Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 69

Chapter 69

Adade Ana Yi Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya rasa me ke mai dadi, cikin hargowa yace "Ni Hajia Mairo zata ma haka? Ni? Ni zata tozarta, wulakanta diyata da tayi be isheta ba, har sai da ta makani kotu? Lallai Hajiya Mairo da Iyalanta zasu gane shayi ruwa ne, zan tona musu asiri, zan wulakantasu, zan tozartasu" Hajiya Sayluba rai 6ace tace "bayan duk hallacin da Nana ta musu, ta so dansu tsakani da Allah, ta zabi zama dashi duk da tasan basuda komai, ta rabu damu ta bar daula ta bisu ta zauna da su cikin talauci, amma itace abun k'ulla ma sharri da mata k'azafi, bayan a yad'ata a social media, yanzu kuma an kawo mana Sammacin Kotu, kai cin fuskan yayi yawa, Daddyn Nana kar ka barsu duka". Nana na shasheka tace "Mom, Dad, ba ruwan My Majeed, Mummyn sa ne, please kar ku mai komai, ku bashi hakuri ya dawo dani, i cant live without him" ta fashe da kuka, lallashinta suka hau yi, suna bata hakurin cewa ta hakura da Majeed, ba za su iya dawo mata dashi ba, kawai suyi focusing kan Case dinsu na court kuma by all means sai sunci, don daga Lagos Alhaji Nakowa zai dauko Attorney. PH Nigeria Dadi yaji da labarin ya iso gareshi, a fili yace"The Nakowa's and The Abba's are against eachother? Intresting(da Iyalan Nakowa da na Abba suna ganin Hanjin Juna? Abu yayi dadi)" Amstrong yace "what are you planning Oga(Shirin me kakeyi?)?" Zaid ya Murmusa kawai, ba kasafai yake furta abunda yake shirin yi ba, ya fiso a ga Action kawai, a ranshi yace; 'zan bari su fafata a tsakaninsu, me kudi shike Nasara a k'asar nan, idan Alhaji Nakowa ya gama dasu Hajiya Mairo, nikuma zan cigaba daga inda na tsaya, yanda breaking dinsu ba zai min wuya ba' Amstrong ya bishi da ido, yanda Zaid ke lumshe idanuwa ya san cewa wani muguntan yake kullawa, Zaid ya san lungu da sak'on Mugunta, ya sake tambayarshi kan shirin me yakeyo, sai Zaid ya shashantar da maganar ta hanyan cewa "Get me an Appointment with Rita Phillips" da mamaki Amstrong yace "Rita Phillips why?" murmushin Mugunta Zaid yayi yace "I need me a Makeup Artiste" da mamaki Amstrong yace "Why?" Zaid ya fashe da Daria yace "Watch the Master and learn" ya zaro wayarshi ya latso wata numbern a wayarshi, ba zai iya tuna ranan da ya kirata da hannunshi ba, amma yanzu da yake bukatar hakan ya taso, dole ya kirata. * Tana kwance tana dogon tunani, anya akwai asararriya a duniyan nan kamarta? Ta banzatar da rayuwarta ta kan Namiji daya, ba don Azzikinshi ta ke sonshi ba, sonshi take tsakanin ta da Allah, tana Aji Biyu a France, da zai dawo Nigeria saboda sonshi ta bar karatun ta na chan ta dawo UNIPORT don kawai ta kasance tare dashi, gashi shi be son iskar ya debota ba, kwatakwata be bi takan ta, tana cikin wannan tunanin ne wayarta yayi ruri, kamar ba zata daga ba ta duba, ganin me kiranta ya sa ta daka wani tsalle tare da kafan wayan a kunne "Hhhello?" muryar da tafi ko wanne dadi a gurinta taji yace "Na'eelah" cike da shauk'i tace "Zaid" yace "Errhm, kin tuna lokacin da kikace idan ina son wani abu a wurinki in gaya miki?" da sauri tace "Eh, ka gaya min ko meyene, nikuma zan makashi with all my Might" ya murmusa kamar tana gabanshi yace "This is somehow complicated" tace "kar ka damu i'll do it, anything for you" ya gaya mata abunda yake so