Chapter 62
Chapter 62
su same shi Mahaifiyar Zinaria ce ta fara zuwa da kuyanginta tana tambayar yaya aka yi ya dawo bata sani ba a cikin zuciyarta domin zinaria dai bata iya fada mata abinda ke faruwa ba hasalima tana cen ta gama shiryawa nufinta da ita za'a juya dan ta rantsewa mahaifiyar tata cewar bata san da maganar auren ba, tana cen tana jiran jin za'a tafi kai amarya ne Turus ta yi a lokacin da ta karaso falon da salama a hankali tana kallon yan matan dake jere saman kujera mai tsayi daya da kujerar mijinta wanda ta tabata wanda ya yi wannan gangancin to fa ba karami bane a wajen mijin nata Sai hakimtacen, nutsatsen, zakaran sirikinta dake zaune a dayar kujerar sarakan da idan sun zo sukan zama , sai mijinta gefensa sunna zaune tamkar abokai Dan murmushi ta saki, nan da nan jakadiya ta shiga miko gaisuwa da gaisuwar sarki ta musaman kafin ta karasa saman babar kujerar uwar gidan sarki ta haye ta hakimce ita ga hajia baba Sai ga mai dakin tsakiya itama ta shigo cikin shigarta ta alfarma Ita kam bata tsaya turus din ba saima gagawar karasawa ta zauna da take dan bin umarnin maman Zinaria cewar ta kiyayi neman waje a wajen mijinsu! Sai da suka gama zama kafin da hannunsa ya salami mutanen dake tare da su Sai da ya sha iska irin ta sarakai sannan ya budi bakinsa cikin tausasawa ya ce" ina farin cikin dawowata gareku iyalaina, Ina fatan na sameku lafia, Kawunansu suke amsawa sai irin kurema yan matan ido da ta yi ta kasa kwakwaran motsi Ci gaba ya yi da fadin" Alhamdulilah, tafia ta yi kyau, ina mai gabatar maku da kanwarku, abokiyar zamanku, yar uwarku GIMBIYA ZAHRAU a matsayin matata ta uku wace aka dauran aure da ita yau yau din nan a masarautar DAMAGARAM Baki dayansu sai da suka zabura da jin kalamansa, sai dai irin yanda fuskar ta tsakiyar ta nuna farin ciki karara da sakin murmushi da sada kai dq sauri ya sha bamban da irin yanda firgici tashin hankali, tukukin bakin ciki ya nuna kansa a fuskar maman Zinariya kafin take aro abinda ta fi iyawa wato kirsa ta yafa ta ringa kokowar danne bacin ranta ta yi iya yinta ta sasauta numfashinta har ya kuma furta" KANWA ce a wajen sarkin DAMAGARAM, Dubanta ta kai wajen mijin yar tata, wada take matukar shaku da tsoro, zata iya rantsewa idan sun yi magana da wannan mutumen bai fi a irga ba, domin yawancin lokuta koda maganar ta hado su da kai ne zai bata amsa ko da firgitatun idannuwan nan nasa ko da yar yatsarsa, idan kuwa abin ya kakare ya zama dole sai ya yi magana zata iya rantsewa a rasuwar dansa ko a wani gagarumin jajen da ta masa ne ya iya furta mata kalmar *ALHAMDULILAH* kawai Kafin ta maida dubanta kan yan matan Bata taba gannin bakar fatar da ta kayar mata da gaba irinta yaren nan baki dayansu ba, bata taba jin gabanta na dukan tara tara a gaban mace yar uwarta sai da ta ganta gaban yaren nan Me hakan ke nufi? Me auren sirrin da mai martaba ya yi ke nufi? Yaushe haka ta faru Zinaria bata sanar mata ba? Yaya aka yi sarkin ne da kansa ya kawo amaryar? Wa'inda suke tare kuwa su waye? Kara danne abinda ke damunta ta yi tana mau yiwa kanta alwashin ba abinda zai faru, zata kawar da ita kamar yanda take kawar da sauran kudirinsa na auren! Wato da ta bara masa wannan shahsashar bata ishe shi