Chapter 109
Chapter 109
na fita da sanyi kamar ba danta ba, abinda yake damunsa mai karfi ne gaskiya, koma menene tana fatan Allah ya sa ba wanda zai hargitsa farin cikin marayun nan bane, domin wannan karron ba zata iya barinsa ya saki yarinyar nan ba ko kadan Gannin waje ya nufa ya sakata dan dakatawa har suka fito kowace tana tafia ne a hankali suka karaso kafin su jeru su fita a falon gaba daya A irin wannan lokacin kasancewar rana ta fara yin zafi duba da gari ne mai zafin rana ya saka daidaiku ke karkashin ranar nan, sai masu gadin gidan, yawancin mutanen gidan kowace na bangarenta tana hutawa, bama kamar matarsa da rabonta da lekowa tun jiya gaba daya ta tsangwami kanta da nutsuwarta, a tsoracema take da shi sosai, hakan ya sa ta labe a ciki Gannin ya mike da tafiyarsa ya saka Mama dan daga kafa tana fadin" MUHAY ina zaka je ne haka da mu?" Dan juyowa ya yi , hakan ya sa ta fuskanci ai waya ce a kunnensa amsa kira yake yi, Gabanta ne itama ya fara faduwa tana biye da shi ne kawai, har tunani ta fara yi ko wani abu ne ya samu mai gidan nasu? A hankali Nahidt ta riko hannun Shuwwa tana kallonta, muryarta a raunane ta ce" Shuwwa, kar mu je, dan Allah kar mu je ya sake ki, kin ga mun fara samun soyaya irin ta uwa, mun fara jin dadin uwar da bata haife mu ba aman kuma ta san cewa d'a na kowa ne, kar mu bishi ya sake ki ya katse mana wannan gatan, Shuwwa da ta zare min ido kan sai na koma saman PO din nan kuka na yi, ba na komai ba sai na tuna Mamanmu....." SHUWWA ta lumshe idannuwanta a sanyaye itama ta ce" Kin ga, abinda ya yi niya zuwanmu ko dakatawarmu ba su zasu hanna shi yi ba, kin san ai yana da gardama sosai, bana tunanin mun isa mu saka shi ko mu hanna shi wani abin, Allah ya zaba mana abinda ya fi zama alkhairi zo mu je kin ga sun bude bayan motar chan" Kafin suke karasawa suka ga Mama ta juyo a firgi ce tana kallonsu, kafin ta daga masu hannu tana fadin" Kar ku karaso ku tsaya daga cen......" Gaba dayansu suka ja suka tsaya gabansu na ta faduwa Mama da jikinta ya dauki rawa ta kalle shi tana fadin" Ka karra ganar da ni abinda nake ganni a kamanin matar nan da yayar matarka MUHAY" Gwauron numfashi ya sauke ya ce" Kadeta na yi, ................" A sanyaye du ya fada mata abubuwan da suka faru har zuwa yanzu, hakan ya sa a wani firgicen ta sake kallon Matar dake hangensu aman bata jin tataunawar da suke yi, gaba daya kuma ta sake tsurewa da tunanin har an shigo da su wajen da za'a sake salwantar da rayuwarsu kennan Ta so ta nuna masa idan y'ayan suka ga mutumen nan kuma ya kasance mahaifinsu ne a haka a lalacen nan hankalinsu ne zai tashi sosai Sai dai kuma ta tabata uwar ba zata yarda a rabata da mijinta ba da wani kwakwaran dalili ba, sannan a yanzu ba zata so ci gaba da ganninsu sunai mata kallo irin na marayun nan da zarar ta kyautata masu ba, haka kawai take jin kaunarsu a cen kasan zuciyarta da son kyautata masu, dan haka ta sake fuskantarsa ta ce" Da ka fadawa Abanku mai yace?" Hannayensa ya dan watsa ya ce" Yana cikin taro ne, na dan so kwatanta masa na ga zan yi ta magana ne ba zai fuskanci inda bayanina ya dosa ba" Kai take gyadawa ta nufi