Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 123

Chapter 123

Mage Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

ina hura hanci rai bace da kudadena da katina na banki na tafi na bar kasar haihuwata" Sasautawa ta yi sakamakon hawayen da ya fara zubo mata daga gurbin idannuwanta A hankali ta ci gaba da fadin "sai dai kashh, da na sani, da na kawar da kaina, na hadiye wulakanci da neman fitina da tashin dukiya da irin yanda kudi ke dukan kansa ke saka shi aiwatarwa a gareni na rungumi yan dagwai dagwai dina na rayu da farin ciki, domin kuwa daga bakin lokacin da na sauka, na fara kokarin ciyar da kaina, tufatar da kaina, neman abinda zan yi dan inganta rayuwata duk da tarin takardunna, da dukiyar da na tafi da ita ta gadona da iyayena suka bara min, sai rayuwata ta zamo wata sabuwar rayuwa mai cike da duhu duk inda na ga yaro ko yarinya sai na saki murmushi sai kuma hawaye ya biyo baya Idan na zo kwontar da hakarkarina wani sa'in idan nonona ya soke ni sai ki fado min a raina Nakan zabura ni kadai a dakin hotel dina ina jin kamar muryarki kina fadin *"MAMA, ZAN YI FITSARI"* Na rayu cike da burin zama wata abu, da son goge ku a rayuwata na manta da ku na sake wani auren na haifi wasun Sai dai me? Ashe na yiwa kaina mugun illah ta hanyar shakuwa da ku, Makwoncinmu daya A tsakiyarku nake kwanciya inai maku tatsuniya kunna hayewa jikina kuna kokoyi, Idan kukai fada nakan ji hankalina ya tashi, zan saka ku shirya ta hanyar nuna maku ilar abin Na saka shakuwa mai tsanani a tsakanina da ku, da yayanku har ya kasance na zabi kulawa da yara a matsayin karatuna" Sosai take hawaye hakan ya saka ta saka hannayenta ta toshe bakinta dan kuka take son yi sosai Dayyabu kansa da yake mai saurin hawaye ne idannuwansa sun cika da kwalla, hakama sauran du hawayen suke zubarwa ciki kuwa Harda Najeeba dake hango duk abubuwan da take fada a zahiri kamar a lokacin komai ke faruwa da rayuwarsu Mikewa ta yi da sauri ta juya da nufin tafiya, domin ita dai da bakinta ba zata iya furta masu dalilin fushinta ba Karron da ta ci da shi ne ya sakata kokarin zubewa Sai dai bai bata damar hakan ba ta hanyar tareta sosai da hannunsa kafin ya maidota dakin da kyau kusa da yaran ya aniya zaunar da ita yana kallonta a sanyaye ya ce... 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 46 A sanyaye ABIH ya ce" ina zaki je bayan ina jiran wannan ranar shekara da shekaru dan na baiwa Najeeba amsar tambayarta wace du sauran yan uwanta ina iya basu amsa kai tsaye na dalilin da iyayensu suka bar gidana aman ita na kasa bata amsar?" A tsorace take kallonsa, bakinta na rawa ta ce" amsar? Wace amsar kake tunanin zaka iya fada masu?" Abih ya dan yi mata murmushi mai ciwo a hankali ya furta" haba *SIRRINA*, baki san sun san wani *Sirrin* rayuwata mai tsanani kuma suka hakura suka ci gaba da mutuntani ba? Yaya kike so ki ci gaba da fuskantar irin wannan shariya da abubuwan da y'arki kwalin kwal ke maki a kan namijin da ya kuntata maki? Kina da bukatar samun girmamawa, soyaya, kallon daraja daga wajenta, tabas kina samu daga wajen yan uwanta aman ita din ke kika haifeta fa? Dan Allah ya isa haka, ki barni na fada" Har bakinta rawa yake ta furta" aa, ba ruwanka da abinda ke damuna, ni ban rokeka