Chapter 79
Chapter 79
ta ji wanda ya aureta nan fa hankalinta ya k'ara tashi idanuwanta suka rufe ta ko wace hanya neman abinda zata lalata lamarin take, shine ta ringa tak'ale tak'ale ganin dai b'angaren Zahrau yarinya ce mai matuk'ar biyayya da matsanancin kamun kai, hakama mahaifiyarta sai kawai ta shiga yada masa magana cewar yanzu da sarkin ya ji ya aikata haka yaya za'a yi ya so had'a zuri'a da shi? Shine fa shima ya ce da ita "In banda abinki Mardiya ni kuwa na had'a da ke?" (Wato idan baki ya san abinda zai fad'a bai san amsar da za'a bashi ba) shine fa ta ringa fad'e fad'en maganar da idanuwansa suka rufe ya wan wanka mata mari domin fadi take" yanzu haka ba ita kad'ai bace shegiyar har sauran duba da irin yanda suke da halayya na shegu." Kamar wani wanda shege yake da halayya tasa daban, hakan ne ya saka Abih hankad'ata yana nunata da yatsa ya ce ta daina sheganta masa y'aya. Sai aka yi rashin sa'a ta kaiwa madubi duka, dama abinda zai kaita gidan sarki take nema sai kawai ta fad'a motarsa ta nufi gidan sarkin, tun da aka fito daga sallah ta tsaya a hanyarsa dogarai na kakarewa aman sai da ta yi yanda ya gane itace kafin ta fasa kuka ta yi hanyar b'angaren Anmy. Burinta ta fasa wannan sirrin y'ayansa su san abinda ya aikata, ta wanzar da tashin hankali tsakaninsu da mahaifinsu da su kansu. A hankali Anmy ke girgiza kanta kafin ta ringa furta "Innalilahi wa inna ilaihi raj'une." Da sauri ta shiga tatara k'annanun da su suna cike da tsoron ganinsu zaune gaban mai martaba dan su tsoronsa ma suke, sai Nusaiba dake ta mak'alar wuyan DAYABU tana wasa. Anmy du ta tattara su ta tura su ciki tana jin kamar juwa zata kifata da k'asa. Shi Kansa sarki sai ya sada kansa k'asa yana jin yanda kansa ke sarawa, ayau yana tare da b'acin ran da wannan fitinaniyar ta haddasa masa, sai ga wani gagarumin da ya tabbata Anmynsa sai ta shiga matsanancin tashin hankali, uwa uba Abih. Abih gaba d'aya jikinsa ne ya ji ya fara masa wata mijirya kafin ya d'ora hannunsa daidai zuciyarsa ya rintse idannuwansa wasu zafafan hawaye suka shiga biyowa gefen kumatunsa. Anmy ta sada kanta sai kawai ta fashe da kuka tana girgiza kanta tana b'oye fuskarta dan kunyar da take ji da irin maganar Mardiya. Baki d'ayansu hankalinsu ne ya k'ara tashi, hakan ya saka du suka rasa ina zasu nufa, wajen Anmy din ko wajen Abih? Da rarafe wa'inda suka fi kusanci da Anmy suka yi kanta suka ruk'unk'umeta, wa'inda suka fi kusanci da Abih kuwa Ummukulsum ce da Dayabu suka yi wajensa da Nusaiba suka had'e a jikinsa. Mamakin hakan ya saka Anmy d'agowa hannunta na rawa ta kai dubanta wajen SHAHEED ta ga kansa a sade, aman ya damk'i sandar dake kusa da k'afarsa da damk'a mai tsananin da ya hadasa jijiyoyin hannun nasa k'ara yin tsaye rad'o rad'o. A rikice take tatab'a jikinsu ta shiga fadin" baku yi mana fushi ba? Wallahi zan fad'a maku yanda aka yi, kun san k'adarar bawa bata fice shi kar ku yiwa mahaifinku da ni kaina da na taya shi b'oye sirrin nan fushi." DAYABU dake dafe da hannun Abih wanda ya dafe daidai zuciyarsa muryarsa na rawa rawa ya ce" ABIH, kar ka kashe kanka a irin wannan lokacin da matarka take son tona asirinka dan manufarta da mu kanmu bamu sani ba, Abih mun san da maganar nan dan girman Allah ka sassauta kar ka had'iyi zuciya domin idan ka mutu mu mukai asara ba ita ba." UMMUKULSUM ta ririk'e hannayensa tana dannawa ta ce" Abih zafi nan ke maka? Idan yana zafi mu je asibiti, Abih wallahi wallahi bama jin kunyar ubanmu ko haushinka domin a haka muke son ka." NAJEEBA ta k'ara rik'e Anmy tana b'oye fuskarta a jikinta tace" Anmy, meye na kukan? Kanmu aka fara ko kanmu za'a rufe?Anmy, koda mu dukanmu ne shegun shine aka ce zamu zo mu shak'e maku wuyan a kan me hakan ta faru? