Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Adade Ana Yi Book 1 Complete Hausa Novel 1,219 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Biyu,ya Mallaka ma Abba na K'ofar Gida,a Kasuwa kuwa yana da Shagon Saida Yankunne masu daraja,聽 Aikin Kafinta kuma be bari ba, don ya zama Ogan kanshi yara ne dashi. Kasancewar ya gama karatu da Matsayi mai kyau, wani Mallamin su ya bashi shawarar zuwa Zaria neman aiki don ya gani a Newspaper ana Neman wanda suka gama Makaranta,ya samu Abba yace "suje Zaria neman Aiki" Abba yace "Wallahi Sada baka da Godian Allah, Aikin me zakaje nema? Kana da Sana'oinka, yo ko ni da Shago na daya a ba zanje neman wani aiki ba, balle kai,Mallam kawai ka zauna tare da matarka, nima hakan zanyi" Sada yace "ai ba laifi idan aka k'ara hanyar Samu" a tak'aice Abba yace "to ba yanzu ba nidai Allah ya baka Saa". Fir ya k'i bin Sada Zaria, Sada ya tafi da takaddunshi, cikin ikon Allah, aka dauki Sada Aiki, kuma zaa dinga bashi Albashi mai tsoka. 聽 Ran Juma'a yake zuwa Kano ya koma ran Lahadi, sosai yake kula da Matarshi da Hajjonsu, harda Abba, duk abunda zai siyo ma gidanshi sai ya siyan ma Abba, dalilin haka ne Abba yayi relying kan Sada,har ya zama raggon Mutum, zuwa da dawowan da Sada keyi na daga hankalin Hajjo, don ta kanji a Radio Hadarin Motoci daga wannan gari zuwa wannan gari, wannan zuwan da Sada yayi ta mishi magana "Yanzu kai Sada, baka jin wahalan tafiya ko? Baka gudun Sharrin k'arfe?" Yayi murmushi yace "Umma, Allah zai kare, tunda ina daku ai dole nake zuwa ganinku" Hajjo ta jinjina kai, tana son Halaiyar Sada, yana da kula sosai ba kamar Abba ba, shi da yake cikin gari sai yayi kwana 8 ko fi bata dorashi a idonta ba, ta nisa tace "Sada, tunda matarka na hutun Makaranta, ka dauketa ku koma chan gun aikin ka, alabasshi in ta koma Makaranta ta dawo" dadi kamar ya shide shi, dama kunya ce ta hanashi tafiya da Yesmeen, yace "Umma kefa?" tace "in dai ta nine kuyi zamanku chan ka maida hankali gun aikinka, amma na san ba zaka iya ba sai kazo ganina da danuwanka, to ko zuwa bayan wata1 haka sai ka dinga lek'omu" yayi godia yaje ya sanar da Yesmin, itama sosai taji dadi don tana kewan Mijinta. 聽 聽 Zuwa yayi ya gaya ma Abba shawarar da suka yanke, yace "ai dama hakan yafi, zuwa da dawowan nan akwai matsala, gwara ku koma chan" nan suka danyi fira kadan har ya ke gaya mai Mairo na da juna biyu wata 3, murna kamar me gun Sada,ya zaro dari biyar ya ba, yace "ga goron Albishir" Abba ya yi dariya, yace "ai ka shiga ciki kai mata sannu don tana ta kwaikwai, ba don yaso ba suka shiga gidan Abba, kawai shi har yau hankalin shi be kwanta da ita ba, tana zaune ta tara uban miyau a baki, yace "Madam ya jiki?" cike da yatsina tace "da sauk'i" Allah ya k'ara sauk'i" Abba na murmushi yace "Gobe zaya wuce Zaria da Yesmeen" ta dan yi yastina kafin tace "au haka zata tafi bata mana Sallama ba?" Sada yayi adria yace "maida wuk'an zamu biyo da safe kafin mu wuce" bata ce komai ba, din har yanzu bata daina jin wani abu game da Sada ba, haka suka fita, har k'ofar gida Abba ya rakashi yace "to a gaida Umma da Yesmeen". 