Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 146

Chapter 146

Adade Ana Yi Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da yace ne ya nuna mata wani Gida zasu, "OK, sai na iso, a ajiye min Appreciation gift" daria yayi yace "Na Mene?" itama darian jin dadi tayi, tace "wait for it, sai nazo gida" dif ta kashe waya tana kallon Zaid da ya ke tuk'i ta mai murmushi tace "Komai yazo karshe Bhaiy" jinjina mata kai yayi cike da amincewa. ******** Suna Isa Gidan suka shiga da Sallama, Maama ta musu sannu da zuwa, ta kawo musu Abinci dining tace bari taje tayi Sallahr laasar, Abdulmajeed yayi serving dinsu Daddy da ke kan Kujerun table din, shi kuma ya dauki nashi ya koma kan carpet yana ci, Sallamar sukaji, duk suka amsa suna me kallon k'ofar shigowa, Mummy ce, kallo daya Daddy ya dauke idonshi, Abdulmajeed ya mike tsaye yana kiran "Mummy..." yanayinta ya sa sun gane tans cikin wani hali, duk da ba wai ya son k'ibarta ba, amma,amma ya san cewa ta yi rama ba kamar randa suka dawo Nigeria ba, Paapa yace "Ahh, Hajia sannu da zuwa Bismillah" zama tayi a kujera idonta fes kan Daddy, durkusawa tayi tace "Ina wuni" ganin Daddy ba amsawa zaiyi ba yasa Paapa cewa "Ina wuni, muna lafiya?" ba ta daddara ba tace "Daddy ina wuni?" dauke kai yayi kamar be san da ita ba, bata daddara ba fa, ta mike ta tako inda yake ta zube guiwa biyu a k'asa, "Daddy, DonAllah ba danni ba kayi hakuri, ka maidoni dakina, wallahi na daddara, ba zan sake ba, ka bani chance, zan gyara komai, donAllah Daddy" banza yayi da ita ya cigaba da cin Abinci. Papa zaiyi magana yaji muryan Najwa na kiransu Maama, Paapa da k'arfi, mikewa yayi da sauri yana tunanin lafia Najwa ke musu irin kiran nan, Abdulmajeed zai fita ya ga lafia, ta karaso da gudu tana murmushi tana haki, kafin ya tambayeta meya faru Zaid ya shigo cikin Parlorn, yana raba ido inda zai ga Mahaifanshi, Mairo ta kalloshi tana mamakin me ya kawo Mijin Ziyada nan? Nan ta ga Ziyada ta shigo, tace a ranta"oh ashe tare suke" ba ta damu da ta mik'e tsaye ba, ta cigaba da durkusonta. Idon Zaid ya sauka kan Dining Table inda Alhaji Abba da Alhaji Sada ke tsaye, hawaye masu zafi suka soma suntiri a idon Zaid da ya hango Mahaifinshi tsaye, da alamu shi din be ganeshi ba, takawa yakeyi da saurisauri har ya k:arasa gunsu, be ma kowa Magana ba illah rungume Paapa da yayi, riko na gaskia ya mai, shi ko Papa Murmushi yakeyi, ba wai don ya san waye wannan ba ko dalilinshi na rungumarsa ba, zai dago Zaid ya sake matseshi, su dai yan parlorn sai kallon ikon Allah suke, Najwa ta ruga daki taga Maama na Sallah, zama tayi kusa da gadon, ba zata katse mata Sallah ba, Zaid ya dawo, zai iya jira ta gama Sallah. A nan kuma Hajjo suka shigo da Zaineema kasancewar Najwa ta kirata tace "ta sa Hajjo a Napep su zo Gida yanzuyanzu". Halin da suke ciki ne ya sa ba wanda ya amsa musu Sallamarsu. Paapa ya fara kokarin raba jikinshi da na Zaid, ganin abun ya fara yawa, kuma yana jin hawayen Yaron a jikinshi, Zaid ya sake matse shi yanzu kukan harda sheshek'a, Paapa da jikinshi yayi sanyi ya bude baki yace "Bawan All--" Zaid ya katseshi da muryarshi da bai fita sosai yace "Babana" da karfi Papa ya raba jikinshi da na Zaid gabanshi na dukan uku uku ya dago ya kalle Zaid sosai, duk da idonshi a rufe yake don kika yake kamar zai shide, be