Chapter 34
Chapter 34
ilaihir rajiun yake maimaitawa, a hankali ya zame k'asa yana hawaye, Nana na kuka ta tsugguna gabanshi ta rungumeshi, a kafadunta ya ke kuka, rayuwa ta mai k'unci, shikenan Mummy ta tafi ta barsu, Shak'uwarsu da Mummy ya wuce tunanin me tunani, yasan his Mom is not all perfect, amma to him, she's the best Mother in the whole wide world, tausayin Daddynsu ya rufeshi, tausayin k'anenshi, Ziyada, Zaineema da zafin zai zame mata biyu ga rashin Miji ga rashin Uwa, Dan autansu Muhsin, da wacce Mummy tafi kusanci da ita wato Zinatu. Jijjiga Mummy Zaineema keyi tana kuka, da k'yar Daddy ya shigo Dakin ya kife kan Mairo yana kuka mai tsumma zuciya, Abdulmajid ya shigo, ya kallesu, kuka yakeyi amma ya daure yace "zaa tafi da ita gida ayi mata wanka don kaita makwancinta" kukansu ya tsanantu gaba daya, haka aka gungura Gadon Hajia Mairo har harabar Asibitin, aka sata bayan Mota aka tafi Abba Abu's Mansion. Ziyada ta shigo gidan da gudu, tana Makaranta Zaineema ta kirata a waya, a rayuwarta, bata ta6a shiga motan haya ba sai yau,a Parlorn k'asa aka shimfide Mairo, tana zuwa ta fada kanta tana jijigata, sai da Majeed ya rungumeta ya na shafa bayanta "Ya Majeed, Mummy ta tafi ta barmu" "Shhhh Ziyada" hankalin Majeed yayi k'ololuwa guj tashi da yaji Zinatu ta k'wallara Ihu ta fada kan Mummy, shigowar su kenan ita da Muhsin, Falallu direba ya daukosu, kuka Zinatu takeyi tana birgima, shima Muhsin Kuka yakeyi bawai don ya fahinci meke faruwa ba, shi dai ya ga Mummynsa kwance a k'asa. Kan Majeed ya fara Zafi, da dabara Mom din nana ta janye su tayi sama dasu don yanzu zaa yi mata wanka. Daddy da Majeed ne zasu wanketa. * Indai Idonshi ba gezau yake ba, indai lafiyar idonshi k'alau to shakka babu ya ga Hannun Mummy ya motsa, motsin ya sake gani, da sassarfa ya k'arasa gunta yana murmushi, "bata mutu ba, wallahi bata mutu ba" hankalin su gabaki daya ya dawo kan Majeed da yake k'okarin ciccibar Mummy, a tare sukace "Ba ta mutu ba?" Majeed na tafiya da Mummy a hannunshi yace "mu koma Asibiti" duk suka rufa mai baya. Ba asibitin da sukaje dazun suka zo yanzu ba, wani sabon Asibiti ne a Maitama, nan da nan aka karbeta aka hau aiki kanta. An samu ta dawo hayyacinta, kafin aka basu daki a ICU, Dr ya shaida musu cewa "ta kamu da hawan Jini wanda ya zoma ta farat daya, sai doguwar Suman da tayi, gashi ta zubar da Jini da yawa, yanzu an samu Bp dinta ya dawo normal, so a barta ta huta". Majeed ya bashi tabbacin ba zaa dameta ba, ta Windown dakin suka lek'ata, Hannunta sanye da Cannula bangare daya ana mata karin ruwa,dayan bangaren kuwa ana mata k'arin Jini, sai Hancinta manne da Oxygen mask, 3in1 kenan.(Hmm lallai su Mairo Ashe akwai sauran kwana) Kwanan Mairo Uku a Asibiti ta farfado har ta fara magana, bakin ta na budewa ba salati ba ambaton Allah sai cewa tayi"Shikenan mun talauce, sun yashe mu" da gudu suka yo kanta suna kiran "Mummy"ta kallesu one by one tace "kar ku damu, ba zaku zauna ciki talauci ba, Mummy zata samo hanya, ba ku gaji talauci ba, ba kuyi sabo da talauci ba, ba--" Daddy ya katseta "haba Maryam, daga farfadowanki?" "mu bamu damu da ko zamu talauce ba, kar mu rasaki Mummy" cewar Ziyadatu, murmushi mai ciwo tayi tace "Ziyada, ba zaki gane ba,Documents din da ka sace a Office din Daddynku, Ownership Shares din Hadin guiwa ne, Ba Daddynku kadai ke dashi ba,to an daukeshi,kuma each share zai kai kimanin