Chapter 180
Chapter 180
UMMU ta idasa bakin bed din da Abih ke kwonce, royal bed ne rantsatse wanda ya amsa sunnansa, idannuwansa a rufe suke tamkar mai baci, sai dai ba baci yake yi ba, Cikin nutsuwa ta saka hannunta ta janyo farar takardar dake ciki Warwareta ta yi ta karanta, Fuskarta dauke da yannayi na rashin jin dadi ta ajiye nan gefe domin igiya dayar da ta yi saura tsakaninsa da Mardiya ne ya tsinke Sannu sannu ta haura saman gadon Hannunsa daya dake kusa da idannuwansa ta kamo cikin nata, a hankali ta furta" Gani na zo Aban Dayabu, ka buda idannuwanka , ka fada min dukan abubuwan da suka faru da kai tsayin shekarun nan, ka fada min wanda ya bata maka ni kuwa zan je mu gwada karfi da shi komai girman tsayinsa da karfinsa" A hankali ya ringa sauke ajiyar zuciya kafin ya kamo hannunta ya dora gefen fuskarsa yana mai kurawa fuskarta ido, sannan yana mai jin sanyi na ratsa dukan zuciyarta da tunaninsa, muryarsa a shake ya ce" Ki dawama da ni har karshen numfashina NANA, ki zame mana uwa baki daya Nana, walahi na ga rayuwa, ba zan sake fade fade ba Nana " Idannuwanta ta lumshe a hankali ta kara matsawa kusa da shi kafin ta shige jikinsa ta lumshe idannuwanta bata ce da shi komai ba Shima idannuwan nasa ya lumshe dan ya amsar kennan, wato ta aminta, kuma ta dawo gare shin kennan, baci ya shiga nema domin rabonsa da bacin har ya manta sai barawon dake fuzgarsa ya dan taba ya farka tsabar damuwa A washe gari aka tafi da MARDIYA, domin koda kuwa labarin mutuwar ya nuna ba da gangan ta kashe y'arta ba hukuma ta ki aminta da haka, sun tafi da ita sai yanda hali ya yi (Ku mu saba da dane zuciyoyinmu, ku mu ringa yiwa kawunnanmu adu'a kan Allah ya sa mu fi karfin zukatanmu) A hankali abubuwa suka fara komawa gurbinsu, du mutane suka kama gabansu ciki harda Zahrau da yarima da dayar kishiyarta Sosai yayan Ammi suka yi sanyi da rayuwa, barema Ummulkhair, ta jima tana nisa cewar a bayanta Nusaiba ta rasu, sai Najeeba da take dan fama da zazabin dare da kewar kanwarta Nadia a wajen take wuni sai dare take tafia bangarenta Sultan kam ido ya kawo ya zubawa ikon Allahn Najeeba, rabonsa da wani kusanci tsakaninsa da ita tun shinfidetan da ya yi a kan babar kujera Ya rasa ina take shiga da idannuwansa suke gaza ganninta, kwata kwata ta yiwa ganninsa tsada, yakan sauke ajiyar zuciya ya dan girgiza kansa kawai, domin yana yiwa al'amuranta uzuri, lalle tana da tata hujar Ita kanta Nadiar lokaci ya barta har ta kara warwarewa, iyayenta sun zo sosai haka kanwar mamanta na nan har zuwa lokacin A hankali komai ya dawo normal, ya rage samun mutane a kai a kai na gaisuwa Ya zamanta ya koma rayuwa yanda yake yi, a hankali komai ya ringa daidaituwa har du wani tunani nasa ya dawo jikinsa Sannu sannu rashinta a kusa da shi ya fara tasiri Sati uku kennan da rasuwar Nusaiba abin ya gama kama jinni da jikinsa Bilhaki a yanzun kewarta yake, idan ya tuna magangannunsu da ita kuwa irin furucinta yakan ji tamkar an dake shi da karfe mai karfi a dukan gabobin jikinsa, da ace zata kasance mai yi masa uzuri da ta gane ta taka matsayin da ba wace ta taba takawa a duniya, da ace zata iya ganewa