Chapter 77
Chapter 77
da dan dogon wuya sai fuskarta mai dauke da saje sakamakon tarin gashin da Allah ya basu na mahaifinsu da ya kasance shuwa arab Gashin kanta baki ne sidik har gaban goshinta hakan yake haska copy choko color din fatarta mai santsi da kyalkyali, Gashin girarta tamkar ta SHAHEED take sai dai ita tana daidaita tata tana gyarata koda yaushe daidai da tsarin da take so a fuskarta Tana dauke da dara daran idannuwa masu tsaga tamkar na damisa, sunna dauke da gashin ido masu yawa da tsayi wa'inda ko a haka wasu na tambayarta idan ta yi kari ne? Hancinta kuwa dan daidai mitsali ne, bata da karan hanci mai tsayin nan aman kuma ba a duke hancin yake ba, dan karami ne daidai da fuskarta Lebunanta sun kasance na kasan ya fi na saman girma da kadan, sannan na kasan tamkar wanda akai masa yannayi na heart domin daga tsakiya ya fitar da yannayin nan gashi idan ta yi niyar shagwaba sai ta kara nitsar da shi sai kawai ka ji ka afka a shaukinsa da son cinye shi Lebunanta sunna da dan duhu kadan, na kasan ne yake da dan hasken pink sakamakon irin yanda take bashi kulawa ta hanyar saka brosh dinta tana dan gurza shi a hankali a hankali har sai ya fara zafi zafi sannan ta wanke ta kawo hadin zuma da lemun tsami da man haba dinta da take hadawa ta dan shafa kadan sai ta kwonta, sai ta wanke da asusuba sannan ta kawo maganin bushewar lebe da saka lebe ya yi wacila wacila wato *Sabarob* ta shafa kadan kafin take tafia wajen aikinta ta wanke hakan ya saka yannayin lebenta ya zama wani unik saman ya dan fi na kasan duhu na kasan ya zama mai ruwan pink shi ba orange ba, sannan suke da wani irin laushi da santsi wanda ko da ido idan ka kala zai tafi da kai ne Daga kasan lebenta gefen hagu kadan, wani dan kurji ne dan karami mai haske irin wanda ake cewa na masasara ne ya fitowa mutun, to ita dai ya fito mata tun tana karamarta kuma bai bace ba, wannan dan kurjin sai ya zama wani cikon sirrin kyan fuskarta, dan tamkar ta yi yar huda ne ta saka abu mai kyalkyali a wajen, har akan tambayeta yanda ta yi ta fitar da shi a kusan lebenta domin idan ta tashi sangartarta takan yi rawa rawa da lebenta sannan ta dan cije wajen kurjin nan idan ta sake shi sai ya kara haske da walwali kafin ta yi wani irin farrrr da idannuwanta Dafe daidai zuciyarsa ya yi da hannunsa na dama yana kallonta a sanyaye ya ce" me kike so na malaka maki? Me kike so na baki? Ki kama daga kaina har dukiyata duka naki ne Najeeba, ki bani kulawar da nake bukata na roke ki Najeeba ta dan yamutsa goshinta kadan kafin ta dan fitar da harshenta ta dan lashi lebenta na kasa as usual, a hankali ta ce" me ya sa kake tunanin dan ka malaka min wani abin zan iya yarda da soyayarka? Ka zo da shirin baje min haja ne Elhaj? Gyara zamansa ya yi yana kallonta ya ce" da haja, da ni mai hajar, baki daya nake son baje maki ki taka ki yi abinda kike so da su Najeeba, ni dai burina ki wanke ni son ranki aman ki aureni kwana kusa dan ina mai tabatar maki a matse nake da ke Idannuwanta ta dan rintse dan jin kunyar wai a matse yake din da ya fada, kafin kuma ta bude tana dan kaucewa kallonsa Hannunta ta saka daga sama wajen rigarta ta janyo chek din da ya bata a saloon shi kuwa yana kallonta, ba kalacin shi ba, harta wanda ke jiran su fara ya samu huja a kusa na kallonsu ta miko masa gefen damtsen hannunsa A hankali ta dan ragewa idannuwanta girma ta ce" shi ya sa ka fara marina da yayan banki? Kafin ya bata amsa ta kara rage tsayinta, Kanta ta waiwaya cikin dabara ta kurawa wajen dake dauke da abin camerar dake nuna cewar ta nan ake iya ganninta Shima idannuwansa ya kura a kan nata tamkar sunna kallon junna da mugun kallo, Cire kanta ta yi a wajen ta ja tsaki a ranta tana furta, wani irin hira ne zan yi da mutun bayan mai yiwuwa matarsa marar mutunci na kallon mu? Ko kuwa cikin barorinsa? Ko kuwa kawayenta yan iska da suke jirana su gane min miji ko me? Gaskiya da sake Haka kawai sai ta sauko itama ya kasance sunna zaune ne a saman cafet din zama irin na kusa da kusa kadan kafin ta rage muryarta sosai ta ce" ban san yaya aka yi ba daga nan da kwana uku lamarin wankar maza ya fara fice min a rai Ka san wani abu? Kansa ya girgiza yana kallonta, ta ci gaba da fadin" na fi kwarewa wajen wankar aljihunnan mazan da suka ajiye mataye a gida suka zo suke bin mu, sukan bude bakin aljihunsu su kashe mana kudaden da a shekara ba zasu iya anfanar iyalansu da su ba, Ina matukar jin dadin karbar kudin wanda matarsa ta tarbe ni ta zageni Shin ka san cewar sunana bashi da kyau a waje? Dan bakinta ta yatsina ta ce" kama sani ne domin wa'inda ke zagin nawa da irin haka da yawansu matan da na zame masu tashin hankali ne, sai samarin da na raina shekarunsu irinka Ban san yaya aka yi na raina mai kananun shekaru ba Ni din ce mai rigima Ina famma da fitina da yawa hakan ya sa nake tunanin anya kuwa namiji mai kananun shekaru zai'iya hakurin halayana? Matsota ya yi sosai yana dubanta ya ce" kannanun shekarunna ba su zasu hanna na kasa hakuri da halayanki ba Najeeba Baki san cewa babar kadara ita ke saka biyaya dole ba? Najeeba.... Ya fada a sanyaye yana mai kara dora mata takardar nan tare da wata takardar itama ta bankin ce sannan ya hade hannayensa ya ce" ba rokona kika yi ba, ban kuma nuna zan iya da dawainiyarki dan kin kasance mai son kudi ko wani abin ba Abinda na sani *MACE* yar gyara ce, dole a gyara mace, dole a kashe mata kudi idan ana so a ganta tsaf tsaf tsaf da ita, ba wai abinda ya fi karfina na tarka ba, kowani mutun kan yi daidai karfinsa ne Najeeba, da kwaliyarki, da kyan tsarinki na ganki, a yanzu da nake son kasancewa da ke ina so ki zauna da ni daya kwal, hakan ya sa nake jin zan iya maye maki gurbin sauran samarinki ta kowani fani, zan iya da kowace lalura taki ta yau da kulun, ki yarda da ni ki amincewa motsina hakan zai saka na kara gyara tsayuwana na faranta maki Murmushi ta yi har cikin ranta, itafa ta mayar masa ne dama dan ta ga iya gudun ruwansa sannan ta nuna masa kudinsa basa gabanta, aman ina ita ina nuna bata son kudi? Ta fada ta kara tana son kudi yanzu tana son su gobe Ba wanda bai fito nema ba Ba wanda idan aka mika masa baya karba ba Halal take
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191