Chapter 80
Chapter 80
Khalim yace " Ki daina bata min lokaci, ki daina bata ma Kotu Lokaci, hakan na nufin, there was never an Audio, you made everything up" Zuciya taci Mairo, ta hau surfa ma Barrister Khalim Zagi ta uwa ta uba, Alkali ya sake tsawatar ma Mairo a karo na biyu yace "Malama Mairo idan kina da wata shaida da zaki gabatar to bismillah kotu na sauraronki inko babu to kotu zata zartar da hukunci a kammala wannan shariar ba ku kadai bane" Ai kamar jira take nan ta hau surfo balai da masifa ba kan Lawyern kadai ba Kotun duka, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, zage zage take kamar sabon hauka,sai sakin layi take tayi "ni zaka yaudara Khalimu? wato Alhaji Nakowa yayi bribing dinka? Ya saye Kotun gabaki daya, har Alkali tsohon Najadu, to wallahi ba zata sabu ba, sai na shayar daku madaran Mamaki dukan ku" Alkali ya umurci YanSanda su kama Mairo, "da sauri Majeed ya nemi Afuwa a madadin Mahaifiyarshi, ya ba Alkali hak'uri, janta yayi ya koma wurin Zama don jiran Hukuncin Judge. "Lawyern wanda ake k'ara ko kana da abun cewa?" cewar Alkali, Barrister Usman Baraji yace "Ya Ma girma mai Sharia, ina so Kotu ta gayyaci Nana Nakowa gaban Kotu" "Kotu na Bukatar Nana Nakowa a gabanta" Alhaji Nakowa ya sadda kansa daidai yanda Nanan zataji shi yace "go Nana, you know what you must do" kai ta gyada ta tashi ta je gaban Kotu ta tsaya, Bayan ta amsa tambayoyin Gabatarwa Barrister Usman Baraji ya fara mata tambayoyi kamar haka; Add Vote Nana Nakowa, shin kin dauki Credentials din AbdulMajeed?" tace "Aa ban dauka ba" "ya akayi kika tsinci kanki a halin da kike ciki yanzu?" Nana ta juya ta kalli Mummy tace "Wata rana Mummy ta kirani dakinta tace ince ma Dad dina ya bani 5mil" sai nace mata tayi hakuri, shima Daddyn beda kudi yanzu, shikenan ta fara threatening dina, wai in ban nemo mata kudi ba, zamana da Yaronta ya k'are, zata k'ala min sharrin da ba zan iya firda kaina ba, da nuna mata ni ban san inda zan samo mata kudi ba ramfa ya baci, the next day sai naji tace wai na sace ma Majeed Credentials kuma wai ina bin Maza" Mairo mamaki ya hanata motsi, ta san ita Makira ce, amma bata taba zaton Nana ta fita iya Makirci ba, kirikiri Nana ta shirga mata k'arya, kotu ya hau surutu, kowa da abunda yake tofawa, sai da Alkali yace 'Order' kafin aka sausauta. Barr Usman yace "Mungode Nana Nakowa, Ina son Kotu ta kira mana Alhaji Ado Nakowa" Alhaji Nakowa ya gabata gaban Kotu, Barr yace "Me ke tsakaninka da Hajiya Mairo?" Alhaji Nakowa yace "Matata k'awarta ce, kuma mun taba wata kwangila da Alhaji Abba Abu" Barrister yace "kace kana da Maganan da kake so kayi a gaban Kotu kafin a yanke Sharia?" "Ya Mai sharia "A lokacin da AbdulMajeed yake auren Nanata, Hajiya Mairo tana amfani da son da diyata ke ma danta tana amfani da hakan matsayin jarinta kamar yadda ta gaya muku da kanta, bata sati bata buk'aci kudi daga gun diyata ba, in Nana ta nuna babu saibta mata barazana cewa zata sa Majeed ya saketa, haka diyata ta kare rayuwarta gidan Abba Abu cikin Barazana, baya ga haka, ina bin Hajia Mairo Naira Miliyan 30, ta karba Miliyan 20 kamin auren danta da yarwurina, Miliyan 10 kuma daga baya ta karba bayan sunyi karayar Arziki, nima ba su ke gareni ba a lokacin, amma saboda naga akwai Alakar auratayyar yaranmu, nayi chukuchuku na hada mata akan zata biyani in ta sayar