Chapter 98
Chapter 98
zatonta ba zata waye ba, irin yanda jikinta ya tsananta zafi, a tunaninta za'a fasa, sai dai tana ji tana gani aka ci gaba da dura mata abubuwan dake kara saka mata kasala , tana ganni Abihnta ya ringa murnar gannin yanda fatarta ta dawo da irin yanda ake kula da ita, tana gannin yanda yayunta ke wani irin farin ciki harta da Nusaiba an yanyara mata kitso kannanu an shiryata cikin yar rigarta ta barbi mai kyau Tana kallon yanda yayanta ke amsa waya hakoransa waje yana ta fara'a yana shaida yana gaiyatar daurin aure gobe a fada zai aurar da kanwarsa Daga nan ta kara sarewa lamarin sai kawai ta aro shiru ta yafawa kanta, tsakaninta da kowa ido ne bata cewa um bare um....um Irin yanda take fitar da kamshi ko fitsari ta yi baki daya kamshin turaran ke fita a jikinta, irin yanda suka mayar da fatarta ita kanta takan ji a yanzu take mace mai classs Irin lesson din da suke bata kamar da wasa ya zama attitude dinta, domin a yanzu a cikin idannuwanta zaka fahimci halin da zuciyarta ke ciki Suturunsu duka masu ruwan sararin samaniya ne, sai alkyabobi farare kar masu dauke da duwatsu da wasu irin kwaliya Zinaria, har zuwa wannan lokacin bata san wa aka aurawa mijinta ta biyun ba, domin yayarta da ta fita neman rahoto tsaf ta ji ko wacece aman tsoron ta kai labarin nan da bakinta ya sakata nuna kai ita bata fahimci ko wacece ba Abinda ya sa kuwa shine, ba yau ba Najeeba ta zama makiyiyar zinaria da mahaifiyarsu , idan har suka ji wannan bayani ta tabata ba za'a yi da kyau ba abin zai shafi har ita Yannayin zinaria har yanzu a bayane ranta a bace yake fiye da tunanin mai tunani Sai dai ta fasa ihun kukan domin ta wuni yi a jikin mahaifiyarta, sannan itin alkawarurukan da mamanta ta mata cewar ta zuba ido ta gani ba wata shegiya da zata yi kishi da ita ya sakata yin shiru tana sauraron ana mata kwaliya ana shiryata Sallah kawai ke tashin su, har zuwa lokacin da aka gama shirya su A lokacin da Anmy ta ringa bin dakunnan su ita da Ummu sun ga kwaliya Sosai Zinaria ta fito a hajia matar sarki hakorin makarta ko yaya ta juya ta dan daga bakinta yana walwali A haka suka ajiye sarkar da suka shigo da ita dan a saka mata sannan suka nuna cewa ita za'a fara rakawa dan ta tarbi kannenta Ita dai kallonsu kawai take har suka fita kafin ta ja wani uban tsaki har mahaifiyarta ta yi gagawar banka mata wani kallon da ya sakata sada kanta domin masu kwaliyar ba tafia suka yi, su kansu da mamaki suke kallonta haka kawai sai suka ji girmanta ya zube a idannuwansu domin mahaifiyar mijinta ne ta yima haka, yo kishi hauka ne? Bale gidan sarauta ai ta san da za'a mata kishiya! Dakin Nadia suka shiga Irin yanda ta sada kanta abin ya basu sha'awa, gaishe su ta yi kanta a sade sosai Ummu ce ke kallonta, kwarai ta so shaida ta sai dai sam sai ta ki yarda ko wacece, a haka itama suka ajiye tanfatsetsiyar sarkarta suka fadi cewa nan da minti ashirin za'a shigo a tafi da ita Daga nan sai suka yi wajen Najeeba A lokacin da suka shiga, ZAHRA ce tsaye tana ta yi mata vidio tare da wani sauti mai sanyi da ratsa zuciya su duka tana daukansu vidion ne har ita da yaya Dayabu wanda shima ya shigo a karo