Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 82

Chapter 82

Mage Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

yin zaman kishin Dayabu ya yi murmushi ya ce" Abih, ka manta Ummu, sun yi zama da maman Bilkisuu fa Sai da ya lumshe idannuwansa a lokacin da ya ji sunnan *UMMU* mahaifiya a wajen NAJEEBA, shi yakan kirata da UMMU, sauran kuwa sukan ce mata mama Murmushi kawai ya yi yana tuna lokacin, zamanin nan ya kasance tamkar wani zaburaran doki a tsakanin matan nan biyu Ya ga rayuwa ya yarda cewa mata sunna suka tara Murmushi ya yi a kasan zuciyarsa kuwa fadi yake" me ya yi zafi haka da aka guje ni an matana? Na kai zuciyar cikin duhun da ta kasa yafe min? ............................................. Ba yanda bata yi da dogaran dake tsaron kofar bangaren ZINARIA kan su barta ta shiga tana da sako wajenta mai mahinmanci, sai dai sam suka ki amoncewa domin ita da kanta ne ta nuna ba zata karbeta ba tana hutawa Haka dole ta samu ta kwana gefen fulani domin idan dare ya yi haka ba mai fita daga fada sai da kwakwaran dalili ............................................. Sam bata samu ta rintsa ba, sakamakon maganar yar uwarta cewar ta saka Anmy a cikin bacin rai Idan ta juyo daga kan gadonta ta hange su sai ta ji uwa ta je ta cicije su ko zata huce, sai kawai ta ji baki daya kewar yayarta ya hana ta rintsawa domin ta tabata da ita ce da ba zata taba yi mata fushi haka ba Suma bangarensu sun matukar yi kokarin gannin sun watsar da fushinta gefe, domin idan har suka biya tabas zata saka su a damuwar da zasu kwana sunna kuka ita kuwa da safe ta warware ta yi tafiyarta! Kiran salar fari a kunnayenta ya sauka Dira ta yi daga gadon ta yi bayi ta dauro alwalah Sai da ta zo ta saka doguwar riga saman ta bacinta sanann ta yane kanta ta shiga gabatar da sallah Tana nan zaune har aka kira sallar asuba ta kuma gabatar da ita cikin nutsuwa ta shafa fatiha da sauri ta mike ta yi bangaren Anmy bata kula yayun nata ba Tana zuwa ta shige da salama kasa kasa kafin ta karasa da dan saurinta wanda ita ganni take sauri ne take yi ta duka gaban Anmy wace ta gama sallah tana jan carbi Kanta a kasa tana jin hawaye na son zubo mata ta kamo hannayenta ta dora a gefen fuskarta a sanyaye ta ce" Anmyna, wai da gaske na bata maki rai wai har kin kwana baki yi baci ba? Anmy dake jin kaunar yar a ranta ta ce" in ji wa? Najeeba ta ce" ba aunty Ummu bace ta fada? Dan murmushi Anmy ta yi jin ta ce da ita auntu Ummu, yau ummun ce auntyn, Kanta ta dan girgiza tana murmushi ta ce" aa, ma baby girl ba zata bata min ran da zan riketa haka a zuciyata ba, Me ya samu idannuwanki suka kunkumbure haka? Murmushi ta yi ta ce" ban yi baci bane Anmy Anmy ta kara shafa gefen fuskarta a sanyaye ta ce" tashi ki je ki kwonta cen ki huta maza Mikewa Najeeba ta yi tana jin hankalinta ya dan fara kwonci dan yannayin da Anmy ta nuna mata ta tabata an bar maganarta Doguwar rigar ta cire ya mata sauran wata yar rigar baci baka wace bata idasa rufe cinyoyinta ba sannan daga saman mai gidan mama ne wada ake kira rabin nono ya kasance saman a bultse suke rabin ne suka rufe Ba abinda ya shafeta dan ta san ba mai shigowa bangaren Anmynta, kuma gaban Anmy kuwa zir ne kawai bata yi Hayewa ta yi saman