Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 44

Chapter 44

Mage Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

junna Maganar da jakadiya ta duka tana fadi ne cewar matar Abih na neman iso ya saka Gimbiya kallonta da kallo irin na son ta maimaita Kara sada kanta ta yi ta maimaita maganar Dago kanta gimbiya ta yi daga kallon Jakadiyar ta sauke saman yaran Ta dan jima kamar second talatin tana kallonsu sannan ta cire kanta a kansu ta gyadawa Jakadiya kai Mikewa Jakadiya ta yi ta juya, dan ta gane amsar cewa eh aman ba yanzu yanzu ba Cike da kauna Gimbiya ta kalli yaran ta dan gyara muryarta ta ce" kunna ji? Du dubanta suka juyo yi Gimbiya ta yi masu murmushi ta ce" bana so a raba hali Du sun fahimci inda ta nufa aman dan ta tabatar cewa sun fahimtar sai ta masu shiru daga haka itama ta ci gaba da dan daukan kambolin farar tana dan ci har tana mamakin kanta yanda aka yi take cinsa da yawa haka ko dan tare da mutane ne An dauki kamar minti goma zuwa lokacin Har Gimbiya ta wanke hannunta, yaranma kananun ne basu gama cinye fararsu ba Da salama suka shigo falon Masu yi masu jagora ke amsawa da karfi karfi sunna fadin" ku shigo a hankali, Gimbiya na falo Ku sada kanku kasa ku gaishe da mace daya tamkar da goma mama a wajen sarkin damagaram Ku tako sannu sannu Bakinta ta dan tabe tare da yayarta suke wace ke biye da jakadiyar dan aiwatar da abinda ake nuna masu Sunna zuwa du suka nemi zama a kujera Sai dai basu kai ga karasa nufinsu ba da sauri Jakadiya ta tare tana nuna masu wajen da ya dace su zauna domin idan ka ga Gimbiya na sama wani na sama toh sarki ne, sai y'ayanta dake hayewa jikinta su dora kansu a saman kafarta, su kansu idan ka ga sun layi da ita to a saman diner ne Ko yanzu Zahrau ce kwonce kanta saman cinyarta ita kuwa tana shafa mata gashin kanta Daga kasa kuwa Najeeba ce ke gyara mata akaifunta tana ta kankare mata su tana yanke mata duda ba wani datin dake jikinsu aman ta saba idan tana zaune ko ta dora rigimar sai ta yi mata kitso, ko ta kama gyare gyaren mata su akaifu ne da sauransu Komawa suka yi wajen suka zauna domin wajenma waje ne mai alfarma dan ba kasa ne dabas ba aman duda haka ita ta so ta hau kan kujera dan a ganninta ai ita matar yayanta ce Yayarta ta fara mika gaisuwa, kafin itama ta buda bakinta cike da yatsina ta ce" Fatan kun wuni lafia, yaya aka ji da hakuri? Gimbiya ta dan dauki lokaci kafin ta lumshe idannuwanta, hakan ya sa Jakadiya fadin" Alhamdulilah, Gimbiya ta amsa Hakuri an gode Allah Da kallo ta bi Jakadiyar sannan ta sauke kan Gimbiya Sai ta ji shakarta ta shigeta domin irin kamalar dake tatare da fuskar gimbiya ba zaka iya takata kai tsate ba komai rashin kunyarka dan ba lalenema ka ji muryarta ba idan ba hakan ta so ba Idannuwanta ta dago ta sauke a fuskar Zahrau wace ke iya gannin hakan Dan mukewa Zahraun ta yi tana gyara gashin kanta ta bi kannenta da kallo baki dayansu, kallon nan da ake kallonka kuma a kalli mutun Du yawanci sai da suka dan turo baki kafin a hankali da daidaya suka shiga gaisheta, gaisuwa kamar haka" barka da yamaci, fatan kun zo lafia? Bakinta ta tabe tana dan jijiga yarta dake bayanta wace ke ta ihun a sauketa tun