Chapter 86
Chapter 86
Tana shigowa Anmy ta fara ganninta hakan ya saka ta mike da sauri tana fadin" NAJEEBA, daga ina kike? Waye ya daga wayana yake ce min na shafa maki lafia na bar kiran ki? Ina wayarki take? Me ya same ki? Dayabu ya juyi da sauri yana kallon yanda ta yi wani irin turus sannan kukan da take ga kuma irin yanda jikinta ke bari gabansa ne ya fadi hakan ya saka da wani irin sauri ya karaso ya kamo hannayenta ya yi ciki da ita Sai da suka shige daki ya zaunar da ita har jikinsa na rawa ya ce" daga ina kike? Kukan me kike? Anmy da ta biyo bayansu ji take kafafuwanta sai bati suke kamar zasu rabu da gangar jikinta dan tsoro da fargaba A kidime ta karasa shigowa tana fadin" wani ya maki wani abu? Wani abu ya same ki? Fashewa ta yi da kuka tana zumburo bakinta ta ce" Anmy, wayata ce ta bata Ba anmy ba, shi kansa sai da ya ji ya sauke ajiyar zuciya duda ba wani yarda ya yi da maganarta ba Abih ne ya shigo ya zauna bakin gadon yana kallonta A sanyaye ya dubi Anmy ya ce" Bilkissu, mu je Anmy sai da ta kamo hannun Najeeba ta rike tana kallonta a sanyaye ta ce" wannan shine alfarma ta fari da zan nema a wajenki nurul khalb Najeeba ta kurawa fuskar Anmy ido aman ta kasa tambayar menene har suka fita Sunna fita Anmy ta ringa sintiri ta kasa zama, dama sun yanke sai dai Dayabu ya tarbeta da maganar dan shi kawai zai iya fatatakarta kuma ta saurareshi Cikin daki Na san karya kike da maganar dan an sace wayarki kike kuka, ki fada min abinda ya saka ki kuka tun raina bai baci ba DAYABU ya fada yana kuma mai jin tsoron abinda zata ce ya sakata yin kukan Sai da ta rintse idannuwanta wasu hawayen suka kara zubowa daga gurbin idannuwanta, cike da jin kunyar abinda zata fada ta shiga kwatanta masa abinda ta aikata wanda ta tabata sai ya babala mata mari aman kuma da ta rike ita daya ta yi ta jin haushi gwara ta fada masa ya wanwanka mata mari ko zai huce Da mamaki yake kallonta kafin ya girgiza kansa a sanyaye ya ce " Najeeba, kin san irin darajar da Allah ya yi maki har kike aikata halaya irin na wasu sakakun mata? Najeeba kin kuwa san irin daukakar da Allah ya maki har zaki je ki zubda kanki haka? Najeeba kin kuwa san irin matsayin da Allah ya maki har zaki yarda wani sakarai ya rungumi jikin ki? Yaya aka yi kika kasance mai saurin sakarwa maza fuska bayan ke din kadara ce da ta fi lu'u lu'u daraja? Najeeba nan da kwana goma idan Allah ya yarda za'a zafa fatiyar daurin aurenki da mutun mafi daraja da mutunci, mai girman mulkin da Allah ya nada tun a kannanun shekaru, mai zamani mai takawa da Alfarmar Annabi, mai watsa taron yan daba mai rikita taron tsageru, Najeeba zaki kasance daya daga cikin mata masu girman daraja wa'inda idan sun zo ficewa ake sada kai ba'a hada ido da su tsabar yanda Allah ya daukaka su ya darajanta su ya fitar da tarmamuwarsu ko da rana take kyali? Najeeba zaki kasance hakima, gimbiya, wace zata zama daya daga cikin wa'inda ko sarakai na jinjina mata kasancewarta matar daya kwalin kwal din sarkin da ya kafa tarihi, Najeeba yaya zaki yarda ki je wani sakaran da ko baran gidan nan ya fi shi mukami a damagaram ya kai hannunsa jikin ki? *NAJEEBA, ZAKI KASANCE DAYA DAGA CIKIN MATAN MAI DAMAGARAM NAN DA KWANA GOMA KACAL* kike faman saka mu a uku? Tun daga wannan kalmar kunnayenta suka dode ta daina