Miliyan Talatin, kwanaki an sace Motar Yayanku, wanda a ciki akwai Muhimman takardun Companies din Furnitures har biyu, me ya rage mana?" ta sauke naunauyar ajiyar Zuciya ta kalli Abba kafin ta kalli Majeed tace "kuyi hakuri, amma naci bashin Banki har Miliyan 15 ba tare da saninku ba, lokacin da 'yanfashi suka tare Boy, nayi zaton bussiness din mu zaiyi k'asa, kila ma har a kai ga kulle Companies din, shiyasa naci bashin, da niyyar in an farfado mu biya banki,gashi yanzu ba da komai, bamu da komai,gashi Zaineema ba Aure, Asirinmu ya gama tonuwa" ta fashe da kuka, Zaineema da Ziyada suma kukan sukeyi,Ziyada tace "Mummy, akwai Allah, mu fawwala ma Allah komai, komai zai yi daidai, wannan ce kalar Kaddararmu, wannan kaddarar ce ta shigo RAYUWARMU,mu rungume shi hannu bibbiyu, kuma InshaAllah Allah zai bamu mafita, besides ai Yaya na aiki" Mairo Kina tunanin kwangilar Zanen Gidaje da Tituna da Yayanki ke samu jefi jefi ne zai rik'emu? Ziyada, ke yarinya ce, har yanzu baki san rayuwa ba, ina muku tsoron talauci" Majeed tausayin kansu ya rufe shi, yayi saurin kwakulo murmushi yace "Who cares if we are Rich or Poor? What matters is that we'll be together always and forever" Ziyada tace "We'll stand by eachother's sides" Daddy yace "Allah ya muku Albarka" suka amsa da Amin, Mummy ta tabe baki, a ranta tace "hmm, kudi sune komai, in ba kudi ba jin dadin rayuwa". 聽聽 Amsa sallamar da akayi sukayi, hankalinsu gabaki daya kan k'ofar, MD Fannaz Ventures ne da wasu mutane biyu,Daddy ya k'arasa gunsu yana musu sannu da zuwa, aka gaisa a mutunce, MD yace da Mairo "Madam ya jiki?" Mairo ta kwakulo murmushi tace "da sauk'i Alhamdulilah" "Allah ya k'ara sauk'i" suka amsa musu. MD yace "Alhaji Abba, maganan Shares dinnan ne, kace zaka ban kudin,in kudin be samu ba, kabani shares din ga masu siya nan" Zufa ya keto ma Daddy, zaiyi magana Mairo tace "MD, donAllah ka bamu lokaci, wani ifti'la'i ya afko mana, amma InshaAllah zamu biyaka" MD yace "Hajia Mairo kenan, nima iftila'i ya auko min na karayar Azziki, a halin yanzu, Mahaifiyata na fama da Cancer za mu fiddata Egypt, ko da suka mana budgeting kudin, ana bukatan Miliyan 20, saboda Cancer din ya kai Stage 8, Chemoteraphy din na tsada, tsakani ga Allah banda isassun kudin da zaayi hidiman nan, shisa na yanke hukunci saida shares din a gaugauce" Dakin yayi shiru sai k'aran Ac din da sheshek'an masu Kuka. Daddy zufa ke keto mai, Mairo kanta yayi zafi, ganin ba me niyyan Magana Md ya sake cewa "DonAllah ku san yanda za kuyi dani, Mahaifiyata na cikin hali" shiru sukayi suna tunanin yanda zasu Samo Miliyan Ashirin, ba sa tunanin ko hade kudaden account dinsu duka zaa yi ba zai rufe miliyan biyar, Majeed ya ja iska ya fesar yace "Alhaji, zan kawo maka kudinka Gobe InshaAllah". 聽 Suka bi Majeed da Ido, MD yace "toh Allah ya yarda, Madam Allah ya k'ara sauk'i" ba ta amsa ba, sai bin shi da ido da sukayi, yana fita duk suka maido dubansu ga Majeed. Ya san bayani suke nema ya samu wuri ya zauna kana yace "Mummy, Daddy kunsan dai wannan Jarabawa ce daga Ubangijin mu,Karayar Azziki ne, so sai mun rungumeshi ko mun k'i ko mun so,MD na bukkatar kudinshi,Mummy kin ci bashi banki har miliyan 15,Mummy ta ya zamu biyasu duka?" ya kafa mata idanuwa yana son ta bashi amsa ido jawur tace "Boy, wallahi ban sani ba,ban san ya zaayi ba"a zuciyar ta kuma tana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169