da ta ga yan uwanta aman uwar ta ki kunceta dan haka sai take kukanta irin kannanun kukan nan Basu wani jima sosai ba, ko gaisuwar yaran ba yanda ya dace ta amsa ba yayarta dai ce ke amsawa kafin su mike su juya su fita Sauri sauri take har suka karasa fita waje sannan suka shiga cikin motarta da suka zo da ita Sai da ta kama hanyar gidan iyayenta dan cen suka nufa tana ta jan wani uban tsaki Ita dai yayarta tana ta jijiga yar da ta ki yin shiru tana kiran sunnan yayanta dan saurayin Sunna karasawa suka sauka suka shiga ciki Mamansu dake shanya hijab din yar yarinyarta ce ta dago tana dubansu ta ce" aa, me ya samu kishiyar ne haka take wantsala kuka tun daga waje? Yayar Mardiya ta mikawa mamansu yarinyar ta zauna tana dan tabe bakinta ta ce" mama, anya kuwa Mardiya ba tana hada mu da y'ayan mijinta da kanwar mijinta dan ta kasance mai son kanta bane? Da sauri Mardiya ta dubeta ta ce" wani irin ina hadaku da su? Hararanta ta yi ta ce" kwarai kin ji abinda na fada! Mardiya du irin rashin mutuncin dake tsakaninki da yaren nan sai na ga da sauki tunda har zasu budi bakinsu su gaishe ki, sannan ke maimakun ki yi masu amsa irin ta uwa ko dan idannuwan mamansu sai kike wani binsu da harara Ke dai kece mai neman fitinar a bayane domin ni dai ba fada min aka yi ba ni na raka ki Mardiya ta zaburowa Nusaiba tana fadin" zaki min shiru ko sai na ci uwarki a nan yarinyar nan? Yar ta yi shiru tana kwontar da kanta saman kirjin kakarta ta kai dubanta wajen yayarta da yannayin fada ta ce" malama kar ki wani fada min haka dan ke baki san abinda nake ciki ba! Yanzu dai a gabanki zuwa muka yi zamu hau kujera aka hanna mu aka nuna mana kasa muka zauna Sannan kina ganni mu muka buda baki muka fara gaisheta bayan mune ya dace ta gaisar! Da kike maganar yaran ba sai da ta harari katuwar guzumar ba sannan suka gaishe mu ba? Itama idannuwan ta ruko mata ta ce" kin fa san bana tauye gaskiya ko a gaban waye, ba zan boye gaskiya dan kina kanwata ba Me kike so? Ki hau kujera ki layu da Gimbiyar Damagaram? Uwar sarki ce fa Mardiya baki da hankali ne? Ke ki kasance da ita a waje dayama ai arzikin arziki kika ci! Kuma maganar kujera ba a kasa aka sauke mu ba, na lura wajen saukewar an dora mu mafi karamci ne a cikin waje uku ne Da kike maganar sai da ta harari yara sannan suka gaishe ki inaga ashema da tarbiyarsu yaran dan har an isa a sakasu ko a hanna su duda kuna cikin haki na gaba da tsanar junna? Ke ki rufawa kanki asiri ke kin san cewa Allah ya baki dama, na rantse da Allah da ace kin sada kanki da matar nan da na tabata kun samu kusanci da fahimtar junna yanda ya dace, da ke ya dace a je a yiwa gaisuwar nan ba wai na tirsasaki na kaiki mu yi dan zama mu tashi ba Haba Mardiya, ke kin san waye mijinki, igiyar aure daya ta tsinke tsakaninku, ke kin san kafin ki shiga gidansa da manufarki ta yin hakan, kin shiga gidansa ne dan ki rama kwace maki saurayi da y'arsa ta yi, kin shiga ne dan ki muzanta rayuwarta ki hanna mata zaman lafia da kwonciyar hankali Baki shiga dan ki haihu ba Baki shiga dan ki jima da shi ba, Da biye biyen abokansa

Table of Contents

Chapters

191 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191