Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 79

Chapter 79

Adade Ana Yi Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

cike da mamaki wai yau ita Abba Abu ke ba umarni har wani tafarfasa yake kamar d'anyar ganda. Daddy yace "nikam Maryam yaushe zakiyi hankali ki gane jiya ba yau bane? Maryam ki ma kanki fada? Kinsan wani irin danyen aiki kika baro mana kuwa? Wa ke takara da Nakowa? Wani me hankalin ne? Wato ke duk abunda ranki ya aiyana miki shi kikeyi ko? Ni da gidan nan bani da ikon sanin meke wakana a ciki? Sai da ta baci nakeji, Wallahi Maryam ki kiyayeni, ki fita idona". Ta inda daddy yake shiga ba tanan yake fita ba yana kai aya ya mike a fusace ya nufi bedroom dinsu. Tsoro ya darsu a Zuciyar Mairo, ko a shekarun baya da yake mata fada be mata irin wannan ba, sosai ta tsorata, k'aryarta ta k'are, things are falling apart, tunani kala kala a kwanyar kanta, saboda tsabar mamaki ko yatsunta kasa dagawa tayi balle ta iya cewa wani abun. Yanda taga Rana haka ta ga dare, kwatakwata bacci kauracewa Idanunta yayi, Abubuwa kala a ranta, ta kasa gane dalilin da ya chanza Daddy dare guda, Lallai reshe ya juya da Majuyi, wai yau ita Daddy ke daga ma Murya, har ya kirata da Sakarya,Tabbas dole ta tashi tsaye ta san abun yi tun kan dare ya mata, a dayan Bangaren karon farko da tsoron Haduwarta da Nakowa ya darsu a Zuciyarta, Daddy duk ya ruguza mata lissafi, bata san ya zata kaya ba, a kan Idonta aka kira Assalatu. ******* Sosai ta firgita da taji abinda ake so ta fada a Kotu, ta kalli Dad da Mom kafin ta kai dubanta ga Attorney dinsu, tace "Amma ba haka bane ba fa, ni da kaina na dauki Credentials din nan, na kai ma wani a waje, ya za kuce ince bansan da zancen ba?" Mom ta hau lallashinta tace "ita sam ba zata karyata Majeed ba" Dad yace "Nana, do you want to rot in Jail? In ba haka kikayi ba, za a saka ki a Prison kuma i cant save you, ina so ki ba Attorney Hadin Kai, zan sa a nemo mishi Credentials dinshi, zan bashi aiki, kuma zan rokeshi ya maidaki dakin ki, that is in munyi winning case din, others ba zaki koma dakinshi ba, kuma zaa kulle ki maybe life imprisonment" Sosai ta tsorata, bata son haka ya faru, bata son zama part of any of this, kawai tana so ta koma wurin Majeed dinta, a wuce gurin, a haka Dad dinta ya dinga dorata, da kyar da sudin goshi ta amince zatayi abunda suke so, haka aka dinga karanto mata Irin Shaidar da zata bada a Court Gobe. (Anzo gurin,daidai gurin, who is excited? Ghen ghen) KOTU Kotu ta cika ta batse da jama'a, kowa da zaman da yazo saurara, mafi akasari manyan Mutane ne abokan Huldan Hajia Mairo Da Alhaji Nakowa, kowa ya hallara, Nana ta k'i yarda ta kalli inda su Majeed ke kallo, a ka gabatar da Shari'ah, Ba tare da bata lokaci ba Alkali ya umurci Lauyan masu kara da ya gabatar da Majeed a gaban Kotu. Majeed ya fito jiki ba kwari, yau ko Breakfast beyi ba, tsayawa yayi inda aka tanada domin bada Shaida. Lauyan Alhaji Nakowa ya nemi da abasa izini ya yiwa Majeed tambayoyi, nan take Kotu ta bashi dama. Lauya Usman Baraji Me kare wadda ake k'ara ya fara jefa masa tambayoyi kamar haka: "Ko zaka iya fadawa kotu Sunanka, inda kake zaune da kuma Sana'ar ka? Jim Majeed yayi kafin yace, "Sunana AbdulMajeed Abba Abu, ni mazaunin garin Kano ne, a halin yanzu bana aiki Amma ni Architect ne". "Mallam AbdulMajeed shin menene