kwalamarsa ba sai da ya jara hango wata? Watarma kanwar sarki bama yar sarkin ba? Kanwarma ba ta jinni ba ta tabata yayan nan ne da Zinaria ta tsana gashi yau yau yarima yake dawowa daga tafiar da ya yi zai zo tare da matarsa da yarsa, Murmushin da ta saki karara zai nuna maka irin murmushin nan ne da ake yi iya laba kafin ta furta" masha Allah, Allah ya bada zaman lafia, bismillah ta tashi mu je ciki a yi mata shirin amare Sai a lokacin SHAHEED ya dago da dubansa ya sauke saman fuskarta, irin kallon da ya yi mata ne ya sakata saurin sada kanta ta yi shiru Sai da Sarkin garin Agadez ya shirya magana sannan ya furta" an gama yi mata komai, harta wajen zamanta an tanada, Allah ya sakawa gimbiya da alkhairi Wannan lamari ya kara girgizata, haka dole dole suka juya suka koma Sai da ya sadata da bangarenta wanda cikin ikon Allah bangaren ya kawatu da bangare biyu ne, kiri kiri SHAHEED ya zarce dayan ya saka kys ya bude ya shiga Da baki bude suka raka shi da kallo kafin suke kallon junna Hannayenta Zahrau ta kama a sanyaye ta ce" eyah, kin ga wace ake tunanin zata zubar da hauka sai ta zama wace ta fi kirki a cikinsu NAJEEBA ta yi sakalau da baki tana kallonta kafin ta ce " wato dai ke kunanyenki ke anfani a jikinki aunty? Zahrau ta kara tsareta da kallo Najeeba ta girgiza kanta ta ce" to ki saurara, idannuwanki nake so su kasance masu taka tsantsan, sannan bara na je na sanyo mamanki tana waje da kannenki tun safe, oh ki ce harda Dunkum a bangarenki? Da sauri du suka zaro ido har sunna rige rigen shigewa ciki jin alamun zai fito A hankali ya furta" ya zama dole mu zauna har kwana biyu a nan, dan ba zan tafi na barku a nan ba Yana gama fada ya fita da kansa dan gannin wa'inda ake so su shigo Nan da nan fadar ta dauka Farin ciki ne karara a fuskokin mutanen fadar da mamakin ashe dama zai iya kara aure? Farin cikin ya gama tarunma matarsa ta tsakiya wace ke tare da madaukakin farin cikin da ta kasa boyewa sai sanarwa yan uwanta take sunna tayata murna har fadi suke ya fara sakuwa itama zata samu yanci da yin adu'ar Allah ya basu zaman lafia Ita kuwa tana komawa ta kama kiran nunber zinariya wace nakudar dole ta kamata take ta gunjin kuka jin wai har sun tafi kamar zata haukace sai hauka take zubawa a gaban kuyanginta sunna biye da ita ga likita an kirawo ga Anmy a gefe a tsaye ta harde hannayenta tana kallon ikon Allah .......................................... Sun gana da yan uwa da bakin da ya yarda da su kafin yake zarcewa wajen sarki suka sake zama Irin adu'o'in da ya kara koyawa sarki ya saka shi kara jin nutsuwa da jin dadin auren, a haka yaronsa ya sauka da matarsa da yarsa Kana ganninsa zaka gane mutun ne dan gayu, sannan ya samu sangarta domin sai da ya karasa ya rungume aban nasa duda kasancewar katon namiji ingarma Sunna gamawa suka koma bangarensu da matarsa wace suke cikin masifa kusan sati biyu kennan rabonta da ta yarda da shi yana cikin tashin hankali da bukatar mace kasancewarsa mabukaci dan kawai ya yi budurwa a cen ta sakoshi gaba gata dama mahaifiyarsa ce ta daure mata take tsula iskancinta son ranta Shi dai ba mazinaci bane, aman a irin yanda yake jin kansa komai zai iya faruwa da shi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191