Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 68

Chapter 68

Alkalamin Kaddarata Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kanshin turaran ruwan da ta zubawa wandunnan ya daki hannayensa hakan ya saka shi lumshe idannuwansa a hankali sanan ya sake budewa ya zubawa hanyar da ta fita ido yana sauke ajiyar zuciya kafin ya tabe bakinsa ya dan karra kwontawa dan yau sai karfe tara zai bar gidan. ______________ "NAHIDT" ta fada da dan karfi tana zarro ido sannan ta shiga saukowa da gudu gudu ta nufo NAHIDTH da ta mike tsaye itama tana kallonta. Hannaye suka budewa junna tamkar wa'inda suka shekara basu ga junna ba sunna kyakyata daria suka rungume junnansu Da muryar dariya da kuka kuka da ihu ihun farin ciki ta ce" Nahidht, i miss you, i miss u so much, sai ina ji kamar zan yi hauka idan na waiga ban ji ihunki ba, kin ga saura kiris ya sakeni na dawo abina, ina missing din muryarki" Nahidt ta dagota daga jikinta tana kallonta ta ce " Ke tsaya dan ubanki Ya sako ki?" SHUWWAR ta dan kifta ido tana kallonta ta ce" No ba haka nake nufi ba." Nahidt ta kama hannunta ta jata sai saman lumtsumemiyar kujerar dake girke suka lume abinsu tana kallonta ta ce" Farka dan ubanki, na ce farka!, Idan ya sakekima babu inda zamu tafi! Ke ashe baki da hankali? Har yanzu kina kan bakanki na ya sake ki? Shi yasa kike zaune da zani a saman rigar barci da safiyar Allah? Ina matsatsu firgitatun kayanki ne? Ko na barcin wannan ai ya yi sutura, Shuwwa kar ki ce min bakya kwana a dakinsa tunda kika zo?" SHUWWAR ta zuba mata ido bata ce komai ba a kasan zuciyarta tana ayana' Du tunani take wannnan mutumen wani mutun ne mai sauki kai ko? Ko du ji take kowani namiji da zarar ka saka matsatsu ka yi tafiya a gabansa zaka dauki hankalinsa ne?, Bata san cewa wannan mai kama da aljannun ya fita taurin kai bane, bama wannan ba bata san cewa baya cikin burikanta ne?' "Kina nufin har yanzu baku yi....." Nahidt ta fada tana kallonta da zarro ido. SHUWWAR ta dafe hab'arta tana fadin" kin ga matsalata da ke fa kenan, kin gani fa ko?" Nahidt ta taba hannu tana fadin" Ko bashi da lafiya? Ko kece yar iskar? Shuwwa mijinki ne fa? Kwana har biyu daga ke sai shi a cikin gida ko shedan din bai samu galaba a kanku ba hala? Innalilahi na shiga uku na lalace Shuwwa du uban kudin da na kashe na dudura maki magungunna har yanzu bai fara kaikaitawa ba? Ke ina safarki? Ban hannaki zama ba safa ba?, Wayo duniya Shuwwa kina kallon kato yana shiga yana fita koda baya so ki masa dole mana?" Wannan Karro SHUWWAR sai kawai ta zuba mata ido ta gaza ce mata komai sai da ta dasa aya ta ce" Wai me ya kawo ki ne?" Nahidt ta dan kalleta, ta dan yi tsam sai kuma ta gyara zamanta tana murmushi ta ce" Na k'auro fa, ai mun ma yi magana da shi kin ga ya sa an saukeni baki ga yadda aka amshi kayana aka min maraba aka ce ga dakina da komai da komai, Shuwwa kin samu duniya Allah baki k'iyama." Shuwwar ta zaro ido tana kallonta ta ce" Kin k'auro ina?, Ni da nake shirin tafiya sai ki k'auro? Waye ya sauke kin ? Ba dai wancen dunkum d'in ba kau? Nahidt tsakani da Allah me yake yawo a kwakwalwarki ke kin san ai ba zama zan yi da mutumen nan ba, na san kin gane da ba zama zan yi da shi