Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 116

Chapter 116

Adade Ana Yi Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

baki tashi zaune kin bar Kukan nan ba, zan ma Ya Gidanku abunda ya fi na yau" da sauri ta tashi zaune tana sharar hawaye tana girgiza kanta "DonAllah kar ka musu Komai, na tashi" a wulakance ya kalleta ya watsar, ya fita daga dakin. Komawa nashi dakin yayi ya zauna, ba wai kukan ne ke damunshi ba fa, kawai ta cika mai kunni da ihu ne, be son damuwa, wayarshi ya dauka yana Waya. Tunda suka iso Unguwar suka hango Motan Jamian tsaro a gaban Gidan, Daddy ya kalli AbdulMajeed, suka karasa garesu da Sallama, musulmin cikin ne ya amsa, Daddy yace "munzo ganin MaiGidan ne" yace "to ku kirashi a waya" AbdulMajeed yace "kuce mai Mahaifi da Wan Matarshi ne" yace "Aa ai ku zaku kirashi kuce mai kuna Kofar Gida, mu ba ruwanmu, Aikinmu shine hana fita da fice a gidan nan, ko waye yazo, dazun ma dan shi yace a bar Mamarta ta shiga shiyasa aka barta, amma da ba haka ba" Daddy yace "ku taimaka ku sanar dashi zuwanmu" nan sukayi biris da lamarin, Wayarshi Daddy ya ciro don kiran Alhaji Ado ya sanar da shi halin da ake ciki, amma wayarsa Kashe(kasancewar ya bar kasar). Sun kusa Awa Biyu a kofar Gidan, ganin mutanen nan ba wani tausayi ko imani tattare da su yasa Daddy Lallaba AbdulMajeed kan su tafi, ba don ya so ba su ka tsaida Adaidaita suka bar Unguwar. Bayan Maghrib Ganin kuka ba zai fissheta ba ya sa ta tashi ta fada wanka, tayi alwalan maghrib kafin ta fito ta shafa mayyukan da ke gaban dressing mirror dinta, bude daya daga cikin Akwatinan da Anty Taatuh ta shigo dasu a ranar da aka kawota tayi, bata taba budewa ba sai yau, dama ina kwanciyan hankalin dubawa, Akwatin cike yake da dogayen riguna, da kananun kaya irin na matan turawan nan, ta bi wata riga聽 navy blue color me torches din re da kallo, ta dauka ta daga ta na duba tsawon jikin Madubin Wardrobe dinta, iyakar rigar guiwarta, hannun dan guntu ne, ta ina zata fara sa rigar nan? Ai da kunya, ta ma saka taje wurinshi ya wulakanta ta? Amma fa na zaiyiwu su cigaba da zama haka ba har karshen rayuwarsu, dole ita zata kokarta wurin karkato hankalin Mijinta gareta duk da ba abu bane me sauki, ta kan gani a littafan hausa Mazaje masu tsaurin raayi, ta hakan ake shawo kan wasu, tasan this is reality, amma zata gwada ko Allah ya sa ta dace, tana son Mijinta, kuma zata iya hakuri dashi in dai har zasu zauna lafiya. Saka rigar tayi ta daura zani a kai tayi sallahr Maghriba, tana kan dardumarta taji kiran Sallahn Isha'i, ta tashi tayi Sallahr ishai, ta hada da shafa'i da wutir, ta zauna tana jera ma Allah Kirari, tana adduar Allah ya kawo karshen komi ya basu zaman lafiya da Mijinta, Allah kuma ya kwabe Fitina tsakaninsu, a karshe kuma ta kara da Allah ya daidaita tsakanin su" ta shafa. Ta mike ta linke hijab da zanin da tayi sallah. Ta sake shafe jikinta da turarruka masu k'amshi ta gyara fuskarta, dan jambaki ta zizara a baki, ta sake kallon kanta a mirror, sosai rigar yabi jikinta, ita ta san tana da kyau, ko da bata shafa jambaki ba, ina ga ta shafa. Sai da ta shiga Kitchen ta dafo ruwan zafi聽 da kayan shayin da ta gani a wajen, bayan ya tafasa ta sa a wani Jug me kyau, ta dauko saucer kalan jug din