motar ta sake bude bayan Matar ta dan takure jikinta tana kallonta hakan ya sa Mama fashewa da kukan tausayi tana kallonta A sanyaye da yaren buzanci ta ce" Su waye suka wulakantaku haka har suka saka muku tsoron mutun dan uwanku mai numfashi? Kin ga yaya sunnanki dan Allah? Kama hannayena ki zo ki ga wani abu, taho ki gani kin ji?" Duda yaren haihuwarta Mama ke yi, sannan kalaman na mama kalamai ne masu saka Nutsuwa da yarda a zuciyar mutun, aman gaba daya sai Manma ta kasance kamar kurma a gabanta sannan ta kasa barin jikin mijinta du sai takura masa take yi bata sani ba Sosai tausayinta ya karra kama Mama, ta juya wajen MUHAY zata fada masa cewar ta ki yarda ta fito sai ta ga ya juya wajen da suke da hannayensa ya yafito su Sai da suka kalli junna kafin suka nufo shi kowace jikinta a mace sosai da kuma tsoron abinda yake faruwa Sunna zuwa wajensa ya saka hannunsa ya kamo na Shuwwa hakan ya sa ta dago tana kallon fuskarsaa hadi da jin faduwar gabanta na tsananta A hankali ya ce" Yaya sunnan mahaifiyarki?" Shuwwa ta karewa lebunnansa kallo da ya dire maganar , hakan ya sa idannuwanta suka farra rawa Nahidt dake kallonsu ce ta kai hannayenta wajen kirjinta tana rungumewa a hankali ta ce" Tsoro nake ji, jikina bari yake yi, Shuwwa tsoro nake ji, wayo Allahna me yake shirin faruwa? Yalabai me kake so da sunnan mahaifiyarmu? Sunnanta TINANA, haka sunnanta yake Shuwwa me yake faruwa ne ?" Tunda ta fara magana matar ta juyo da karfi tana kallonsu ta madubin motar, kasancewar mai duhun gilas ne sai dai ka ga wanda yake waje ba dai shi ya ganka ba Kalaman dake fitowa daga bakinta suka saka matar sake kura mata ido har sai da idannuwanta suka fara zafi A yanzun da kanta ta miko kafafuwanta ta nufo fitowa jikinta na rawa har ta bayana gaba dayanta a waje kafin ta zubawa yan matan ido gaba dayansu Wajen da ya zubawa ido suka juyo dan gannin me yake kallo ne kuma? Kallon yan matan take yi itama da wani kallo mai nuni da kamar tama a tsorace da ganninsu a haka ne ko kumaa bata yarda cewa wadinnan din y'ayanta ne da ta haifa a duniya ba duba da ta baro su a cen karshen duniya yaya aka yi suka samu zuwa nan? Kai kwata kwatama ta yaya suka samu kasancewa a nan kai tsaye haka? Haka summa suke masu binta da kallon da ya dakatar da bugawar zuciyoyinsu, ballema Nahidt da wayonta a lokacin ya fi karfin wasa ko yaya mahaifiyarta ta zama ba zata bace mata ba, zuwa Shuwwa din da karfin jinnin haihuwa da kamanin suke ta dawo mata suka sakata daskarewa tana kallon matar da a jikin mahaifiyarsu kamar an raba hudu ne an bata daya, haka farin fatarta ya yi duhu , sannan fatar tata du taa bushe ba kamar matar da sukaa sanni yar gatan mahaifinsu mai kyau da tsari, mace mai lafiya da fara'a ba A hankali SHUWWA ta ringa lalube a cikin duhu, domin so take sai ta riko hannu a cikin hannunta, aman ta kasa riko hakan har dai Maman MuHay ta fahimci haka ta karasa da sauri kusa da ita ta riko mata hannun tana kallonta hakan ya sa ta juyo, sai dai gannin ba Nahidt din bace sai ta saki hannun da sauri ta kuma damko na Nahidt din tana kallonta a dan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188