Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 65

Chapter 65

Mage Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

kuwa ta bata maganin da zata sha dan rage rad'ad'in dake damunta na bak'on lamarin daya ziyarceta bayanshi bata samu wani mugun raunin da zai saka a kaita asibiti ko a mata d'inki ba, tana shiga ruwan zafi komai zai dawo normal sai dai abinda aka yaye din da ba za'a iya maido shi ba. Tawul ya d'auko ya mik'awa Ummu ya nuna mata bayi hakan ya ganar da ita abinda yake nufi. Wasu kayan ta d'aukar mata ta nufi bayin da su. Kamata tayi ta fitar da ita daga cikin ruwan dan har lokacin tana ta zubar da hawaye wani irin ciwo take ji a zuciyarta domin a rayuwarta idan akoy abinda ke tayar mata da hankali, ya sakata a firgici to fa irin abinnan ne. Kayan ta saka jikinta a mace suka fito tare. K'arasawa tayi ita ma ta zauna ta d'ora kanta gefen wuyan Ummu Muryarta a sanyaye ta ce" Ummu, kiyi magana mana, dan Allah ki ce wani abu mana." Suma hawayen suka ringa sharewa shi kuwa yana kallonsu. Sun d'auki kamar minti goma a haka kafin a hankali ta bud'a bakinta, hawaye ne wasu ke korar wasu cikin disashiyar muryarta ta furta" Dama me kuke jira da rayuwata? Kun manta wacece mahaifiyata? Yanzu haka idan kuka je tudun jamus layi na biyu babbar k'ofa mai ruwan blue gidanta ne, zaune take tana amsar kud'in wannan." "Ki yi min shiru!" Ya bud'a bakinsa tun d'azun ya fad'a da wata murya ta tsawa wace ta saka du suka rintse idannuwansu suka sada kawunansu Muryarsa ya kuma bud'awa yana cijewa yace" ku tashi baki d'ayanku mu fita!" Da sauri Najeeba ta d'ago tana kallonsa, sai dai ba damar yin magana domin har ya juya ya fara fita. Zahrau kam bata da katab'us, baki d'aya duniyar ce ta yi mata zafi ta rasa wani tunani zata yi da irin wannan lamari, aman tsawatarwar daya yiwa ummu ta sakata jin dama dama domin idan har haka zata ringa fad'i idan bakinta ya bud'e tana iya idasa halaka masu tunani su yi ta kuka. Kamata suka yi ta mik'e da k'yar tana rintse idannuwanta kafin ta sauko. Kamata suka yi a hankali tana tafiya suka fito domin basu san inda zai kaisu ba, su kuwa basu isa su k'i fitowar ba. Irin yanda suka ga duk mutane ne a zazaune kama daga Sarkin Agadez, na damagaram, Gimbiyoyin, yarima da matarsa sai du suka ji hankalinsu ya k'ara tashi. A hankali suka k'arasa da niyyar zaunar da ita a kasa, sarkin garin Agadez dake kallonsu ne kamar zai fashe da kuka shi kam ko rawanin babu a kansa yau an yi abinda ya cujewa buzu nad'i ya nuna masu doguwar kujerar dake ajiye." Nufar wajen suka yi suka zaunar da ita kafin su zauna kusa da ita sosai a jikinta. Najeeba irin kallon da take bin yarima da mahaifiyarsa da shi irin kallon nan ne wanda zaka ji kamar ka kashe mutun. Yayi d'agowar kansa ya fi a k'irga sai zai bud'i baki sai ya kasa hakan ya saka Gimbiya saurin zamowa kasa ta had'e hannayenta tana kallonsa muryarta na rawa ta furta" dan girman Allah a rufa mana asiri, kar ku manta yarima shine mai jiran gado, sirrinsa ya fita tamkar sirrin baki d'aya gidan nan ne zai fita, Allah ya huci zuciyarka a rufawa yarima asiri a gafarta masa." Tayi gaggawar juyar da kanta wajen SHAHEED ta d'an k'ara rarafawa hannayenta a had'e ta ci gaba da fadin" Ku rufa mana asiri, wannan sirri namu ne baki d'aya, dan girman Allah ku rufa mana asiri." Du wani