ta hada mai, ta dauko tayi dankin Oga. Nan gabanta ya fadi da ta tuno wurin wanda zata je, jiki na rawa ta fita daga dakinta, tana karanto adduar shiga gida bismillahi walajna.. Bata san ko ya dace ta karanta shi ba ita dai ta karanta, ta murda k'ofan da Sallama. * Ko Darduman da ya idar da Sallah be ninke ba ya hau kan Gado yana Waya, inda aka kirashi daga Maaikatarsa ta Bauchi, wai ana bukatar shi a Maaikatar saboda wasu clients da suka samu daga London, karamin tsaki yayi yace "kuma dole sai ni? Ba gaka ba? Or Zan turo Faisal" Cike da ladabi mutumin yace "Oga sai dai kayi hakuri, sunyi insisting sai sunga CEO din company din ne" Zaid ya buga tsaki yace "matsalarsu, in representative dina ba zaiyi tending dinsu ba, they should forget it" yace "Oga, zaiyi causing dinmu Millions of Pounds" Zaid cikin daga Murya yace "I dont care" Manager ya kwantar da kai yace "this is the Company your Dad spent his time and energy Building, ba zaka sa muyi asarar nan ba" Zaid ya rintse Ido ya bude ya sauke su kan Ziyada da ta shigo yanzun da Sallama hannunta rike da tray, kallonta yakeyi kallon kurilla, be san me yakr tunani ba, ji yayi Manager na cewa "Oga, are you there?" cikin sanyin murya Zaid yace "Yes i'll see you Tomorrow" ya kashe waya ya mik'e tsaye ya na kallon Ziyada, kallo yake binta da shi, kallon da be san na menene ba, takawa yakeyi a hankali har yazo gabanta, sansanyar murmushi take binshi dashi, tana murnan Zaid ya fara dawowa kan hanya. Ba ta ankara ba sai jin wani irin Zafin da bata taba sanin akwai irinshi ba akan kafarta, wani tsalle tayi ta ja baya, sai a sannan take jin muryan Zaid na cewa "kar ki sake shigo min daki, dan gulma harda hado min Tea, waya san irin Asirin da ke ciki? Da da ki ka kawo ni kike son na sha? Ki kara gobe a jiki zan watsa miki, sai sannan ta lura da ba sakin Jug din tayi ya fadi a kasa ba, shi Zaid din ne ya dauka ya kwarara mata a k'afa, murmushin takaici tayi ta share hawayen da ke fuskarta ta kalleshi da jajjayen idanunta tace "Ba a horo da Wuta Zaid" ta ajiye tray din kan wani drawer da ke gun, ta fita daga dakin da gudu, binta yayi da wani irin kallon da be san na meye ba. Toilet ta nufa ta sake ma kafarta ruwan sanyi, tun daga guiwanta har kasan kafafunta, kuka take me taba zuciya ganin yanda kafar tayi Ja, tasan in ta shafa ko ta sosa kafar zai tashi ya ja ruwa, kuka take tayi, bata da abunyi da ya wuce ta zuba ma wurin ruwa, akwai radadi, ta dau lokaci me yawa a toilet kafin ta fito ta cire rigar jikinta ta saka Nightgown, ta kuddura a ranta, in Allah yayi duniya don Manzo ta fita harkan Zaid kenan, Allahn da ya jarrabeta da sonshi shi zai yaye mata" tana jin zafi ta hau Gado ta kwanciyarta tare da jan bargo a jikinta, tun tana kuka har bata san Lokacin da bacci barawo ya saceta ba. *** 2:35am *"ZAID" yaji wata kakausar murya na kiranshi, ya dago ya kalli fuskar a razane, fuskar da ba zai taba mantawa bane, fuskar Babanshi , Gatanshi, baki na rawa yace "Baba" cikin tsawa yace "kar ka sake ka kirani da wannan sunan, ni ba Babanka bane, ban taba haihuwa ba, banda da, dana sani na barka a inda na tsinceka, da na sani, da ban baka duk wani jin dadi na

Table of Contents

Chapters

169 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});