Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 121

Chapter 121

Adade Ana Yi Book 1 Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Waya chan ki danna 1 roomservice ki fada duk abunda kike so su kawo miki, take care of yourself please" be tsaya jin rashin kunyarta ba ya dauki bag ya rataya ya fita. Kamar jira take, yana fita ta kira roomservice tace a kawo mata Chips da liversauce" ba a wuce 15 mins ba akayi knocking aka kawo mata service dinta, tana gama ci ta chanza kaya, ta kunna TV ta fara kallo, har wurin past 10, kafin ta kashe kayan Kallon ta kwanta, ba bacci takeji ba, ta dai gaji ne, ga tsoron da bata san na meye ba. Wurin 10:30 sai ga Zaid ya bude ya shigo da Sallama, ya kunna wuta, ganin Plate yayi alamun taci abinci, ya sauke ajiyan zuciya, ya kalli Gado, ya ga ta kwanta, a gajiye yake, a gun Meeting din sai rushing yake don ya dawo ya ganta, harda ya hakura a ka gama and it was succesful.. Kulle kofan yayi ya soma Zare kayanshi a hankali ya chanza zuwa Pyjamas, ya kashe Wuta ya dauko Laptop dinsa ya hau kan Gado, kamar jira take ya hau Gadon tayi zunbur ta tashi, da hasken Laptop dinsa yake kallonta yanda ta tsura mai ido yace "Yadai?" tace bangane ba, ya zaka hau min Gado? " da mamaki yace "to ina kike so na kwanta Kujera?" tace "ba dai dakin nan ba, ta ya zamu kwana daki daya?" Murmushi yayi yace "to ya kike so inyi?" a takaice tace "ka kama wani Dakin" ya kalleta yace "banda kudin kama wani dakin" galala tace "kaidin? Ni mallam ka fitar min a daki, ba zan kwana daki daya da kai ba, ko ka fita ko na fita" Zaid ya kalleta sosai yace "kiyi hakuri ki kwanta, barin koma kujera, ba bacci ma zan ba, zanyi wani aiki ne" cike da karfin hali tace "ni fa ba zan kwana daki daya da kai ba" ya kwantar da murya yace "kiyi hakuri, gobe sai mu raba daki, please Ziya, i dont have the strength to argue" bata tanka shi ba ta juya ta kwanta, ganin haka ya sa shi tashi ya koma kan kujera ya cigaba da latselatsenshi, Ziya ta sauke Ajiyar Zuciya, bata san ya zaayi dama ta kwana ita kadai ba, dama duk wani abu da take karfin hali ne, Thank God be fita ba, hankalinta zaifi kwanciya in ta san cewa yana dakin, bargo ta ja ba a dau lokaci ba bacci ya kwasheta. INDIA Yatsina fuska yayi yana ajiye cokalin shi cikin abincin da yake ci hadi da dafe kanshi dake wani irin sarawa kaman zai bude gida biyu yana kiran Allah. Hakan ya dawo da hankalin Maama dake danna wayarta tana kokarin kiran Najwa kanshi. Da sauri ta mike tana kama hannunshi da fadin "Subhanallah, lafiya?" Hannunta Paapa ya rike dam yana jin bazai iya bude bakinshi ya fada mata abinda yake ji ba, bama zai iya magana ba a yanayin da yake jin kanshi. Gabaki daya yanda yake riko Maama yana dafe kanshi da dayan hannunshi ya rikita mata lissafi. Bude bakinta tayi da nufin tai mishi magana taji kanta yai wata irin dokawa kaman an kwada mata karfe, ba shiri ta sake dumtse hannun mijinta dake cikin nata tana durkushewa kasa hadi da fadin "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un" wani duhu-duhu take ganin yana lullube mata idanuwanta data runtse gam tana salati da neman taimakon Allah jin yanda kanta ke sarawa. A hankali duhun dake cikin idanuwanta da kanta take jin yana budewa da duk numfashin da take shak'a. Kamun wasu images da bata fahimta su fara mata yawo cikin kanta. Daki ne take gani da kujeru a cikin shi da labulaye