Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 97

Chapter 97

Alkalamin Kaddarata Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kazar da bata jin as" Tsayawa tayi tare da dawowa baya ta shiga kallonta a kausashe tace "Bana jin ni da ke muna da bambamci indai a wajen MUHAY ne, dan ga dukan alama ke ma iskan wahalar dake yake sakamakon dakon kayan karmami da kike yi" A hassale kamar mai jiran tab'i tace "K'arya kike wallahi, dan ko ba komai ni ina amsa sunan matarsa, ke fa ? A cikin gida kike ke ba karuwa ba kuma ba cikakkiyar mace ba mai daraja ba, ke kulun kina jira ki ga motsinsa" Cike da neman fitina da rashin wayo Umma tace "Sai dai in uwarki ce karuwar amma ba ni ba, jaka kawai, ita matar so d'in ai gashi ya taho da ita har nan, ke fa ballagaza kina zaune ki.." A tsiyace ta dafe k'irji tace "Ni? Uwata kike fad'ama karuwa?" Ta katse maganar Ummar Cike da rashin aji da d'aukaka martabarsu ta 'ya'ya mata sai kuwa suka had'e jikinsu da sunnan dambe wanda sam ba tsari a hakan face zubar da mutumci, musamman ma a wajen uwar gidan Muhay wacce da ta san darajarta da kimarta ba za ta yi fad'a da wacce ma ta amsa sunan matarsa bare kuma wannan. Uwar gidan Father ce ta fara fitowa tana neman rabasu da kwaroroton zancen tana daukaka maganar har maman su Ummi itama ta fito wace ta kwana bata rintsa ba itama da nata kalar bacin ran ta ce "Kai! Kai me kuke yi hakane? Ku saki junanku." Ba wacce ta san tana yi in banda dambatuwa da suke, sake bud'e murya tayi tana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Na shiga uku na lalace, wannan wace irin masifa ce ? Ku kenan kullum a haka akan namiji...wai za ku bari ko sai na had'aku da Chief?" Duba da babu wacce ta kula da ita yasa ta kada daya daga cikin sojawan dake bada tsaro kan maza ya kira mata CHIEF duda ta sani sarai dokar gidan ba'a aikensu ko nan da nan Maman Ummi na gannin haka ta hanna ta nufi almajirinsu mai yiwa yaren dan aika wanda sunne suka dauke shi yana ta faman share wajen flowers d'in nan ta turashi ya kira Father. Father na k'arasowa a tsawace yace" Kai meye wannan kuma!" Umma ce ta fara kiciniyar raba jikinta da ita tare da dafe kunnenta daya had'e da rigarta, a hankali suka raba jikinsu sai huci suke uwa wasu zakuna suna ta k'ok'arin gyara kayan jikinsu duk sun cimimiye. Matsawa Father yayi saida ya je gaban Umma ya d'aga hannunshi ya wanke fuskarta da mari, razananniyar ihu ta saki tana d'agowa ya kuma zuba mata wani marin, cikin tsananin b'acin rai da takaici ya juya ga sojawan dake tsatsaye suna kallon ikon Allah, tun farko sun so raba fad'a to amma duk mata ne ba zasu iya kama jikinsu ba, bare fad'an mata da kan k'asa ake kai nushi sai a samu d'an rabo ba gaira ba dalili ga cizo da yakushi, nuna musu Umma yayi a hassale yace "Kai ku d'auke ta ku kai min guardroom d'in nan, sai na tabbatar tayi hankali koda zata fito." Ya k'arashe da kallonta yana zabga mata harara yace "Yar iska kawai." Uwar gidansa da abun bai zo mata yanda ta so ba rufe baki tayi jin ya b'aro wannan zagin, dan a saninta da shi ba ma'abocin haka bane, ga kuma wani tashin hankali wai a kai Umma guardroom, to a kan me? Umma kam fashewa tayi da kuka uwa jiniya ta durk'ushe tana fad'in "Dad ka yi hak'uri dan Allah ba zan sake ba, wallahi ba laifina bane." A harzuke Father ya nufi part d'in shi ba tare daya kula kowa ba dan idonshi a rufe suke da b'acin rai, ita kanta ba dan yana kallonta a matsayin sarakuwa ba, da sai ya falla mata marin dan ta gane ba'a masa haka. Shuwwar da Nahidt da ke tsaye kusa da juna wannan hargagin ne na uwar gidan Father ya fito da su dan ko baccin su basu gama ba, dan Shuwwar ma kayanta na jiya ne da ta cire doguwar rigar da ta kwana da ita ta saka su domin sun bushe yanzun watau farin dogon wando da farar riga mai dogayen hannu kanta ko d'an kwali babu sai ribom d'inta daya kusa fita a kan ta. Mama ma na gefe tsaye da carbinta a hannu dan tana kan sallaya ta ji wannan tashin hankalin ta fito, kallonsu take ranta na k'ara b'acewa da tunanin me yasa suke aikata haka? Me yasa suka kasa zama mata ne? Me ye anfanin banzatar da mutumci da kimarsu akan wanda ko damuwa ta ainihi baya nunawa a kan muradinsu ? Ribar me za su samu yanzu bayan k'ara tusa masa tsanarsu da d'abi'unsu, dan a yanda ta san d'anta ba mai hayaniya ba abinda sukayi yanzun zai sa ya musu kallon hadarin kaji ne sannan ya ba banza ajiyarsu Ai kam dai abinda Mama ke rayawa ne ke faruwa, dan tunda suka shigo tare da Father idonshi ya sauka a kansu da k'alak'antan da suke da maganganun da suke fad'a, sai ya fara jiyo k'amshin dalilin fad'an kam shi ne, sam a zuciyarsa ya ji hakan bai dameshi ba, sai dai abu d'aya da zai iya cewa bai ji dad'i ba a matsayinsa na namiji mai kishi shi ne, yanda matarsa ta aure ke dakuwa da wacce zai iya cewa k'anwarsa a gaban wasu k'arti masu kaki, sai yake hango da fa wata ta cirewa wata kayanta? Idan fa sun yaga tufafin junansu? Bayan ba shirin fad'an sukayi ba, shikenan asirinsa ya tonu kenan, duk da bai da tabbacin gaurayarsu amma dai ai tana amsa sunan *mallakinsa*. Tun wuri ya gaggauta d'auke idonsa a kansu, sai dai me? Idan har ya fahimci rayuwa daidai zai iya cewa duk tashin hankalin da ya sameka a bazata, sannan ya zo maka a baibai ya fi d'aga maka hankali fiye da komai, dan kuwa wacce aurenta ya zo masa a bagatatan, sai gashi ita ce ta fi tsone masa ido a tsayuwar da ta yi da kuma tufafin jikinta. Lokaci d'aya ya samu kansa da rarraba ido kamar marar gaskiya, yatsina fuska yayi ya sake kallonta amma ko a jikinta, to dama ta ya zai dameta bayan da gangan ta fito? Amma dai ko ya ya ta tayasa kare martabarsa mana, yanzu idan sun gama k'are mata kallo fa? Kenan shi ya tashi a sakarai d'an a bi yarima a sha kid'a? Guardroom d'in da Dad ya ambata ne ya dawo da shi daga duniyar b'acin ran da ya tafi na tunani, ganin Dad d'in ya nufi b'angarensa ya sa ya ma d'aya daga cukin sojojin da yake tunkaro Umma dan son cika umarnin Chief d'in alamar ya tafi ya barta, Da kai ya amsa masa shi ma alamar "Ok sir." Ratsawa ya yi tsakanin Umma dake durk'ushe da uwar gidansa dake tsaye tana ta gyara rigar shaddarta wacce ita a shirin had'uwarsu ne tayi da sanyin safiyar nan. Ta tsakiyarsu ya bi ya wuce fuskarshi a mugun d'aure ba tare da ya ko had'a ido da ita ba Baki bud'e ta bi k'eyarshi da kallo sanda ya isa kusa da Shuwwa

Table of Contents

Chapters

188 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});