Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 157

Chapter 157

Adade Ana Yi Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Allah ya sanya Alheri" nan tai ta addua suna amsawa. Mikewa tayi ta shiga ciki don kiran musu Mairo, "Hajia Mairo, ga Yarana sunzo" tsaf ta gane ko su wa take nufi da Yaranta, Hajia Aynarh yar bariki ce, so take ta dinga k'ular da ita ta hanyan kiran 'yayanta, yaranta, inshaAllah ta daina nuna mata haushi ko wani abu takan hakan, don ta hakan take so ta dinga k'ular da ita, indai bariki ne to itama ai ta iya, murmushi ta mata, tace "sunzo gaida uwasu ko? Barinje in gaida yaran Aunty Aynarh" ba ta jira cewar Aynarh ba ta fita daga dakin, ita ko Mamaki ya sa ta bita da budadden baki. Tana shiga Parlorn duk suka yo kanta don suui mata Oyoyo, banda Abdulmajeed da yake zaune yana ta fadada Murmushin shi, Wallahi Uwa Uwa ce ko da ta banza ce, yanda sukayi missing dinta haka suka dade a jikinta rungume da ita, basa tuna komai sai Soyayyar dake tsakanin Uwa da 'ya'yanta, ganin yanda Zaineema da Ziyada suka runk'unk'umeta yasa Abdulmajeed cewa "Yadai? Ku saketa mana" suka saketa suna Daria. Don k'ulafuci kujera daya suka zauna da ita, wannan ta jingina da hannunta wannan kuma ta kwanta kan kafadarta, Muhsin da Zinatu tuni sun shiga gun Aunty Aynarh. Baki suka hada wurin cewa "Mummy ina wuni" ta amsa su cike da So da Kaunarsu, tana kallonsu daya bayan daya tana tunani a zuciyarta, in banda Zuciya kowa da irin tasa, me zai sa tana da Wadannan kyawawan hallitun amma ta sa a ranta Jin dadi ba zai cika ba sai da Arzikki, ai Babban Arziki Allah ya mata, kawai dai son Zuciya ne ya hanata gani, to me ya kai wannan samun Namiji kamar AbdulMajeed a matsayin Da Arzikki? Yaro daya tamkar da dubu, Yaro mai hangen nesa, da dukkanin zuciyarta ta yi nadama, akan ce *Dan kuka me ja ma uwarshi jifa, wannan Uwar ce ta jama 'ya'yanta jifa* murmushi ya k'i bacewa daga fuskarta, meyasa tuntuni bata fuskanci in tana da yaranta bata bukatar komai ba? Meyasa son kudi da son abun dunia suka makantar da ita? "Ya Allah! Ka yafe min" AbdulMajeed yace "Mummy, wai wannan farincikin na ganin mune? Naga sai dai a kalleni a juya a kalli Zuzu da Zaineema ana Murmushi". Wani Murmushin ta sakar me k'ayatarwa tace "hmm kaidai bari Boy" duk suka sa daria don ta jima bata kirashi da Boy ba, tace "ina ta nadamar wautana da son zuciya ya sani aikatawa, tare da kunyarku da nakeji, ina ji kamar nayi failing dinku, ban bar muku komai da zakuyi Alfahari dani ba, inaji kamar So, k'imata, da daraja na sun ragu a idanuwanku, ina ji kamar kun tsaneni ba kwa kallona da Mutunci--" AbdulMajeed ya rausayar da kansa, wallahi ya tsani maganar nan kwatakwata, ya dan zamo daga kujera yayi kamar tsugunne yake kan kujerar yace "Mummy listen sosai, don yau ne rana ta k'arshe da zamuyi maganar nan, Kinyi laifi babba, amma kinyi nadama, Allah na yafe ma Bawan da yayi laifi ya kuma rok'i gafarar Allah da wanda ya ma laifi, ya kuma sa a ransa cewa ba zai sake aikata irin laifin ba, to Mummy kin tuba, kin nemi yafiya, an yafe miki, me zai sa ki ta fama da guilt? Mummy abunda kikayi rubutaccen alamari ne, babu yanda zaayi a guje mishi, me aukuwa ta riga da ta auku sai dai a kiyaye gaba, ke Mahaifiyarmu ce, ko me kikayi zamu cigaba da kasancewa mu 'yayanki ne, in Dunia ta juya miki baya, mu Yayanki mu zamu kasance tare