hana ganeshi ba, amma don ya tabbatar ya sa hannu ya shafa idonshi, a hankali Zaid ya ware idanunshi, Papa ya girgiza kai cike da farinciki mara Misaltuwa yace "Zaidu na". Mairo ta tashi Zumbur cike da zare idona, kafafuwanta na rawa, dukkansu na gurin Mamaki ya rufe su banda Ziyada da ta san komai, Daddy kamar an dasashi yake kallon Zaid, Sake Rungumar Juna sukayi Zaid yace "Baba, ashe kuna da rai? Ashe zan sake ganinku? Ina Mamana?" Papa ya rik'e hannun Zaid ya bude baki "YESMEENAH" daga chan daki Najwa tace "tana Sallah" Zaid ji yayi kamar ya ruga dakij ya katse mata Sallahr amma sai ya tausashi zuciyanshi da ya barta tayi Sallahrta su kasance tare. Paapa murna yace "Zaid aka ce ka mutu, amma ga ka nan, Me ya faru?" Idonshi ya sauka a kan Mairo, wata jijiyan saman kanshi ta mike tsaye, be son ganinta ko na sakwan daya runtse ido yayi yace "Baba, nima a zatona kun mutu, bansan kuna da rai ba, da ban bata lokaci ko daya a nan ba, da na biku chan Indian" Papa da murna yace "Komai sai da ikon Allah, Zaid ga Yayana, Baba Abba sunanshi, ga--" Zaid ya katseshi da cewa "Na san su, na san su duka" Paapa yace "Dagaske?" Daddy cikin sanyin Jiki yace "shine Mijin Ziyada ne, Gatan Marayu na ii" Papa yace "Allahu Akbar its a small world after all, amma duk ta kare be san yanda kuke dashi ba " Zaid ya runtse ido cikin wani yanayi yace "nasan Komai Baba, nasan komai" Da mamaki Abdulmajeed da kowa na Parlorn suke kallon Zaid, wato abunda ya ma Mairo kwanakin da suka wuce yana sane kenan, Daddy ya jinjina kai yace "Zaid kayi hakuri da yanda ka tsinci rayuwarka, ka ga wanchan Matar?" ya karashe yana nuna Mairo da yatsa, ita ko ta sadda kai irin na marasa gaskia. "Itace ta shiga tsakanin ka da Mahaifanka, wanchan matar Ibilisun dunia ce" * "Yadai Najwa?" cewar Maama da ta dago ta kalleta bayan ta sallame Sallahr, Najwa cike da murna tace "Maama guess what?" tace "Najwa, gaya min, menene?" "tashi muje, Bhaiyya na parlo" ta dan zabura "Najwa me kike nufi? Bangane ba" Najwa ta mike tsaye ta kamo Maama ta tadata tsaye tace "Your Son Zaid is not Dead. he's here(Danki Zaid be mutu ba, ya na nan) " yi tayi kamar zata fadi, Najwa tayi saurin kamota, tace "Maama, relax, i promised you i'd find him and i did(Maama, ki kwantar, alkawari na maki zan nemoshi, kuma nayi)" dabas ta zauna kan Gado gabanta na dukan uku uku, tsoro takeji, bata san dalili ba, kar hakan na cikin mafarke mafarken da na ta saba na haduwanta da Zaid, bata son hakan ya kasance ba gaskia ba, tana so ta ga Danta, tana so ta taba shi, tana so ta jishi a jikinta, tuni hawaye suka soma sunturi a kan fuskarta. Najwa tace "Maama tashi muje, yana parlo" kamar an sa mata battery, ta mike da sauri tana gaba Najwa na binta a baya, burinta kawai ta ga danta, duk girmanshi sai ta rungumeshi. *** Zaid ya dan yi dariar takaici "Ni ko zan gaya maka wacece Hajia Mairo, Matar da bata damu da damuwar kowa ba sai tata, Matar da 'yayan wasu ba 'yaya bane sai nata, da kunena naji kawarta na bata shawaran ta kasheni sabida zan girma na zamar mata threat, saboda kar wata rana nace komai nawa ne, Wallahi ta yi niyyan kasheni da na tsaya, ko ba ita ba, zata sa a kasheni, sabods abun dunia? She made me a monster, ta

Table of Contents

Chapters

169 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});