lafiyayen bed din Anmy mai sansanyen kamshin turaranta ta yi kwonciyarta tare da rungume yar kanwarta dake ta baci ......................................... Kamar yanda ya saba da duhu duhu yake shiga dan gaisheta Hakan ne ya faru, a lokacin da ya daga labulen dakinta ya sanyo kansa Idannuwa masu neman fitina suka sauka a kan fitsarariyar yarinyar nan wace ya yi mata kallon shari'a daya tak ya yi gagawar cire idannuwansa yana jin wani nishi na kwace masa kamar mai cutar athsma Da sauri ya saki ya juya ba tare da ya shigan ba, domin gani yake sam bai dace ya shiga a irin wannan lamarin da mace ke kwonce da irin wannan shigar bayan ba muharamarsa bace! A wannan rana Najeeba bata fita saloon ba, sai da aka yi salar magariba ta fito cikin shirin abayarta lurub har kasa ta cewa Anmy zata dan leka ta dawo a tsaitsaye Da adu'a ta bita tana mai yin dan murmushi Irin yanda yarinyar ta fi sauran yan uwanta kulawa da ita ya saka take mata so daya tak da babu irinsa Kwana bakwai dai suka dauka zasu sake zama su dukansu tana adu'ar Allah ya yi zabi na alkhairi Tun da ta zauna a wajen yau ya fahimci halin da take ciki Shima zaunen da yake hotunnan tsala tsalan yan matan da aka turo masa ne yake bibiya yana son gannin wace zata iya da shi? Kuma dago shanyayun, lumsasun, idannuwansa masu shige da na mashaya da kuma dauke da kwali ya yi ya kai dubansa a kanta a karo na bakwai Haushinta yake ji sosai, ta zo ta wani zauna masa a wajen da ya rigayeta kamawa a nan yake zama, bayan yana cike da haushinta na har wani ta ja mahaifiyarsa na hada sunnansa da nata, yo shi Allah ya tuba idan aka ce za'a aura masa wannan yarinyar a ranar zai cire rigar sarautar ya je da gudu ya tari katuwar mota ta murje shi da ya ga takaici! Me zai yi da masifafiya, yar balaki, balagazar mace? Ai shi auren nan da zai yi na hutu ne ba na jazawa kai balaki bane! Sai da ya dani zuciyarsa kafin a sanyaye ya furta" *wa ya taba ki? Sai nake ga hankalinki tamkar ba a kwonce ba, hakan kuwa kwata kwata ya dauke min nutsuwata* Dagowa ta yi tana kallonsa, yauma da alama ya yi gudu ne dan da kayan gudun a jikinsa sai mahaukacin basket din takalmin dake kafarsa wanda yannayinsa zai tsadanta maka tsadarsa A hankali ta cire kanta ta dan daga kanta tana kallon taurarin wajen Muryarta a sanyaye itama ta furta" *ina cikin tsaka mai wuya ne, ashe haka zaman juran amsa yake? Ina cikin gararin rayuwar da kila wa kala ne idan har zan kai labari, domin kuwa da na yarda da abinda zai iya kasancewa da ni gwara a ce bana duniyar!* Da matsanancin mamaki yake kallonta, aurensa ne take fadin da ya kasance a kanta gwara ta rasa ranta? Ita din wacece da har take tunanin tana da girman matsayin da shi zai yarda ta amsa sunnan matarsa? Ashe aurensa zai iya kuntata mata rayuwa har haka? Tabas da ace zai iya da ya je da kansa ya roki a aura masa ita ko dan ya ringa kallon yanda zata yi har ta mutun Sai dai ina, irin yanda yake jin kyankyaminta ba zai iya wannan kasadar ba Sai da ya dan cije lebenta na kasa kafin ya furta" me ya yi zafi haka NAJEEBA? wani irin abu ne wannan dake damunki mai tsanani? Ki fada min ni zan yi maki maganinsa

Table of Contents

Chapters

191 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191