na uku a yau yana hankalce da kin maganar Najeeba sai dai ya yi murmushi kawai ya kyaleta, gwara ta yi shirun da ta ringa ihun kuka haka kawai kan abinda ba za'a fasa ba Tun da Anmy ta shigo sai ta ji idannuwanta sun cika da kwallah Ta kasa yarda cewa Najeebanta ce zaune a wajen nan, saman wata kujera mai alfarma an rufa mata alkyabarta a saman daurin dan kwalin da ta sha mai tsari da kyan fasali Karasawa suka yi su dukansu sunna kallonta Anmy ta fi kusanci da ita inda yan matan du suka kara rukunkume Ummu, hakama yaran da ta yi yan kwanakin nan sun matukar sabawa da ita kamar wata mamansu Anmy ta kamo habarta kadan ta dago dubanta Sunna hada ido Najeeba ta yi raurau da idannuwanta Kai Anmy ta ringa girgiza mata a hankali ta ce" kar ki bari su zubo su bata kwaliyar nan an matana, kin ga yanda kika yi kyau? Kar ki bari wannan rana ki yi hawaye Najeeba kin san farin cikin da nake ciki kuwa? Da kin san yanda nake jin nutsuwa da auren nan da sai kin fi kowa murnarsa Kuma juyota ta yi sosai tana amsar sarkar da Dayabu ya bude ya ciro ta zinari ce su dukansu iri daya A hankali ta shiga daura mata kafin ta ce" abinda muna tare, ina nan fa, ina tare da ke fa Najeeba ta ringa sauke ajiyar zuciya Mahaifiyarta ce ta matso kusa da ita Itama idon ta kura mata, wai ita ta haifi santaleliyar yar nan? Lalle Allah ya mata kyauta ta saka kafa ta shure ta tafiarta? Murmushi ta yiwa Najeebar dake kallon fuskarta, mamanta sam bata tsufa , bata da kaurin jiki hakan ya sa bata wani zaune ba, sannan cikinta bashi da yannayin wace ta haihu dan mace ce mai matukar kula da kanta A hankali ta dan lumshe mata ido bata cire dubanta da karfin nan ba hakan ya saka Ummu sakin ajiyar zuciya a boye tare da saka ran watarana zata dubeta Nan suka lalace sunna ta daukan hotunna da vidio, Ba wanda ya dauki maganar nasiha, Anmy ce ta katse hakan cewar su bar mata y'a zata yi mata a nitse, to nasihar wacece ba'a mata ba, har mai wa'azi aka kirawo ta mata sosai sai dai abinda ba za'a rasa ba Sai da aka dauki kusan minti arba'in sannan su Anmy suka fara tafia A lokacin da suka nufi runfar aka shaida masu Sarki ya hana zama a nan ya umarci a je falonsa na kurya mai dauke da su camera da sauransu Nan suka nufa cike da ayar tambaya, sunna cike da mamaki Kasancewar tuni yana cen ciki ya saka Anmy na samun waje suka hakimce ita da Ummu tana hangen su Gimbiya kusa da zinaria da wata yayarta, hakama Nadia tana tare da aunty da wasu yan uwansu biyu manyan mata du sunna zazaune ne saman manya manyan kujerun falon sun cika sosai sosai kowace na dan murmushi idan sun hada ido da wata, su kuwa matan kowace kanta sade da alkyabarta Wayar da ta dauka umarni ta bada kan a rako Najeeba da zahrau, da dayar matar sarkin Tana kashewa ta kuma kiran SHAHEED A lokacin an gama masa wani nadin ana ta binsa da turaruka ne Tambayar da ta masa kan me yasa ba'a zauna a rumfa ba? Amsa daya ya bata a hade cewar" Eumfar na dauke da hatsari ne Ajiyar zuciya ta sauke, gaske ta ga dogarai da mai wasan maciji sunna tsaitsaye sun tsare ko'ina da alamu hayaki zai yi Ajiyar zuciya ta kuma saukewa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191