Chapter 121
Chapter 121
amma ya ki zuwa, gashi ni ba sakina ya yi ba" Dan saurarawa ta yi ta dan dago dan gannin shin tana sauraronta? Gannin Ammi na kallonta da kyau ya saka ta ci gaba da faɗin "Idan laifi na masa tsakanina da shi ai ya ci ace ya yafe, idan kuwa fadana da yara ne ba ruwansa ya fita a ciki domin tsakanina da su ne" Da mamaki Ammi ke kallonta a kasan zuciyarta kuwa faɗi take 'Ikon Allah, wai ita a gidansu ba'a fada mata ka so mutun ka so d'ansa ba?' Dubanta ta kuma kai wa wajen Ummu dake dan jijjiga Nusaiba, ko nauyinta bata ji haka take jibgata a baya ta yi ta jijjigawa, a yan kwanakin da ta yi da yarinyar ta matukar sabawa da ita domin yanzun Mama sak take kiran Ummu da shi kamar yanda sauran yaran ke faɗa. Mikewa ta yi ta nufi wajen Muryarta a dan dake ta ce "Sannu fa?" Dakatawa Ummu ta yi ta juyo daga wajen yaran dake ta mata surutu Ido cikin ido suka kalli juna, ita dai bata santa ba, sam bata taɓa haɗuwa da ita ba, ko hotonta bata sani balle ta shaida ta. Ba wata shigar firgita mutum ce a jikin Ummu ba, domin riga doguwa ce sakakkiya baka a jikinta Sai dai yannayin tarin kamalar da fuskarta mai cike da yalwataccen gashi da ɗan murmushi ya saka Mardiyya jin shakkun yi mata magana a gatsai gatsai Dan haka sai ta dan kakari murmushi ta ce "bani ita na rarrasheta ko zata yi shiru? Kallon da Ummu ke mata dan ta fahimci ko wacece ita, sarai ta san matar ta hoto amma ko ita bata taba haɗuwa da ita gata gata ba A hankali ta ringa kunce goyon kafin ta juyo da Nusaiba ta mika mata ita Da farko idon yar a rufe yake, hakan ya sa ta yo lufff a jikin Mardiyya, sai da Mardiyya ta ce "A'a, bata da lafiya ne? Jikinta zafi haka me yake damunta?" Jin muryar ya sakata buda idannuwanta Kallonta take kafin ta fara rigimar sai ta koma wajen Ummu (idan baku manta na Nusaiba yarinya ce karama, ko a haka Mardiyya ta kasance mai yawan zaginta hantararta da yawan faɗa, a rayuwar yanzu ko ɗan naka ya mallaki hankalin kansa sai da addu'a da kawar da kai, bare yar yarinyar da ta samu mai rarrashinta da nuna mata soyayya hakan na iya haifar da son nisantar mahaifiyarta da ta haifeta, karamin abu ne hakan) Da mamaki ta kalli Ummu, da yanayin shashanci ta ce "ke ko har kin canza uwa ne haka zaki ringa kuka a hannuna?" Ummu kam wajen ta bari ta koma saman kujera ta zauna tana mai bin Wudiliya da kallo wace ke zaune tana bin kowa da kallo itama Wani murmushin ta yi ta kuma maida dubanta wajen yaran Da idannuwanta take gallawa duk wanda sukai ido hudu harara, sai dai a yanayin yanda ta lura sun rigaya sun hade kan nasu na iya shege wato kar wanda ya gaishe da Mardiyya? Sallamar Dayyabu ne ta saka su duban wajen Shine ya fara shigowa cike da yalwatacciyar fara'a a fuskarsa Bayansa wata yar budurwa ce kyakyawa fara tas , ta saka abaya baka har kasa ta yane kanta da mayafinta Du sai yaran suka shiga murnar zuwansu Zahrau ta mike tana yafa dan kwalinta cike da nuna kulawa suke yiwa budurwar yayan nasu barka da zuwa Kasa ta zauna kanta kasa tana murmushi tana dan murza yan yatsunta, shi kuwa yana zaune kusa da Ummu yana mata magana kasa-kasa, haka kuma kannansa duk sun zagaye shi ban da Zahrau da ta