Chapter 151
Chapter 151
Sun yabawa tsaftar girkinta domin sun yi karantun girkin ne su aman kuma sun yabawa nata girkin, harma suka bada hankalinsu dan kara daukaka iliminsu a fannin girki. Tana tsaka da kallon Film din da ake nunowa a tashar larabawa ya bude kofar a hankali ya shigo da salama a bakinsa ya ja ya tsaya yana karewa falon kallo da kuma wace ke kwonce saman doguwar kujeraALK'ALAMIN KADARATAH Na *Sajida* Page 6️⃣3️⃣ Tana tsaka da kallon Film din da ake haskowa a tashar larabawa ya bude kofar falon da salama a saman lebensa a hankali, sanann ya sanyo kafafuwansa sosai yana maida kofar ya rufe ya tsaya yana bin falon da kallo har ya sauke duban nasa a samab wace ke kwonce saman doguwar kujera sanye da farar riga irin doguwar nan mai siririn hannu , aman rigar ta tatare ta yi sama kusa da cinyarta wace hakan ya sa cinyoyinta suke waje da farar safar dake kafarta fara fesss tana dan balancing din kaffafuwan nata A hankali ya hauda duban nasa har saman fuskarta, nan sukai ido hudun da ya saka shi kwacewar ajiyar zuciya yana sake tunanin to ba zata mike ta masa sannu bane dai da sauransu dai haka? Ita kuma ta cire dara daran idannuwanta ta dan mike a kwoncen da take ta maida dubanta saman TV din tana yi kamar bata gane ko wanene ba, domin tsakani da Allah tafiyarsa ba labari ya mata ciwo a zuciyarta sosai, ba kuma taso a kuma aikata irin haka Sake kallonta ya yi da kyau, kafin ya tabe baki ya sake bin dakunnan dake jere a falon da kallo yana tino maganar da mamansa ta fada a kanta cewa bata yarda ba koda wasa ya saki yarinyar nan ko ya yi mata abinda zai raunata farin cikinta da gangan, ta cire lamari na zaman tare aman bayan wannan kawai karma ya wani muzgunna mata aka ce Dan jan hanci ya yi ya idasa shiga yana muzurai ya nufi dakin da yake tunanin nan ne ya dace ace nasa ne, domin idan bai manta yannayin ginnin nan ba dakin na biyu ne ya dace ya zamto dakinsa, tunda dai ai gidansa ne kuma baban dakin ne ya dace na mai gida kau? Da kallo ta raka shi gannin ya bude mata daki ya shiga, ta sake tabe baki ta kuma gyara zamanta bata bi bayanshi ba bale ta tambayeshi me zai yi a dakinta ne?, Gaba daya tana so ta ga ciwon bakinsa har ina ya kai ne? Yan mintunna tsakani ya fito daure da tawul ya karaso wajen da take zaune a hade ya ce" ina kayana suke?" Dagowa ta yi dan ta kalle shi, sai dai da sauri ta cire kanta gefe tana jin kamar zata kurma ihun tsoron yadda tawul din ya masa, gaskiya soja bashi da kunya, shi sam baya iya suturta jikinsa nsa a gaban yara kanana? A dan daburce ta ce" Wasu kaya kuma?" Ya sake dubanta da dan haushi haushi ya ce" Na shiga bayina na tarar da bruch da maclean pink, da tawul pink pink a ciki, sannan tawul din nan yaya za'ai ya min ya min kadan!, Ina aka saka min kayana ne ni? An ce an kawo min komai?" Da mamaki ta kalli daga dakin da ya fito , hakan ya sa ta ce" dama akoy hanyar dake sada wani dakin da wani ne?" Kin bata amsa ya yi yana yi mata kallon da zata iya fasarashi da harare, hakan ya sa ta mike tana fadin" Mu je dai in gani " Gaba ta yi ya bi bayanta , haka kawai idannuwansa suka sauka a bayanta dake juyi kamar wace ke yin hakan da gaya, yana biye da itan idannuwansa kyam a saman bayanta har ya zo gam ya hade da garu ba tare da ya san ya karaso wajen ba kuma a daidai garun yake tafia ba Kasancewar abin ya zo masa a ba zata dole ya yi saurin dora hannunsa a goshinsa yana furta" aushhhhhh" Turus ta yi ta juyo da sauri dan gannin abinda ya saka shi yin Aushhh, sai dai tana juyowa ya yi gagawar ajiye hannunsa yana matse fuska irin ga jarumin nan, hakan ya sa ta bi kirjinsa da kallo da hannunsa har ta sauke dubanta a kan hannunsa na dama da ya jimke, wanda ke nuna alamun ya daku fa Bakinta ta dan tabe kadan da dan baya baya ta fara idasa shigewa dakin , sai dai me itama tana shiga ta harde da dogon wandon da ya cire ya yar a nan kan kofar dakinta hakan ya sa sai da ta yi tangal tangal kafin ta diba duwawu a kasa Dan kara ta saki tana dafe kugu hadi da kallon abinda ya yarda ita Da wani takaici ta dago dubanta ta sauke a kansa domin sai ta kula kamar wanda yake murmushi a saman lebensa, sai dai sunna yin ido hudun sai ya sauke idannuwansa kasa wajen wandon yana kallon wandon hadi da dan cicije lebensa na kasan Da takaici ta bi dakin da kallo, ai kam ta ga gajeran a yashe a nan kusa da gadonta, gadon da ta yiwa gyara na kasa da kasa, tunda ta gyara shi fa tana son shiga ta kwonta aman idan ta tuna shinfidar da ta malala masa sai ta ji cewar gaskiya tsaftar jikinta ba zata hau gadon ba, watau gadon ya sakata maka masa shinfidar yan gayu irin ta sarakai , shinfidar da ta rantse da ubangijin talikai ta dauki kusan minti ashirin tana yinta, shine ya tako ya cire mata dan kampai ya yar mata a gaban gadonta sannan ya cire safar kafafuwansa da ya tako datin kasar da ya fito da na anguwanni ya dora mata a saman shinfidarta ita?, Uwa uba abinda ya fi kona mata zuciya ashe takalmin dake kafarsa da shi ya shigo mata daki? Oh no wannan daya, ba zata dauki wannan ba gaskiya Hakan ya sa ta dago yar yatsarta ta yi kalar balbalin balaki sannan ta shiga fadin" Saurara malan saurara, ba zai yiwu ba gaskiya, a gidan nan za'a zo ne a dauki byro da takarda a ware abinda ake iya yi na yi hakuri da wanda idan aka yi lalle lalle za'a iya tono abin bacin raina, ka ga yarda gajeran wando a ko'ina ba tsafta bane, kazanta ce tukuru mai lasisin tsiya, idan ka cire yabadaibadai dinka kaimin bayi ajiye min idan na shiga zan wanke na shanya, bale ka ga ba zan dauki a cikin gidana a ringa shigo min da takalmi ba, lallalalalalaalalalalala, sannan a dakina a zo min a ari tawul dina kuma a karashe da ajiye min safa a saman bed? Shinfidar nan ai kana gani ka san na wahala wajen yinta, to shi musulmin kirki ba an ce ya sowa dan uwansa abinda yake sowa kansa ba?, Wannan lamari sam ban ji dadinsa ba, kar a kuma ina dalili ina dan mafari ne........?" Ta karashe tana sake kallo fuskarsa, domin tunda ta fara magangannun nununawa ne take yi tana jujuyawa ta yadda zata masa gwari gwari ya gane da kyau ya kuma kiyaye, sai da ta ajiye maganar tata ne sukai ido hudu, ido hudun da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188