motsin kowa yana hakimce ne yana bi da kallo, bai furta ko A ba. Kansa dake kasa ya dago, irin kukan da yake sai ya baiwa mutun tausayi. Da sauro ya rarrafa ya nufi wajenta hakan ya sa sarki sakar masa tsawar da ta saka bai idasa idasawa har inda take ba aman ya ja daga d'an nesa. Hannayensa ya had'e ya kara duk'awa sosai yana ta kuka kamar zai mutu yace" Dan girman Allah ki yafe min wannan lamari da na aikata maki, na rantse maki da Allah ni ba mazinaci bane na je d'akin iyalina ne ta fito ta bar min d'akin sai na biyo bayanta a tunanina inda kike tsaye itace a tsaye domin idannuwana sun rufe, satina biyu kennan tana guje min a shinfid'ata, zaki ga na rufe maki ido da bakinki ba dan komai ba sai dan sannin tana iya k'wala min ihu ta tara min jama'a ni kuwa na yi alk'awarin a daren sai ta bani hakk'ina, ban san cewa ba da ita nake mu'amala ba sai da na kai ga shiga wajen da ba nawa ba, wallahi wallahi ni ba mazinaci bane, sannan ba mai afkawa mutane bane, na kasance ina koyi da halayen nagartatun mutane dan na kasance nagartace, ban tab'a aikata zina ba ko a lokacin da bani da aure, dan girman Allah ki yafe min wannan b'arna da na aikatawa rayuwarki sannan na aikatawa rayuwata, ki maka ni kotu a yanke min hukunci daidai da laifina ko ki kaini kotun musulunci a yanke min hukuncin jifa domin ba zan iya rintsa ido da hak'inki irin haka a kaina ba." Mahaifiyarsa ce ta fashe da kuka mai tsanani. Da sauri ya juya ya k'arasa kusa da SHAHEED ya duk'a ya kama k'afafuwansa yana gunsheken kuka ya shiga fadin" Dan Allah yaya ka saka baki ta yafe min, ka saka baki ta gafarta min kar abin nan ya tab'a d'iyan d'iyana, ka ga wannan dake zaune zata iya maimaita abinda ya faru tsakanina da ita kafin ta baro d'akina, hakan yasa na biyota da sauri ban san inda ta lab'e min ba na fito da gudu ina nemanta sannan itama wando ne a jikinta da rigar baci na rufe bakinta da hanuna da idanuwanta dan kar ta min ihu ko ta fad'a min abinda zai fitar min da son zuwa gareta a raina hakan ya sa na afka mata, ba zan iya fahimtar ba da matata nake ciki ba, hankalina ya gama tafia burina na samu nutsuwa." Gannin ya k'ura masa firgitatun idanuwan nan nasa masu matuk'ar abin tsoro ya saka shi sakinsa ya juya wajen mahaifinsa ya karasa ya kama k'afarsa. Kafin ya fara magana ya hamb'are shi da k'afar tasa hakan yasa ya fad'i gefe aman bai gaza ba ya kuma tashi ya kara ruk'unk'ume k'afar tasa yana wani irin kuka murya a cakule ya furta"BABA." Sarki ya saka k'afarsa yana kiciniyar kuma hamb'are shi aman ya gaza dan baki d'aya jikinsa yayi sanyi lamarin ya shige shi a lokacin da bai shiryawa hakan ba. Muryarsa ya bud'a a birkice ya furta" Inna lillahi wa'ina ilaihi raj'une." Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une! Sai kawai muryarsa ta shiga rawa sai kuka ya k'wace masa, hakan ya saka SHAHEED saurin rintse idanuwansa ya sadda kansa. Muryarsa na rawa ya shiga furta" Lalle kana wasa da adininka, kana wasa da ibadunka, idan kuwa ba haka ba kaima k'addararka mai tsauri ce domin kamar yanda ka fad'a saina hukuntaka! Wani irin rayuwar aure kake da macen dake gudunka har cutuwa ta shiga tsakaninku haka mai tsanani mugun raini ya shiga tsakaninku har ya kaika ga neman afka mata

Table of Contents

Chapters

191 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191