da wasu kadarorinta da tayi ikirarin tana dasu, shine nake son Kotu me Adalci ta da tace mata ta biyani, ina da bukatar amfani da su". Kamar Robot haka take zaune, komai ya dauke mata dif,ba ta gane komai, sai da Majeed ya zungureta "Mummy yaushe kika ci bashin Miliyan Talatin? Firgigit ta tashi kamar wacce aka tsikara, kamar ta rufe Alhaji Nakowa da duka tace "Babban Balaeen chan, Kaci uwar rainin wayau Alhaji Nakowa, dan kutumar babbar buraubaka wani yace ka bamu Miliyan 20 dinnan? Ba lokacin da kuke son Majeed ya Auri Nana bane kuka kawo mana Miliyan Ashirin din har gida ba? Saboda kai baka tsoron Allah, kuma da yake karya cike yake a tunbinka zaka ce Miliyan 30 ne, kuma wai bashi, to Mortgage bank ma yaci Ubanshi, shege Makaryacin banza, sai ka danneni ka karba, karfi yaci daru ya danne, Mutumin banza". Da k'yar Alkali ya sa Mairo yin shiru, ya juya ya tambayi Alhaji Nakowa Shaidansa na Maiaro ta karbi Bashi a gunsa, yace " kwarai kuwa ina dasu ya mai shari'ah, ganin da nayi Miliyan 20 da ta karba da farko bata fara biya ba, hakan yasa naji shakkun sake bata wasu kudaden don nima lokacin ina fama da kaina, Don haka nace sai ta sa ka hannu a wadannan takardu guda biyu, sai da tayi signing gaban Matata Aminiyarta, da wasu k'awayensu su 3," Alk'ali yace a gabatar da takardu gaban Kotu, Sakatare ya amshi takardun daga hannun Alhaji Nakowa ya ba mai shariah". Sosai Alkali ya karance takardar sannan ya sa aka mik'awa Mairo ta duba ko tana da Ja, Cikin tashin hankalin da tun da tazo duniya bata taba ganin irinshi ba tace"WALLAHI WALLAHI ALKALI BAN SAN WANNAN BAYANI BA, TABBAS WANNAN SA HANNU NA NE AMMA NI BA NI NAYI BA, wani ne yayi fabricating Evidence dinnan, dis is a Forged Signature". Alk'ali yace "Alhaji Nakowa kana da Shaida, baya ga takardun nan?" Alhaji Nakowa yace "Shaidun da ke jikin Takardun, Hajia Sugrah, Hajiya Zarah Bukar, da Hajiya Suwaiba wanda suke ce ma Mom fateey, kuma duk suna cikin Kotun nan mai Albarka" Alk'ali ya bukata da su fito gaban Kotu, ya musu tamboyi suka amsa, suka shirshirga tasu karyan, suka ce a gabansu akayi a garin Abuja, tayi Signing din kudin a kan Idanunsu, kuma Alhaji Nakowa ya bata kudin kan idanunsu. Mairo ta hasala ta chakumo Hajia Suwaiba don sun fi shiri tana jijjigata "Wallahi k'arya suke man, kuji tsoron Allah Hajia Suwaiba, ku tuna Zaman mutunci da Amana da mukayi da juna, kar Alhaji Nakowa ya siyeku kuyi min kazafi" Mom Fateey ta bangajeta tace ba wani "kazafi, abunda muka gani ne muka fada, mu muna bayan gaskia". Bakin Hajiya Mairo be mutu ba, nan ta hau surfa ruwan zage zage da tsine tsine, harta Kotun da Alkalin sai da ta zage tas, Majeed ya ji kanshi na barazanar fashewa, a hankali ya zame jikinshi ya bar Kotun. Kotu ta dau Hayaniya, kowa da abunda yake tofawa, Alk'ali yayi 'yan rubuce rubucen shi, Alkali ya umurce kowa da yin shiru, da k'yar aka samu kowa yayi shiru, Alkali ya zartar da hukuncin shi kamar haka; Bayan Kotu ta saurari bangarori biyu, na me k'ara, da wadda ake k'aran, Kotu tayi watsi da k'arar Hajia Mairo a matsayin Kara Mara kan Gado, saboda rashin kwararun hujoji da Shaida, sannan kuma Kotu ta ci tarar Hajia Mairo Naira Dubu Dari Biyar don ta ci Zarafin Kotu ta Wulak'anta Kotu, Sannan kuma Kotu ta Umarci Hajiya Mairo da ta biya Alhaji Nakowa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169