聽 聽 聽 聽 Bayan Wata Daya Kwana biyu kenan ta ke jinta wani iri, tashin zuciya da k'warnafi ke damunta, bata yi k'asa a guiwa ba Sada na zuwa ta sanar mai, yace ta shirya suje Asibitin Shika, haka ko akayi, gwajin farko ya nuna tana dauke da juna biyu wata daya, Fadin farincikin Sada bata baki ne, haka ya dinga Addua. Washegari yaje Kano ya sanar ma Hajjo, Hajjo tayi adduan Allah ya raba lafiya, a lokacin Cikin Mairo na da wata huddu, fi'ili da iyayi dai Mairo nayi, ita bata son kaza ba ta cin kaza, kullum sai ta ci tsiren Hansin,shi ko Abba ya ta biye mata. 聽 聽 Lokacin da watan Haihuwan Mairo ya tsaya, lokacin Yesmin suka koma Kano, Yesmeen tayi ja sosai, cikinta na wata biyar yayi dabas a jikinta, ta zama abar shaawa, da taje gidan Mairo kai mata Akwatin da Sada yayi na Jariri, baki Mairo ta bude tana kallon Yesmeen, kasa boye hassadarta tayi, ko murnan ganin kayan batayi ba kamar yanda take mamakin chanzawar Yesmeen. Don bala'i, saboda da damuwa a ranar ta fara nak'uda, bayan yan wasu awanni ta haifo yaronta dan Jazir dashi,daga Asibiti tace ita a wuce Gidan Hajjo da ita, Hajjo ta tarbeta sosai. Yesmin ta kama zanin da Mairo ta bata wurin haihua ta wanke su tas. Haka a ka dinga tarairayar Mairo da Jaririnta.Rago Sada ya Siyo, ran Suna yaro yaci ABDULMAJID. 聽聽 Yesmeen ce Rainon AbdulMajid, Allah ya dora mata son yaron, itace wankin kayan kashin shi,har Abba kance mata Ummin AbdulMajid. AbdulMajid na da wata 4 Yesmin ta haifo danta Namiji,Farinciki gunsu ba a magana, har Yola Sada yaje ya gaya ma Iyayenta,da zai juyo aka hado shi da tsohuwan da zata kula da ita, Akwati guda Sada ya yi ma Uwar Jego da Jaririnta, harta Mairo sai da ya siyan mata Atamfa da Lifaya na fitar suna, ran Suna Yaro yaci ZAID. 聽 聽 聽聽Jim kadan bayan Haihuwan Zaid Mallam Iro ya rasu, Mutuwar ta girgiza Sada,yayi kuka sosai, Allah sarki tun kafin a rufo shi babban danshi yace akwai dukiyar Sada a gun Mahaifinsu, Sada yace "a bari a gama zaman makoki sai ayi magana" amma shi Dan yace "aa, Baba yace da ya rasu a damka maka Dukiyoyinka" Mukullin Shagon Kasuwa ya ba Sada, kasa karba yayi sai Abba ya karba, haka aka suturce shi aka kaishi gidanshi na gaskia. 聽 聽 Sada ya dauki nauyin gidan Mallam Iro don ba zai taba manta Alherinsa gareshi ba. A na haka ne Sada suka tattara ina su ina su suka koma Zaria, Zaid na da Wata daya, sam ba haka Mairo ta so ba, so tayi su zauna tare tayi ta ganni abubuwan da suke ciki. 聽聽 Bayan 40 ne Sada ya samo ma Yesmeen makarantan Ungozoma(Midwifery),Goggo na nan, Haka suka cigaba da Rainon Zaid. 聽 聽 聽 Bayan Shekara Hudu 聽 Alhaji Abba Abu ya kalli k'aninshi Alhaji Sada Abu yace "Gida yayi kyau sosai, Allah ya sa Alheri, sai ayi Sauka ku tare" Alhaji Sada ya murmusa yace "InshaAllah, yauwa sai maganan Makarantar Abdul dina da Zaid,tunda bakinsu bude yake ya kamata a sakasu a Boko da Islamiya"聽 Alhaji Abba yace "to ai sai a saka sun". Alhaji Sada ya Gina Gidanshi a Sharadda, Gidane hadadde wanda sai wane da wane ke mallakan irin gidan,yana da motarshi mercedez 190, da ya siya Motar nan ne ya ba Alhaji Abba tsohon Motarshi starlet, bayan ya siya musu gidan da Alhaji Abban ke Haya, duk sun zama Alhazawa, don shekaru biyu da suka wuce Alhaji Sada ya biya musu Makka su 5 har Hajjo, sukaje suka rage farali. Kudi gareshi amma ba su rufe mai ido ba, ba su sa ya dau rawanni tsiya ya daura ma kanshi ba don har Yau yana aikin Kafinta. Yana kamantawa duk abunda

Table of Contents

Chapters

169 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});