Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 15

Chapter 15

Mage Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

idan ya tashi dukan yaro yakan yi masa duka kamar zai kashe shi Mahaifinsu baya duka a banza, aman du randa hannunsa ya daga sai ya daka Da wani irin tsinanen gudu DAYABU ya warci kananun biyu ya fada dakin NAJEEBA wace ta rigayi kowa guduwa Yana shigowa suka dantse kofar wanda hakan ya saka uban nasu dukan kofar ransa bace yana jijigawa Ransa a matukar bace ya ce" bude min, marar kunyar banza marar kunyar wofi, bude min ki fada min maganar banza a gabana Ummu ni ne zaki yiwa fatan na maku aure a sako ku? Kennan ni jarabawar sake saken mata ba zata iya samuna ba ko? Zahrau shine kika zagar masa uwa kika ce masa shege? DAYABU shine ka saka su gaba sunna munanan kalamai a kaina ba zaka tataka su ba? Khairy shine kina ji ta zagar maki uba baki mareta ba? Najeeba me ya hada ki fada da dan gidan docter Basheer? Hannunsa ya saka ya kara dukan kofar NAJEEBA wace ita ta fi kusa da shi kafin ya zame ya zauna a jikin kofar yana sauke ajiyar zuciya Dawowarsa kennan ya tarar da wanda ke neman auren Zahra da mahaifiyarsa da kawayanta biyu a kofa sunna jiransa mai gadi ya hanna su shigowa sai kunfar baki suke wai sai ta fada masu a inda ta ga ta yi shegu Dama tun a hanya inda ya tsaya siyan fruits ya tsinci maganar fadan NAJEEBA harma ta summa Daga cen ya nufi asibiti aka shaida masa yayanta ya daukota an sake su Shine ya shigi ya tarar da Ummu na fadin irin wadinnan magangannun wai koda sun yi aure za'a sako su ne da ciki ko daga sun haihu a sake su Idannuwansa ya lumshe ya yi shiru yana tunanin rayuwa A jiya ya so kwarai ya saki Mardiya, sai dai gannin yanzu y'ayan nasa kansu sun fara fada masa magana a kan auri sakinsa ya saka shi kyaleta domin ba'a taba masa y'aya a wanye lafia Idannuwansa ya kuma lumshewa yana tunanin inda zai bi ya yiwa tufkar hanci, ya zama wajibi ya katse hanzarinta, ya zama wajibi ya yiwa tufkar nan hanci idan kuwa ba haka ba lale watarana y'ayan nasa zasu yi abinda zasu zubar da hawayen jinni, zasu ja sirrin da yake binnewa ya fito fili Zasu saka baki daya su tatara su bar kasar a lokacin da suka zama abin kyamata sannan abin gori a cikin kasar nan A hankali ya ce" ku fito Du sun ji shi, aman ba wanda ya yi yinkurin fitowa Ajiyar zuciya ya kuma saukewa ya ce" ku fito, ba zan daki kowa ba Zahrau ta fashe da kuka ta ce" ABIH, dan Allah ka yi hakuri Muryarsa ya dan daga ya ce" magana nake so mu yi ku fito na fada maku ba zan daki kowa ba Shiru suka kuma yi, wanda hakan ya saka shi sada kansa yana jin zuciyarsa ba dadi Sam baya jin dadi a kasan zuciyarsa Karar bude kofar da yake jingine ya saka shi sauri dagowa harma ya mike tsaye ya juyo yana son gannin wanda ya iya fitowa A hankali ta fito tana matsowa kusa da shi hankalinta a kan fuskarsa Shima idannuwansa ya sauke a nata fuskar Lokaci daya ya ji wata kauna irin ta da da uba na mamaye zuciyarsa A hankali ta daga kanta tana kallon fuskar nasa, idannuwanta da ta gama sannin sunna da effet a kan mahaifin nata koda ya tashi duka sunna saka shi dakawata ta kara masu girma sosai sannan ta yi masu kwal kwal Nan da nan kwallah