Chapter 67
Chapter 67
hannayensa aje saman kansa muryarsa na rawa ya furta" innalilahi wa'inna ilaihi raj.une, hasbunnalahu wani'imal wakim aya ta tabbata a kaina ni MUTALAB gashi, abinda na aikata ya kamo ni da wuri haka a kan yarinyata." Sai ya fashe da kuka yana kallon yanda D'AYABU ya tsurawa sarki ido kamar wanda ya suma a zaune. Da sauri Anmy dake kukan itama ta kaleshi a firgice jin zai tona asirin da suke lullub'ewa kansu da k'afarsu, zai tonawa kansa asiri a cikin irin rud'anin nan da suke ciki zai k'ara masu wani. Duban da Ummu ke masa ne ya saka shi k'ara sada kansa yana hawaye Ummulkhair ta kalli Najeeba wace ita ma ita take kallo kafin Najeeba ta bud'a bakinta a hankalΓ¬ tana kallon Ummulkhair tana dan yatsine fuskarta tace" eyah, eyah, yau kin yarda da ayar tambayar da na d'ora a kan maganar da Abih kan fad'a wani sa'in?" Maida dubanta tayi wajen Abih a sanyaye ta furta" *ABIH, WACE AYA CE TA TABBATA A KANKA?* komawa sarki yayi ya jinginar da bayansa jikin kujera yana lumshe idannuwansa, ta faru kuma ta k'are, rikicin cikin gidansu zai k'ara kunnuwa a yanzu, ya tabbata wani tashin hankalin ne zai k'ara kunno kansa hakan ya saka ya idasa had'e fuskarsa da dukan wani abu wai shi annuri ya lumshe idanuwansa a lokacin da Anmy a firgice ta kallesu tace "... Happy juma'atπ§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π» *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π» *Na* *SAJIDA* π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€ β *[ T.M.N.A]* β πποΈ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 27 A firgice, a rikice, a tsawace Anmy ta ce" yaya muna cikin wannan tashin hankalin zaki yi mana wata tambaya kina mai kokarin tirke mun tamkar kece uwarmu mu kuwa y'ayanki? Baki daya yan matan sai abin ya basu mamaki, yannayin Anmy din ya saka jikinsu ya yi sanyi harma du suka zuba mata ido da wani irin duba na mamaki Anmy ta kawar da kanta tana jan hancinta tana kara rintse idannuwanta da sukai mata luhu luhu ranta hade ta ce" ku tashi ku je dakin ku Jiki sanyaye du suka mimike, Najeeba ta kara waigowa ta kalli mahaifinta ta ga kansa a kasa sannan hannayensa sai rawa suke, ta kai dubanta wajen yayansu ta ga shima kan nasa a sade shi kuwa kuka ne yake a hankali ta saci kallon mai martaba ta ga ya yi wata kwonciya a jikin kujerar ya daga kansa sama idannuwansa lumshe rawanin dake kansa ya kara fadi sakamakon yannayin kwonciyar nasa, shigar alkyaba ne a jikinsa mai ruwan duhu wace ke da igiya wajen wuyanta, fari kal din hannunsa daya ne a waje yana rike da sandar girmansa dake ajiye a kusa da kafarsa, sai dayan dake dafe da gefen zuciyarsa Da sauri ta cire dubanta a kansa ta juya da wani irin sauri ta bi bayan yan uwanta Sunna shiga da sauri Ummulkhair ta zube a kasa tana mai dora hannunta saman kanta tana dubansu a rikice ta ce" shin kun fahimci abinda na fahimta? Kun gane cewar akoy wani gagarumin sirin dake damun mahaifinmu wanda da alama mahaifinmu ya shafa wanda nake kyautata zaton idan har ya fito fili mun kade? Najeeba ta jefar da iPhone dinta saman kujerar dake ajiye ta cire alkyabar jikinta ta jefar ta zauna a kusa da Ummukulsum ta shiga cakuda gashin kanta Dagowa ta yi da wani irin yannayi ta ce" aya ta kasance a kansa da wuri? Bai fadi haka ba sai da ya ji cewar wannan tsautsayi ya afku da Ummu? Me ke faruwa da