Chapter 30
Chapter 30
Sayluba sukayi, da gudu suka baiyyana a Parlorn, Nana ce rik'e da wata irin zuk'ekiyar wuk'a. * Kanta suka yi duka, hankalin Alhaji Nakowa a tashe, yace " Nanana, kiyi hakuri, ki ajiye wukan nan, ba a wasa da wuka" cikin karaji tace "wasa da wuk'a? Kana tunanin wasa da wuk'a mikeyi?" wukar tasa daidai saitin hannunta ta yanka, a lokaci guda suka sa ihu, Jini ya far fita daga hannunta, ta nuna su tace duk wanda ya matso kusa dani zan chaka mai, AbdulMajid yana matsowa tace "Wallahi zan kashe kaina idan har baka amince zaka auren ba" ta karashe tare da daura wuk'ar kan wuyanta, Hajia Sayluba ta zube gaban Majeed tana kukan ya taimaketa, ba zata iya rasa Nana ba, ita kadai gareta, Alhaji Nakowa ma magiya yake mishi, Hajia Mairo a kidime, kowa hankali tashe. Nana tace "Majeed ka ban amsa, na baka nan da 15seconds, idan baka ban amsa daya ba Wallahi zan lumama cikina wuk'a". Irge ta fara. Yanda Majeed yaga yanayinta ya ga tana bulayi yasan ta sha wani abu, tana iya kashe kanta a banza, ga jini na zuba ta hannunta, tana kawowa 5 da sauri yace " Na amince Zan aureki" murmushi tayi tace "ka rantse" ba watawata yace "na rantse da Allah zan aureki" tace "ranar juma'ah" guntun tunani yayi yace "gobe ne jumaar fa" wukar ta kara dadirawa a hannunta, da sauri ta fasa ihu shima yace "Na rantse gobe zan aureki Nana, donAllah kar ki k'ara illata kanki" murmushi tayi ta sake wuk'ar tare da zubewa k'asa,da sauri duk sukayi kanta. Asibiti suka kai Nana akayi dressing hannun, tasha bacci na kusan awannin 5, tana farfadowa ta sa aka sallameta, a cewarta Amarya ce ita, bai kamata ta kwana Asibiti ba. Majeed fa??. Tunda ya kulle kanshi a dakinshi bai sake budewa ba, kanshi yayi zafi, wai shi ya amince da auren Nana? Kuma gobe? Wai Nana? Kanshi ya rik'e sakamakon sarawan da yakeyi, yana ji Mummy na k'wank'wasawa yayi banza da ita, tayi tayi ya bude har ta gaji, haka zata koma jiki a sabule. Sai da akayi Sallahr Maghrib AbdulMajid ya fito yaje Massalaci, ko da ya dawo daga Massalaci ya iske Mummy a dakinshi, fuska ya daure, ya samu guri ya zauna, da sauri ta dawo gunshi, ta rik'o hannunshi tana kuka "AbdulMajid, nasan yanzu katsaneni, me zanyi ka fahimci duk abunda nakeyi don kai ne? Kana tunanin zan taba cutar da kai? I want the best for you, Nana isnt bad, tana da kyanta, da gatan ta, donAllah ka kwantar da hankalinka" da ya ga zata matsa mishi yace "Mummy just walk out" kuka ta fashe mishi dashi, AbdulMajid sarkin tausayi tuni Zuciyarshi ta karaya, nan ya hau lallashinta ya tabbatar mata da zai Auri Nana.. * Amsa kiran wayar tayi da "Hello" muryan da ta ji ne ya sata tuno da mutumin da suka hadu shekaranjiya a Silverbird, murmushi tayi kamar yana gabanta, ji tayi a tak'aice yace "fill me in" da murna ta fara koro bayani tace "ai in gaya maka, komai yayi daidai, nabi shawararka, gashi ya amince, gobe zamuyi Aure" "Good,kiyi insisting kan ayi muku dinner a goben, a beautiful girl like you deserve a Wonderful wedding" murmushi tayi wanda har ranta taji dadin kodata da yayi,a fili tace "zaka zo ko?" yayi murmushi yace "i wont miss" duk da bata sa ko waye shi ba, amma tana jin kanta da bin duk wani umurni nashi, dole kuwa a musu Dinner Party, bari ma ta kira Wedding Planner. Bayan Sallahr Jumaa aka daura auren Abdulmajid Abba Abu da Amaryarsa Nana Asmau Nakowa bisa sadaki Naira Dubu 100, mutane ke cincindiron yi ma Alhaji Abba murna, AbdulMajid yak'e kawai yakeyi yana gaisawa da mutane. Abunka da masu kudi, tuni aka hada wani Dinner a The Sheraton Abuja Hotel. 