwa ya ja ya juyo da sauri yana kallon bayan MUHYIDEEN MUHYIDEEN ya sake tausasa kalamansa ya furta" Aikinka ne hanna yaduwar fitina ko wace iri ce Abah, ka taimaka ka shiga a matsayin da Allah ya nadaka a kai ba wani dan adam ba, kana da ruwa da tsaki a ciki a matsayinka da Allah ne ya baka, ka dube mu ka kama Abahna, ka kwatanta masa cewar wannan din ba komai bane ba, karma ya daga hankalinsa a irin wannan, Allah ne ya kadara masa haka , wannan al'amari a rubuce yake tun kafin a halicemu, Dan Allah kar ya rikita lafiyarsa ko ya saka a ransa ta yadda zan rasa wani uban a karro na biyu, ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188