ta cika su, bakinta take son budawa aman ta kasa A hankali ta shiga kokarin riko hannayensa muryarta na rawa tana son fitar da lafazi ta kasa, sannan hannayen nasama ta kasa rikowa dan sai take gannin sun mata nisa sosai Idannuwansa ya rintse sakamakon jin wani irin tausayinta ya gama halaka bacin ran nasa Tsantsar kaunar y'ayansa yana matukar yin tasiri a rayuwarsa Ko dan sun kasance mata da yawa wa'inda ya dauki son duniya ya dora masu? A hankali ya kama habarta ya dan dago yana kallon kwayar idannuwanta Muryarsa ya sanyaya ya ce" kuka zaki yi? Jin ya sauko hawayenta suka samu damar zubowa tana kallonsa sai a lokacin kuma bakinta ya bude cikin sanyin murya sosai ta ce" kar ka dake mu Abih, ka ga an summar da ni bayan bani da laifi, ka ga ya zazageta dan kawai an fada masa abubuwa Abih ina zamu shiga mu ji sanyi ne? Da sauri ya kama hannayenta ya karasa kusan dakinta sosai Muryarsa ya dan daga ya ce" ku zo gare ni, ku zo kun ji? Jin irin yanda muryarsa ta sanyaya ya saka du suke budewa sunna fitowa Du kusa da shi sosai suka zo suka zazauna wasun su har sunna dora hannunsu saman jikinsa Murmushi ya yi yana kallon ZAHRA ya ce" Zahra, daga yau kar ki kuma zagin mutun da nasabarsa, ko dukiya, koma menene kin ji? Na gwamace ace da ni gaki cen kun daku da mutun na je na raba da ki yi irin wannan abin, kin san me ya sa? Kanta ta girgiza tana kallonsa, hakama sauran Hannayenta ya riko ya ce" abinda ya sa shi mutun ba'a gama halitarsa, baya fasa gannin jarabawar rayuwa har sai ranar da aka saka shi cikin kabarinsa Eh lale yin fari ne kadara, na biyu ganganci na uku kuwa da gangan Aman koda y'aya goma ta haifa na hane ki yi mata gorin hakan domin ko ke kin tsufa zaki bar baya kin ji? Kanta ta ringa gyadawa Ya maida dubansa wajen Ummu ya yi murmushi ya ce" haba Umana, idan inada mumunan hali ai bana tunanin zaki kulaceni haka, na fi tunanin zaki min adu'a sannan ki yi fatan kar Allah ya jarabeni da ku, wato ya dora hakan a kanku dan na rantse maki ban san wani hali zan shiga ba, ki ringa kyakyawan fata kin ji? Kanta ta ringa gyadawa itama tana share hawayen fuskarta Hannun NAJJEBA dake cikin nasa ya kara rikewa yana kallonta, murmushi ya yi ya ce" ni ko dai kece jinnin abuna ba ni ba? Yaya aka yi da wahala safia ta yi dare ya yi baki yi fada ba? Allah ya shirye ki Kanta ta kifa saman cinyarsa Ya kai dubansa wajen DAYABU dake tsaye da NAJEEB a hannunsa wanda ya ki yarda ya sauka daga hannun nasa tun da ya tsorata kar aban nasu ya dake shi Murmushi ya masa mai tsayawa a rai kafin yana kallonsa ya ce" wa ya ce maku baku da wajen da zaku je ku ji sanyi? Kunada wajen da zaku je ku ji sanyi sosaima Ina raye, a doron kasa ai zan kasance maku katifar da zaku zo ku kwonta Tunda shi ya fasa aurenta, dama yana neman hanyar silibe mata ne, da izinin Allah, Allah zai fitar maki da miji na gari Murmushi DAYABU ya yi gannin du sun dodora kansu jikin Aban nasu Dan haka ya karasa da najeeb a hannunsa ya ringa dauko ledojin dake dauke da burger din yana kawowa yana ajiyewa Nan fa suka baje abincin, inda mahaifinsu ya fita ya je ya dauko yar karamar

Table of Contents

Chapters

191 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191