锟� 聽聽 * 聽 Amstrong ya kalli Zaid yace "All set sir, we can go into the mansion now"kafin ya juya ga yanmata biyu da ke zaune bayan motan sanye da Atamfa riga da skirt, yace "get ready girls"Zaid ya furzar da iska tare da danna horn a gidan,Maigadi ya bude k'ofa ya karasa gaban Mota tare da lek'awa, Zaid da ke gefe yace "Mallam Hadi ya aiki" Mallam Hadi ya yashe baki ganin an ambaci sunanshi "Aiki alhamdulilah" daya daga cikin matan dake bayan mota tace "sun wuce gurin Dinner din ko?" Mallam Hadi yace eh sun fi Awa daya da tafiya, Zaid yace "Abokan Abdulmajid聽聽 Ango ne daga Lagos, mun kirashi a waya yace yana wurin dinner ya aiko mana da key din part dinshi yace muzo mu shirya kafin mu iske su a Hotel din, ya ma ce in mun gama Falalu ya kai mu gun dinner" Zaid ya karashe tare da daga Makullan, Mallam Hadi yace "ai kuma Falalu ya tafi gun dinner shima, nikadai aka bari" dayar tace "ba Sheraton Hotep bane? Ai nasan gun, muje mu shirya kafin a tashi" Mallam Hadi ya wangale Gate suka shiga ciki zuciyarsu fari k'al. 聽 聽 Ba su sha wahalan bude k'ofofin Gidan ba, yanmatan nan su biyu tantiran 6arayi ne, ko ya k'ofa take sai sun budeta, daga Warri Amstrong ya musu waya suka taho ta jirgi. Zaid ya bi Gidan da Ido,wani tangamemen Hoto ya gani na Familyn Abba Abu gabaki daya, ya matsa kusa da hoton ya kura ma hoton ido, idonshi yayi Jazir ganin murmushinsu. Amstrong ya katse mai tunani yace "Oga, we have to hurry" Zaid ya basu Go ahead da su hau Sama, suka hau sama, da dakin Farko suka fara, Office ne, Zaid ya musu nuni da su wuce sauran dakunan, shi kuma ya kustsa kai cikin Office din tare da mace daya. Zaid ya bi Office din da kallo, wani save ya gani, ya ce macen tayi mai unlocking, Makullai da suka fi dari ta ciro daga bujenta, ba daukan lokaci save ya bude, Zaid ya karasa ya dinga ciro files files yana budewa, murmushin gefen fuska yayi ya tattara duka a hannunshi, aka rufe Safe din suka rufe Office. Amstrong kuwa yayi Babban Gamo, don Ghana MustGo din kudin da Baban Nana ya basu ba su kaishi ko ina ba sai dakin Mairo, Amstrong ji yake kamar yayi ihu don Murna, ga wasu Sark'a daham da Yankunne da suka samu a wurare dabandaban, har dakin Abba da AbdulMajid sai da suka shiga, suka samo abun amfani. Zaid da murmushi a fuskarshi yace "lets get going guys, i'm done here". Amstrong yaja ghana matan suka tattara jewelries din, bayan dayan ta sauka ta dauke ma mai Gadi hankali suka sa komai a booth suka bar Gidan,bayan ya ba Maigadi kudin da be san yawansu ba, Maigadi ya kwashi godia. ** 聽 Bayan sunje masauki amstrong yace "Oga ya zaayi da kayan nan?" Zaid ya murmusa yace "Its all yours, share among yourselves".suka hau shewa "Osheyyy, sai Oga".. Su sun san Oga yafi karfin komai, su gaba ta kaisu. * Manage this please, i'm preety occupied these days bear with me. Vote and Comment please. #1love #ADAY #bibilicioufreakingfans #anatare #nagode Biebee Isa [12:06, 25/09/2017] 鈥�+234 803 414 9368鈥�: 锟斤拷A DADE ANA YI....sai gaskia锟斤拷 NA BIEBEE ISA 庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Wattpad: @biebeeisa Pg1鈨�4鈨�
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169