ba, shine zaki kauro kema?, Innalilahi wa inna ilaihi raj'une Nahidht ina yayan namu yake yo? Gaskiya sai dai mu koma wajensa tare, waima me yasa baki zauna a wajen yayan namu bane?" Nahidt ta zaro idanuwanta da fada fada ta ce" Ke da barin gidan kun ci uwaku! Na ce kun ci uwaku!, Kuma da kike cewa wai ina yayanmu yana nan baima san na kauro ba, ni ba zan iya zama a gidansu ba sai kumbiya kumbiyar munafurci suke yana sando baya so a ga zai je dakin Fauziya, itama wai ni take jin kunya dan wani tsohon munafurci, ke ni gidansuma ba hayaniya walahi ni kuma na saba ana haya haya ko yayane kau? Shuwwa wai ko dai korata kike ne? Kudi kika yi kike korata ne?" SHUWWAR ta rafka tagumi da hannayenta bibbiyu tana kallon yayar tata, wai irin abin nan take yi na daukaka karamin abu dan ta sakata a uku, wai da wani yare NAHIDT take so ta kwatanta mata dala dala waye MUHAY ne?, Da yaya take so ta kwatanta mata shi din ba kalar maza yan soyaya bane? MUHAY bai yi kama da wanda zai iya tatalin mace ko ya nuna mata yana sonta ba, domin shi matan suke yiwa haka ta yaya shi zai fara yiwa wata? Shikenan ita sai ta zama banza a banza kenan? Ta zauna da k'aton sai dai ita ta ringa rarashinsa shi ba zai rarasheta ba? Ai ba haka bane rayuwa gaba daya ba haka bane ba, ita burinta ta samu namijin da zai kasance mai yawan maimaita mata kalmar so, wanda zai ringa fada mata ba dare ba rana cewar itace so dinsa, wanda zai zama tamkar redio idan tana gefensa, aman wanna mutumen idan ya budi baki dan ya mata masifa ne, a kwana biyun nan da ta yi da shi zata iya cewa kyautata masa b'ata masa rai yake! A hankali Nahidt ta ce" Da kin san abinda ya koro ni gidan nan da sasafe da baki nemi na koma ba, dan na san ranki sai ya baci Shuwwa." Shuwwar ta cire taguminta tana kallonta ta ce" Wani abu aka yi maki?" Nahidt ta sauke ajiyar zuciya tana aron jarumta zata fara magana wayarta ta shiga kuka. Kin dubawa ta yi domin a tunaninta yayansu ne ko Fauziya, bata san cewa Malan bane, da ta dauka ta gindaya masa sharudan da ta gama zanawa ranta sannan ta fada masa ya ji kunya wollah, ta danne wayar ta hade hannayenta ta ce" Abanki, Shuwwa Abanki ne ya ba matarsa waya ta zageni ta ce min karuwa?" Gaban SHUWWAR ne ya fadi tana kallonta ta ce" Aunty, kalle ni, kalle ni, dan Allah ki fada min gaskiya kin ji? Aban nawa?" Nahidt ta taba hannu tana fadin" To karya zan maki ne?, Na rantse da Allah tsakiyar dare muna maganarki da shi jiya kawai ya tashi ya kai mata wayar dakinta ta aniya duran ashar harda mamanmu da abanmu ta zaga, ta kuma ce min karuwa wai ina kiran mijinta tsakiyar dare!" Zuciyarta ce ta fara tafasa a zaunen da take tana kallon auntynta ta dan wara zamanta tana kallonta ta ce" Nahidht, dan Allah ki rufa min asiri ki fada min yadda abin ya kasance kin ji? Kar ki saka na aikata abin kunya, domin idan matar nan ta taba ni ta kwana lafiya banda ke, bana tunanin zan iya kyaleta a yau Nahidt, me ya hadda ku waya da Abahna? Kin tabata shi ya kai mata waya? Abana ba zai aikata haka ba Nahidt, ki fadan yadda abun ya kasance." D'auke hannunta ta yi daga na ta hannun da mamaki

Table of Contents

Chapters

188 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});