ruwan kasa masu haske. Kamun ta ga mutane guda biyu a tsaye suna hira, tana jin sautin maganarsu da dariyar da suke sai dai fuskokin su take son gani da dukkan zuciyarta, kaman sun san me take so suka juyo. Wata irin dokawa zuciyar ta tayi har cikin kunnenta. "Ammi..." Maama ta fada tana kara dumtse hannun Paapa cikin nata. Saboda yanda kanta yake ci gaba da bugawa. A mafarki, a ido biyu, a cikin maye, zata gane dakin da tai kuruciya a cikin shi. Yola ne, asalinta, tushenta, garin iyayenta da kakaninta. Yar Yola ce ita, bude idanuwanta tayi tana jan wani irin numfashi kaman wadda tasha gudu, kamun a hankali komai ya soma dawo mata. Da duk wani abu da zata tuna, da yanda ciwon da kanta yake yi yake sauka, har lokacin hannunta na cikin na Paapa da babu abinda yake gani sai Zaid da AbdulMajeed dan gun Yayanshi lokacin yarintar su. Sai dan uwanshi, dan uwanshi da yake kauna da dukkan zuciyar shi. Kano yake gani da yanayin komai na rayuwar su na dawo mishi kaman film aka kunna. Kamun yaga fuskar Mairo, yaga fuskar da a yanzun yake da yakinin har mutuwarshi ta riske shi bazai taba mantawa da ita ba. Musamman kalamanta da suka zauna a kirjinshi da zafi kaman garwashi, kanshi ya saki da dayan hannunshi yana dafe kirjin shi dake kuna. *"Ina so ka dauki matarka, da wasu 'yan kudi, ku bar k'asarnan, kuyi nesa da k'asar nan, kar ku sake waiwayen Nigeria, duk inda ka san muna iya haduwa ko ba dade ko ba jima kar kaje gun, wurare kamar Makka da Madina, Ina so ku manta da Mahaifarka, ku tashi ku tafi yanzu"* Kalamun Mairo ke dawo mishi kamar a lokacin take mishi, Ware idanuwanshi yayi akan Maama, da ta sauke nata idanuwan cikin nashi cike taf da hawayen da suke gab da zubowa, na Paapa cike suke da yanayin da bazai misaltu ba, kamun ya mike tsaye daga kan kujerar da yake yana dago da Maama. Goshin shi ya hada da nata "Na tuna...na tuna komai..." yake fadi mata muryarshi na rawa. Kai Maama take daga mishi hawayenta na zuba. "Me mukai mata? Me yasa zatai mana haka?" Saida Paapa ya hadiye wani abu daya tsaya mishi a wuya kamun yaja numfashi da fadin "Bansan dalilinta ba. Bansan me yasa ba, in akwai abinda nasani shine kowacce kaddara na faruwa da dalili..." Hannuwa tasa ta tallabi fuskarshi cikin tata, babu abinda take so, babu abinda take muradi da duk wani abu da ta mallaka daya wuce taji kafafuwanta kan kasarta, ta sauke idanuwanta kan yan uwanta, kan yayanta, ta shaki iskar data banbanta da duniyar nan da Mairo tai musu sanadin shiga. "Let's go home" ta ce wasu sabbin hawayen masu dumi na zubo mata. Sumbatar goshinta Paapa yayi yana jin yanayin da bazai misaltu ba. "We are going Home. Komai yazo karshe Yesmeenah " In hankali da nutsuwar shi sunyi dubu gida suke kira mishi.a Kama hannunta yayi suka shiga ciki dan su fara shirye-shiryen daya kamata, kamun ai musu visa ne aiki, sun san zai dauki lokaci amma abu daya suka sani, Zasu Gida. Tana shiga daki ta zaro wayarta Paapa yace"Wa zaki kira?" "Najwa.." ta amsa shi tana dialing number din Najwa hadi da kara wayar a Kunne. #1love #ADAY #bibiliciousfreakingfans #anatare #nagode Biebee Isa 馃挱A DADE ANA YI....sai gaskia馃挱 NA Wattpad:@biebeeisa Pg3鈨�6鈨� Pappa yace "Aa Yesmeenah,聽 duba kiga lokaci,聽 yanzu 10pm daidai da kusan karfe 3am dinsu,聽 duk inda Najwa take tayi bacci, kuma聽

Table of Contents

Chapters

169 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});