fadin wannan abin ba, ina fadawa Allah idan lokacin ta dubeni ya yi zata dubeni dan kanta" Murmushi ya yi yana dubgure kanta ya karasa da sauri ya zauna gaban y'ayam nasa ya ce" ba ga irinta ba, ci gaba zata yi da boyewar, tana kakare laifina, ita dai a haka take so ta kare?" Najeeba, na auri mata goma sha bakwai a rayuwata Cikinsu ba wace ban haihu da ita ba, kuma ba wace ta ga girman y'arta take fecewa Na birne mace uku a gidana wa'inda suka rasu a hannuna, sauran goma sha ukun nan du rabuwa muka yi, banda mardiya ta sha hudu Najeeba, kamar yanda kuka sani, wasun dalilin na tarda su sunna dukanku ne, wasun rana tsaka zaku tubure da rigimar bakwa son su, wasun zasu nunan ba zasu iya rike y'aya birjik haka kawai bane, wasun zalamarsu ta saka, wasun kuwa sun aikata abinda ya hana min yafe masu ne ya saka ni rabuwa da su aman banda *NANA MARIAMA* Sai da ya kalli UMMU dake kallonsa da mamakin wai da gaske bayanin zai yi ya yi murmushi ya ce" aminiyar BILKISSU ce, wato Ammi dinku, ita ta yi mata gorancen aurenta, sun kasance masu raba ayya daya, sunna rike sirrin junnansu duda BILKISSU ta bata shekara UKU a haife wanda hakan ya saka idan ta yi niyar tsokanarta ko idan tana cikin yannayi na tashin hankali takan kirayeta AUNTY domin takan ce da ita "Bani da kowa sai Allah sai ke" Min sasanta kanmu da NANA MARIAMA a lokacin da nake amsa sunnan Yaro da kudi, ina jin wani irin tashen kudi dake daukana yana yawo da ni yana dadani da kasa Na tara y'ayan sai dai ba wai takamaiman su din ne a gabana ba, ina dai da wani irin kaunarsu a zuciyata wada ke sakawa idan aka yi katari na dan zauna na ji damuwarsu to fa ko wace iri ce zan dage na magance masu banda zama da su da kukawa da tarbiyarsu da kuma gane irin ilar sakin iyayensu da shigowar bakin fuska a matsayin sababin iyayensu ke janyo min Sai da na auri NANA MARIAMA na fara gane meye ma'anar zuri'a, Tanadinta zuri'arta, burinta zuri'arta, farin cikinta zuri'arta, abokannanta zuri'arta a lokacin ta shigo ta tarda mahaifiyar Ummukulsum da tsohon cikin Ummukulsum Zamansu bai yi nisa ba na sawake mata a lokacin da ta haifi yar jaririyarta sakamakon gannin itama ta haihu yanzun zata fara ware nata daban sauran daban wanda na kamata da hakan sau uku karshe dai na sawake mata na ci gaba da koyon rayuwa a wajen NANA Mariama Fadace fadace, rashin zaman lafia, rigingimu na tsakanin miji da mata kan hada mu, sai dai wani ikon Allah daga lokacin da zan tabo ku zata zube a kasa gwuiwoyinta a kasa tana kuka ta ce" ka yiwa Allah ka yiwa Annabi muhamadu salalahu alaihi wa salam ka barni na huta, ka barmin yara su huta, kai baka gannin yarintarsu, soyayarsu, karfin zuciyarsu? Kar ka hargitsa min tarbiyarsu ko ka birkita min zaman lafiyarsu, yaren nan sune farin cikina, kai ka san ba dukiyarka ko kyanka ya saka nake hakurin zama da kai ba sai dan yaren nan" Abinku da wanda shedan ya rigaya ya buga min ganga sai na sheke da daria sai na kalleta a kaikaice na ce" ku ji shishigi malan, yara ina ruwanki da su? Su tashi a tashama mana na san tarbiya ta Allah ce ba ta wani ba, dan haka idan kin gaji da zama da ni ki kama gabanki!" Zata kawar da kanta, ra mike

Table of Contents

Chapters

191 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191