mahaifinmu? Wace aya ce wannan ta kasance a kan ubanmu? Ummukulsum dake share hawaye itama ta budi bakinta a hankali ta ce" sai jake jin tsoron abinda zuciyata ke fada min, sai nake jin tsoron abinda nake tunani Ummulkhair ta ce" me kike tunani ummu? Ummu itama ta dora hannunta a kanta ta ce" sai zuciyata ke ce min bayan mahaifiyata mai amsar kudin zina ce mahaifinama ya taba fadawa wata Da sauri Najeeba ta matso kusanta tana daga hannunta da ihu ihu ta ce" ke ke, yi min shiru, walahi zan tsinka maki mari idan kika fadi cewar Abih ya taba yiwa wata fyade Ummulkhair ta shiga yarfe hannayenta tana fashewa da kuka ta ce" Najeeba ai ba haka ta fada ba, abinda kike tunani ne kika fada kuma nima abinda nake tunanin kennan innalilahi wa'ina ilaihi raj'une me ke faruwa da mu? Itama Najeebar baki daya kafafuwanta ne suka gaza daukanta Tana kokarin zubewa kasa Dayabu ya shigo Da wani irin sauri ya karaso ya tareta a jikinsa suka kai kasan tare Da rarafe sauran suka karasa wajensa suka rungume shi sunna kuka baki dayansu Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, yake maimaitawa hankalinsa a tashe ya shiga fadin" tabas kadara, mumunar kadara ta faru da kanwata, sai nake jin ba wanda ya kaini jin ciwo duda irin yanda aka fada min lamarin cewar ba da son ransa ba, duda na san Allah ya kadarto hakan, sannan har an yanke hukunci zai zama mijinki aman zuciyata ta kasa daina hawaye Tsoro nake ji , walahi tsoro nake ji Idan ita ummu ta faru da ita a wajen mutunci wajen da aka isa a tankwasa karfe komai taurinsa ku fa? Shin wace irin kadara ce ta afkawa mahaifinmu ya aikata mana haka? Da sauri Najeeba ta dago kanta tana kallonsa DAYABU da hankalinsa ke tashe ya shiga fadin" ba zan iya kuma zuba maku ido kuna yawo haka ba, du ku fitar da mazan aure a cikin manemanku a yi maku aure ku tare a gidajenku hakan zai saka mani nutsuwa a cikin zuciyata, walahi idan ayar nan ta kuma kasancewa a kan wani a cikinku bana tunanin zan iya yafewa Abih! Lebunanta ke hadewa da junna sai jimkesu take tana kara budewa A rikice ta ce" me me ya yi ne wai? Me ya yi? DAYABI ya sasauta masu rikon jin du sun dago shi suke kallo Kansa ya sada ya kasa magana hakan ya saka Ummukulsum dora hannunta a kai ta shiga zunduma ihu tana son mikewa ta yi burgima ko zata ji sanyi, cikin muryarta take fadin" shikenan uwa karuwa uba karuwi ko dai ni shegiya ce ban sani ba? NAJEEBAma dake kuka tana kallonsa ta ce" yaya waye shege a cikinmu? Ummulkhair kam sai ta kame, gaba daya ta kasa kuma motsa hannayenta tambayar da yan uwanta ke yi take jiran amsarta Hannunsa ya saka ya rufe bakin Ummukulsum sannan ya ringa bin Najeeba da kallo wace ta zama uwa wata wada ke son tashi sai tsale take tana kai kawo sai kuma ta tsaya tana kallonsa gashi kanta baki daya ta balbaza shi hannunsa ya saka ya jata kasa da karfi hakan ya sa ta yi wani irin zama dabar a gabansa gabanta na yi mata wani irin tsalen albarka kamar zai bale ya fito daga kirjinta Wayarsa ya dauko ya shiga galeri Hoto ya fitar saman wayar tasa ya mika masu Har rige rigen amsar wayar suke suka tsurawa hoton ido Yannayinsa a kansu ya ce" sunnanta *HUWAILA* , sati daya ne tsakaninku ita da Najeeba, Tana nan garin zaune gidan kannin mahaifinta tana karatu a lycee Du da iein tarin kamanin da take kamar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191