fahimtar abinda yake fada har sai da ya dasa aya ya ga ta kurawa bakinsa ido kamar wace ta suma a zaune Hannunsa ya kai wajen kuncinta dan gannin yana furya sunnanta a sanyaye ta kasa amsa shi ya shiga dan taping a hankali ta ce" Najeeba kina ji na kuwa? Sai a lokacin ta yi wani firgigita ta farka daga summan zaunen da ta yi kafin ta kurawa fuskarsa ido a karo na biyu Wani irin hantsilowa ta yi daga saman bed din ta fadi kasa har tana take doguwar rigar dake jikinta ta kuma dagowa Hannayenta duka biyu ta dora saman kanta kafin ta takarkare ta kwala wani firgitacen ihun da ya saka Dayabu saurin kai hannayensa wajen kunnensa ya dode lokaci daya kuma yana nufarta dan rufe bakinta daga wannan ihu da ta saka daya kwal ta ja shi da wani irin jan da ake yi kamar wace ke kiran sallah... Happy juma'at jama'atul musulmi😲🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *MAGE* _(Mai kwanciyar d'aukar rai)_ 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻 *Na* *SAJIDA* 💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟 _(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝 ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/ _Bismillahir rahamanir rahim_ 34 Hannayensa dode da kunnayensa ya diro ya karasa inda take ihun nan Yana zuwa ya saki kunnensa ya damke bakinta da hannunsa sannan ya saka dayan hannun nasa ya riketa da kyau Sikewa ta yi, lokaci daya numfashinta ya dauke ta tafi luuu a jikinsa Ido ya zaro cike da tsoro da mamakin suma ta yi? Lalle ya dauki abin da wasa ashe har ya kai cen? Jikinsa na bari ya samu ya kaita saman gadon ya shinfideta sannan ya mike ya karasa wajen kofar dakin A hankali ya bude hakan ya saka Anmy saurin juyowa a lokacin da Abih ya rike hannayenta yana lalabata cewar kar ta shiga ta bari har su fito Ummu da Ummulkhair dake tsaye jikin kofar ne suka kutsa kawunansu cikin dakin hakan ya saka ya basu damar shiga sannan ya maida kofar da sauri ya datse dan ya ga Anmy ta zaburo ta nufo wajen Dakatawa ta yi kusa da kofar hankalinta tashe ta kalli Abih, a sanyaye ta ce" me ya sa ya hana min shiga? Baka jin shirun ya yi yawa ko wani abu ne ya sameta? Abih ya kara kamo hannunta suka koma falo suka zauna, a sanyaye ya ce" mu yi jira, idan yana irin wannan hali da kannensa nakan basu dama, idan na saki mace na dauko wata haka muke shiga da su du su rikice, shi ke rufe kofa daga shi sai su, ban san ta yanda yake lalaba su ba, in sha Allahu zai lalabata (Ya Allah, du wani yaya da ya dauki girma ya kasancewa kannensa tamkar bango, wajen da suke kai kukansu ya share masu, wajen da sun san uba ne a gare su, Allah ka dafa masa, ka masa albarka, ka kare shi, Yayana JAMILU Allah ya kara daukaka baban yaya👏👏👏) ........................................ Cike da tashin hankali Ummulkhair ta yi kanta, ita kuwa Ummukulsum ta yi bayi da gudu dan dibo ruwa A rikice Ummulkhair ta ce" yaya, summa fa ta yi? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une daga fada mata ta summa yaya zamu yi da ita ta nutsu? DAYABU ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Ummulkhair, kar ki yi kuka, kar mu saki ta ga rauni a tatare da mu idan ba haka ba na rantse zata botsare mana ne ya kasance mu dake son tirsasata ta amince da maganar nan mu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191