dake, darajarki ba zai zube a idonmu ba, k'imarki k'ara yawa take a zuciyoyinmu, ban taba nadamar samunki a matsayin Mahaifiyata ba, ina Alfahari dake, kece Uwar da kowani Da zai so ya kasance shine Da a gareki, saboda Soyayarki a garemu me yawa ne, Mummy muna sonki, we love you the same or even more, donAllah yau ta kasance rana ta karshe da zaki sake mana irin maganar nan" Ziyada tace "Mummy wallahi muna sonki, ni yanzu ko mutum kika kalli gabas kika yanka ai ba zan daina sonki ba" Zaineema tace "You are the mother we could ever ask for, wallahi Mummynmu tafi ta kowa, Allah ya ja da rai Mummynmu" Farinciki ya sa hawaye gangarowa daga idanunta, Waiyo Allah, cike da so da kauna take kallonsu tace "AbdulMajeed me zanyi in ban da kai? Me zanyi in ban da ku? I'm the luckiest Mother living, Alhamdulilah bi ni'imati.. Nagode Nagode, ina alfahari da kai, ina alfahari daku gabaki daya". Abdulmajeed yace "Mummy dama nace miki Khalid yazo ko? To an maida auren yanzu da laasar, yanzu Zaineema bankwana tazo miki, zata bishi America yau, chan yake wani course" ganin hawayenta sun cika taf a idanunta ya sa shi saurin cewa "Exams zaije yi, zasu dawo InshaAllah da ya gama" ta dan ja numfashi tace "toh Allah ya bada saa ya tsare hanya, sai a kula da kai, Allah ya muku Albarka, ya baku zaman lafiya da Mazajenku" suka amsa da Ameen, Abdulmajeed yace "Sai kuma niko? Allah ya kaimu bikina ko?" Ziyada tace "kai ya Maji ko kunya?" sukayi daria Wayar Daddy ya katsesu, Abdulmajeed ya dauka "Hello, wai ku kwana zakuyi? Bakaji yanzu zasu tafi Zaria kuma suje Abuja duk a yau ba? Ku dawo yana jiranku" a ladabce yace "Toh Daddy" yace "Oya ku tashi, Maigida ya kira yana fadan zaman mu" Mummy tayi dan jim, bata son rabuwa dasu, Abdulmajeed yace "ku shiga ku ma Aunty Aynarh Sallama, Zaineema ta mike ta shiga ciki, Ziyada ta bi bayanta, kan Mirror sukaga Aunty Aynarh na ta zuba wani abu kamar magani a wani bottle tace "Yauwa Zaineema, ga guzuri ina miki" tace "Aunty na menene?"tace "ke yanda kika dade a Gida ai dole in gyaraki, duk da a k'urarren lokaci ne, amma its never late" so ki sha yanzu, ki sha da daddare, kiyi overdose, kar ki damu, kayan Natural Products ne, ko ni da ba Miji ba ina ta sha, kinga randa nayi aure a dadin Mijin" Zaineema da Ziyada suka sa daria, Zaineema tace "ana ma Daddy tanadi kenan" tace "Ahh, ku tsaya nan, kai dan Gidanku uwaku ce ni" suka sa daria tace "ba illah, InshaAllah ki saki jiki ki sha kingane?" ta murmusa tace "Allah ya bar Aunty Aynarh" Ziyada ta turo baki tace "ni kin manta ina da Aure?" tace "Ya zan manta Matar ZSA, aike muna tare" ta runguma Zaineema ta mata Adduan fatan Alheri, a tare suka fita daga dakin, Mummy duk jikinta yayi sanyi bata son rabuwa da Yarta, ta tuna farkon Auren Zaineema, kuka sukayi tayi a tare, da yake Bariki ne, a lokacin Harda ita aka sada Zaineema da Gidan Miji, yanzu ko an girma, ya zatayu tunda Gidan Miji zata, Addua ta mata, ta shafa bayanta, suka shige Mota suka koma Gida. ** "Yanzu Daddy ba zamu rakiya ba?" Daddy yace "Rakiyar me Najwa har Abuja? Come on my friend, ku zauna Gida, salon Yawo, kuyi bankwana ai ko sati biyu ba zasu wuce ba" Paapa yace "ba wani rakiyan da zaa, Khaleed ya dauko Matarshi su tafi, say your Goodbye's Zaineema, gashi to 5" Zaineema ta rungume

Table of Contents

Chapters

169 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});