ta mishi, ta danyi jim tace "idan na maka haka zaka aureni?" kai tsaye yace mata "Aa, amma zanji dadi idan kika min hakan" taji ba dadi, ta so tace ba zata iya abun da yake so tayi ba, amma ta na son Zaid, his happiness comes first, a hankali tace "Okay, I'll do it" murmushi yayi yace "Good, comeover now" ya kashe wayar, Naeelah ta jima zaune, tana mamakin Izza da nuna isan Zaid, ita zata mishi abu amma not even a thanks, tashi tayi ta gyara jikinta ta fita don zuwa gidan Zaid. KANO Tun Sallamar Majeed daga Asibiti, suna zaune lafiya da junansu, saboda Majeed Mummy na kawar da kai bata kyara da tsangwaman Najwa, bayan idonshi tana harararta da hantararta. Tun a Asibiti Najwa bata sake bari sun kebe da Majeed ba, sai in sun hadu a Parlor, shima gaisheshi takeyi ba tare da ta kalleshi ba, saboda wani irin kunya da yanayin da takejin kanta a duk lokacin da suka ke6e da Majeed. Da daddare Zasu hadu gabaki daya su ci Abinci, Mummy ke dafawa, bak'in cikinta ta dafa Abinci Najwa taci, da ta lura Najwa bata son Kifi, sai ta dinga yin Abinci da Kifi, Najwa ko da taga Abinci da Kifi sai tak'i ci, sai tace ta k'oshi, sai Majeed yace "me kikaci? barin dafa miki Indomie" sai Mummy tayi saurin cewa "haba, barta ta dafa da kanta zata fi jin dadinshi ko Najwa?" sai ta gyada kai ta shiga Kitchen ta dafa Indomie dinta, Muhsin yace "Ya Najwa, me zai sameki in kika ci Fish?" tayi murmushi tace "I will fall sick" Muhsin ya kalli Mummy yace "Mummy, ki daina abinci da Fish, Ya Najwa will fall sick idan taci fish kinji Mummy?" duk suka kafe Mummy da ido suna jiran me zata ce, Yak'en dole tayi tace "na bari" har ran Majeed yaji dadi. A ranta ko ta aiyana sai ta sa kifi yanda Najwa ba zata gane ba taci ta ga me zai faru da ita, yarinya sai shegen Iyayi, wai bata iya cin Kifi, Washegari da rana tayi abinci da Man Kifi, ba zaka gane ba in har ba gaya ma akayi ba, sun hadu gabaki daya zasuyi lunch, two spoons kadai tayi numfashinta ya fara daukewa, Majeed ya fara lura da ita, "Najwa are you Ok?" duk hankalinsu ya dawo kanta, cikin shesheka take cewa "abin abinci, ki-fi" Majeed ya tashi da sauri ya tsiyayo juice ya bata tasha, Muhsin rai a bace yace "Mummy kinyi Abinci da kifi?" baki na rawa Mummy tayi karya tace "aa, banyi ba, da kun gani ai" "YaMaji mu tafi Asibiti" cewar Ziyada, Daddy yace "she needs a first Aid treatment" kamar zata shide ta fara magana a hankali, "FresssshTomato" Majeed yace "me kika ce?" da kyar ta maimaita, da gudu Ziyada ta shiga kitchen ta dauko Tumatir guda biyu, Majeed ya Amsa hannun Ziyada, da bakinshi ya fasa tumatirin ya kafa mata a baki, ya juye mata ruwan tumatir din a baki, ta dinga tsotsa, haka ya fasa dayan ya juye mata, a hankali a hankali numfashin ta ya fara dawowa daidai, Daddy yace "Muje Asibiti" tayi murmushi ta girgiza kai tace "i'm fine Daddy" "are you sure?" "Eh, ba wani abu, dama idan haka ya faru dani, Tomato Maama take bani, dana sha sai in dawo normal" Hajjo ta jinjina kai tace "haka fa mutum zaiji beson wannan abincin, kamar Sada, shima beson Kifi" Damm gaban Mairo ya fadi, ya akayi Hajjo ta iya furta sunan Sada?hakan na nufin ta iya tunashi? Shin Abba ma ya tuna? Kafin kowa ya fahimci abunda Hajjo tace tuni Mummy tace "bari a dafa maki

Table of Contents

Chapters

169 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});