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, Anmy ba shege bane abin gudu, d'an halal d'in aman mai halayan shege! Anmy, ai ba daga yannayin da aka haifeka kake nuna halaya ba, halayanka na nuna wanda ya baka tarbiya." "Anmy, kowani tsuntsu kukan gidansu yake yi! Koda dubu ya tara mu ubanmu ne, babu wata hallitar da zata zagar mana shi bamu sauke hak'oranta k'asa ba na rantse!" Ummulkhairma kukan take tana kara share hawayen Anmy ta buda bakinta ta ce" Anmy, ku daina kukan nan haka, kin ga fa Abih sai rike daidai zuciyarsa yake Najeeba ta saketa tayi wajen Abih ita ma ta d'ora kanta gefen k'afarsa tana jin kamar ranta ne ake wasa da shi, irin yanda iyayen nata ke zubar da hawaye sai ta ji tsoron Allah ya k'ara shigarta, wai kunyar duniya kennan, duniyar ma yayanka, ina ga kunyar Allah? (ALLAH, ALLAH, DAN GIRMANKA DAN SOYAYARKA DA FIYAYEN HALITA ALLAH KA SHIRYE MU, KA YAFE MANA, KA SA MU GAMA DA DUNIYA LAFIA, KA RUFA MANA ASIRI DUNIYA DA KIYAMA). Anmy da Ummulkhair ma da rarafe suka k'arasa wajen Abih, Anmy ta d'ora hannunta inda hannunsa yake tana hawaye tace "Ya isa, daga yau nauyin sai ya tafi ya baka lafia, yaya sun ji, sun sani sun sani." Sai ta had'e kanta da su suma sunna ta hawaye, shi kuwa da hannunsa yake daddab'a su yana jin wani irin a cikin ransa. SHAHEED kuwa abu d'aya ya hana shi tashi daga zaunen da yake shine shara'a, ya hau kujerar nan ne dan ya yi shara'a tsakaninsu tana zaune ta kawo k'ara ne, du irin kukan da mahaifiyarsa ke yi tamkar ana narka dalma ne ana zuba masa a k'irjinsa. Mardiya kuwa baki da hanci duka a bud'e suke ta yi wani fik'i fik'i tana ganin abin na neman juyewa a kanta. Anmy dake kuka tayi saurin d'agowa, hannun Dayyabu ta damk'o sannan ta damk'o na yayanta tana hawayen nan ta ce "Insha Allahu ba zamu yi kunya ba, insha Allahu Allah zai yi ta rufa mana asiri." A hankali ta kuma fad'in" *YAYA, DAYABU, SHIN ZAKU BAIWA MAI MARTABA AUREN Y'ATA?* *INA BARAR AUREN YARINYATA WA SARKIN DAMAGARAM, INA BARAR AUREN Y'ATA WA YARON KA*?" Ta karashe tana mai hade hannayenta da nuna Abih. Tunda ta fara neman auren ya d'ago da rinanun idanuwansa ya tsura mata daga ita har yayan nata da kuma y'ayan nata, suma y'ayan mata biyu da suka yi saura sai ya zamana kukan nasu ya d'auke d'if sai kallonta da suke da kallo irin na son ta idasa maganarta. Anmy ta k'ara kamo hannun Abih na dama tana mai k'ure shi da kallo, gwara a yita ta k'are, gwara ta nunawa Mardiya a lokacin da ka so wulak'anta bawa Allah kan rufa masa asiri, gwara ta fad'i muradinta idan ya so ko wace wace, idanuwanta a kansa, su kuwa idanuwansu a kanta inda zuciyoyi suka shiga bugawa tamkar zasu b'allo su fito daga k'irjin da dama a wajen. A sanyaye tace " _Idan kun yi comment zafafa, zaku samu zafafa🤣, wasan fa yanzu ne ya fara._🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191