da ta ture du wani abin sun zauna, bai je mata da wata magana ba sai dan ya yaba, bai je mata da rokon ta gyara kawarta kuma yar uwarta ba sai dan ya jita daban, ba cin fuska bane, yabo ne Yakan girgiza kansa, a hankali ya furta" Ban yi haka da sanina ba BEEBAH " Sai ya shafa gemun dake habarsa a hankali ya ce" da ace zaki yarda, da na furta maki irin ilar da kika gama yiwa rayuwata Beebah, kin kai wajen da nakan ji a kasan zuciyata cewar ba zan iya babu ke ba" Wayarsa ya dauko a karo na bakwai kennan da zai tura mata mesage ba amsa, shi kansa tun abin na bashi mamaki har ya dawo ya daina bashi mamaki irin yanda yake da naci a kan lamarinta, shine zaune da aikin yiwa mace message, shi da ko aurenki zai yi mai zuwa ya masa zancen daban shi kawai sai an kawo ki zaku hade, dan murmushi ya yi A hankali ya dora dogayen yatsutsansa ya shiga taping din message kamar haka" Kin manta da bawan Allah ne? Ki bani amsa alfarmar rasululah S.A.W " Sai da ta amsa da sallalahu alaihi wa salam, kafin ta tura masa da salama Ajiyar zuciya ya yi yana kallon salamar kamar wani dogon message mai dadi kafin ya dora da fadin" Ina muradin gannin matata, ko zan samu wannan alfarmar? " Bata maida masa da amsa ba sai kurawa Nadia ido da ta yi wace ke ta ciye ciye abinta, sam yanzun ta sake da mutanen gidan tana cudanya da su tamkar yan uwanta na jinni, sannan ko tsakaninta da Najeebar sukan taba hira, maganar sirri ce ta kau, basa wani sirrin junna irin na da Mikewa ta yi ta shige ciki Katon hijab ta sanyo hade da nikaf ta fito Wajen Ammi ta je ta dan duka ta yi mata magana sannan ta mike ta yi gaba Saloon dinta ta nufa Tana shiga ta je ta zauna su Aida suka saki aikin da suke yi suka bita dakin da ta shige Umarnin su gama ta basu sannan ta fara tsife kitson kanta da ya tsufa Sai bayan sun gama ne suka rufu a kanta, wasu na tsifar kan, wasu na wanke mata kafa da akaifu, daya na gyara mata akaifun hannu , mai kunshi na hada kunshin da zata yi mata dan kadan ba mai yawa ba iya hannayenta Ba ita ta bar saloon din nan ba sai da yama sosai kafin ta koma bangaren AMMI A cenma wanka ta shige cikin nutsuwa ta gama kimtsa jikinta cikin lalausan lesh ja mai adon baki a jikinsa kafin ta fito hannunta rike da dan mayafi ruwan baki sidik mai shara shara Ido kawai AMMI ta zuba mata, kalar fatar jikinta wani sheki take kara yi tamkar ta rihana, a yanzun sai ta kara budewa ko dan abinda suke zargin tana dauke da shi ne? Kiraye kirayen salar isha ya sakata daukan hijab din AMMI ta gabatar da sallar sannan ta zauna nan sunna dan taba hira Sai da karfe tara ta yi ne Ammi ta kuma kallonta a karro na ba adadi , muryarta sanyaye ta ce" NAJEEBA, tashi ki tafi mana " NAJEEBA ta dan yi murmushin, ita kanta ta kusan minti ashirin tana saka ta tashin to sai ta kasa tashin, dan haka ta mike Har ta fara tafia AMMI ta ce" Kar ki manta, k8 fada masa gobe in sha Allah zaki koma bangarenki kin ji? " Ita dai ta amsa ne kawai ama ba wai dan tana tunanin zata iya zaman wani bangarenta ba, ita kam me zata je yi cen ita daya kwal? Duda ta san tana kaura yan uwanta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191