Alakar ka da Wacce ake kara?". Majeed ya hadiye miyau din takaici kafin ya amsa da; "Matata ce a da amma yanzu babu aure a tsakanin mu, ba ma tare". Lawyer ya sake jefo mai tambaya"Wacce take k'arar fa ko menene Alakar ka da ita?" A takaice yace"Mahaifiya ta ce". Barrister Usman Baraji ya karanto ma Majeed k'arar da Mahaifiyarshi tayi ya tambayeshi "Mallam AbdulMajeed muna so ka gaya ma Kotu, shin wannan bayani da na maka haka yake?". "Eh ya mai sharia haka abun yake, babu tangarda a bayanan da mahaifiyata ta ba ma Kotu". Barrister Usman Baraji yace "tsakani ga Allah kaga Lokacin da Nana Nakowa ta daukan maka Credentials ta ba ma wani?" Majeed yace "Aa bangani da ido na ba, amma da bakinta tace ita ta dauka". Barrister yace "tambayar itace Kaga Lokacin da ta dauka da Idonka?" Majeed ya hadiye miyau yace "Aa bangani ba" Barrister yace "Kaji Audion da ake ikirarin tayi a cikin Maye?" Majeed yace "Eh da kunne na naji". "Mallam AbdulMajeed Kotu tagode da wannan shaidar da ka bayar zaka ka iya zuwa ka zauna har sai an sake buk'atar ka." Yayi Godia ya juya ga Mazauninshi. Barr ya maida dubanshi ga Alk'ali yace " Ya Mai girma Mai sharia, a report din da muka samu, sun nuna mana tambayarta yayi wata ba ma Takardunshi, k'ilan ta tsorata da wani abu ne ta amsa abunda ba tayi ba, sannan kuma maganar Audio dinnan, muna so a sanya ma Kotu taji, Nagode Ya Mai girma Mai sharia ". Alkali ya juya kan Lauyan Mairo ya umarce sa da ya gabatar da shaidunsa. Lauyan Mairo ya mike cike da isa ya ce "Ya Mai Sharia, Shaidar mu Kenan AbdulMajeed, kuma ya bamu tashi Shaidar, shikenan shaidan da mu ke da". Cikin zafin rai Mairo tace "wani irin shikenan Barrister Khalim? Ina audion? Ka musu Playing". "Wani Audio kenan Hajiya"? "Kutumar Babba burauba! yau akeyin ta, Bar khalim bansan wasan banza dana wofi, Audion da na tura maka lokacin da nazo Office dinka, nace maka Alhaji Nakowa ya sa anyi Attacking Aliyu Abokin Majeed an goge Audion, don kar a samu matsala na zo har Ofishinka na tura maka?" Barrister Khalim yace "Aa Hajia Mairo, i dont know what you are talking About, ni baki turo min ko wani Audio ba". Wani tsallen da Hajia Mairo tayi sai da ta chakumo wuyan Barrister Khalim, tace " Ni zaka mayar 'yar iska? Kaika Nakowan ya sayeka ko? To wallahi baka isa ka mayar dani mak'aryaciya ba" Alkali ya tsawatar ma Mairo, yace "ta yi taka tsantsan da yanda take gabatar da kanta a gaban Kotu, Kotu ba zata dauki wulakanci da shashancin banza, Kotu ta ma Mairo gargadi da Babban Murya. Mummy tace " Ayi Hakuri Ya Mai Sharia, raina ne ya baci, amma ba matsala in shi ya sayar da Audion, ni ban sayar da nawa ba, yana nan cikin Wayata" Alkali yace "ta gabatar da Audion gaban Kotu" da Murmushi tace "Minti daya" ta koma gun zamanta ta bude Jakarta ta ciro Wayarta ta hau latselatse, kusan mintina 5 shiru, take zufa ya hau ketowa Mairo audio dinnan ko sama ko kasa ta rasa shi a wayarta. Da sauri ta kalli direction din da Alhaji Nakowa yake, watsowa mata mairo murmushin mugunta yayi, zufa ya shiga keto mata, ta san k'aryarta ta k'are, a hankali tace "Yau ake yinta" wurin Barrister Khalim ta nufa, tace "Bar Khalim kai wa girman Allah ka bada audio dinnan, kayi hakuri, i'll pay twice what they paid you". Barrister

Table of Contents

Chapters

169 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});