shiga hidimtawa bakuwar cike da fara'a Hannun Bilkisu ya dan doke ya ce" Mairama ki barni da tsegumi wai ba yayarku bace ku je mana ku tambayeta" Jin abinda ya fada ya sakata dan dago dubanta tun bayan gaishe su da ta yi Dan murmushi ne a fuskarta kafin ta mika hannu a hankali ta furta "Ku zo" Sai da suka kara kallon iyayen nasu kafin duk su yi wajenta Ai kuwa ta ringa cafe hannayensu suna gaisawa duk da ba sakin jiki suka yiwa juna ba amma fuskarsu da mawadacin farin ciki Baki ta tabe kasa-kasa ta ja tsaki sai kokowa take da Nusaiba dake son zuwa wajen Ummu Ammi ta kai dubanta wajenta ta ce "Mardiyya, barta ta je wajenta mana, mamanta ce fa, mahaifiyar Najeeba ce" Da sauri ta dago ta kai dubanta wajen Ummu, Sam Ummu bata kallonta, hasalima dariya take yiwa maganar DAYYABU na irin rigimar da suka sha kafin budurwar tasa ta yarda ta zo gaishe da su A hankali ta furta "Na ji dadin jin haka, hakan na tabbatar min da tarbiyyarta, har ma na ji ina zumudin kasancewarta matar yarona" Tana maganar tana kai hannunta gefen fuskarsa ta dan shafa a hankali sunna dariya a tare Wani irin abu ne ya tokare kirjinta kokowa take da abinda zuciyarta ke tambayarta, dannewa take dan kar ya fito fili tana kara kallon su UMMU da DAYYABU ga kuma AMMI dake ta sakin murmushi da alama ta manta abinda ya kawo su gidan ko meye. Zuciyarta ce ta ci gaba da fadin 'What? Meye wannan? Wani irin abu ne wannan? Ko dai yar uwarsu ce? Meye tsakaninsu mai karfin da take zaune rashe rashe a gidan Ammi haka? Goye da Nusaiba ga kuma yaran sai wani hira suke uwa wace ta haife su da cikinta?' Daga dogon corridor din dake hadawa da bangaren SULTAN iso ya ringa shigowa cikin maganar mutun kamar biyu Da sauri Ammi ta kai dubanta, hakama Zahrau da du wani wandake wajen Ita ce ta sanyo kai, cikin shigar da ta tafi da ita wato alkyabarta ce sai dai kamshin turaran ba wanda ta je da shi bane, kamshin turaran SHAHEED ne ya fara dukan hancin duk wani wanda ke wajen Da sauri yayunta suka yo kanta, domin ja ta yi ta tsaya tana mai jin kunyar kallon su ido cikin ido Wani irin farin ciki ne ya lulube zuciyar Ammi a lokacin da ta fahimci komai Ummu ta sadfa kanta tana murmushin cin nasara DAYYABU ne ya mike shima cike da farin ciki ya yi wajensu A hankali suka kamota suka nufo ciki da ita Budurwarsa da kallo take bin su, tabbas yau ta kara yarda da irin soyayar dake tsakaninsu, cike da mangari take dubansu, a ranta kuwa ji take inama ace sune haka? Ita bama yan uba bane aman ba wani kulawa da junna da suke da yan uwanta A ranta take jin zata dauri niyyar kusantar yan uwanta koda kuwa ba zasu kulata ba har su samu fahimtar juna Kanta a sade yake baki daya yau kunyarsu take ji, ji take duk sun gane abinda ya sameta hakan ya sa ta kasa hada ido da su sai kara sada kanta take DAYYABU ya ce "Ke wai menene?" Jakadiya da babar baiwar bangaren SULTAN ne kawunnansu sade JAKADIYA ta furta" Allah ya ja da rai , Allah ya taimake ki , Sarki na gaishe ki, yana mika sakon gaisuwa da godiya, yana neman afuwar jinkirin zuwan GIMBIYA" Ammi ta kara yin murmushi kafin ta gyada masu kai suka mike suka fice
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191