Chapter 38
Chapter 38
zama ne na wani dan lokaci " Hajia Aliya tace "toufa, karayar Azziki kukayi? Don na tuna kince ke da Kano sai hutu" Mairo ta dan daburce "habadai karayar Azziki, kawai yara ne suke son Zaman nan, na Majeed yace Zaman barikin ya ishe shi haka, kuma kinsan zan iya komai don Yara na". Hajia Aliyah ta gyada kai bawai don ta yarda da bayanin Mairo ba, da Mairo taga shirun yayi yawa sai tace "Kawata, donAllah taya zanyi in karkato zuciyan Yaron wani k'usa a k'asar nan zuwa ga Ziyada da Zaineema?" Hajia Aliyah ta katse ta da cewan "Zaineema ta fito ne?" Mairo tace "Aa, Mijinta ya rasu ne" "Ayyah, Allah ji k'anshi". Mairo ba ta son raini, bata son abunda zaayi ta surutu dashi a kanta da kuma yaranta, Balle In Hajiya Aliya Kunnen gari tahi, to kowa ma sai yaji, haka zata zama abun zunde da nune cikin kawayensu. " Ai abu mai sauk'i ne Hajia, kudi zaki sake Sosai, na kaiki gun Na kan tundu, wanu sabon shigowa ne ya na nan, aikinshi kamar yankan wuk'a", "Allah ko Kawata? Suka chafe, Hajiya Aliya tace " Amma fa yana da Tsadar aiki, don daga aikin Miliyan daya sama yakeyi" gaban Mairo ya fadi, ina zata samo kudadden nan? Muryan Hajiya Aliya taji tana cewa "Aff! Na manta ku manya ne, ba ku da matsalar kudi". Yak'e dai Hajia Mairo keyi tace "idan ta shirya zatayi mata magana ta rakata". * "Mummy, ko shekara dari zanyi a matsayin bazawara, ba zan aura kowa ba, zan jira Khaleed ya dawo min, zan jira shi ya dawo gareni, i'll wait forever for him". Hajia Mairo ta girgiza kai, tace "Zaineema, please" Zaineema ta katse Mummy da cewa "Wallahi idan kika matsa min da Zancen Auren wani to Wallahi zan shiga duniya, Jahilci ne ma wannan ina Iddah ki fara min zancen Aure" Mairo tayi saurin cewa yi hakuri Zaineema abun be kai nan ba". Sum sum ta tashi ta fice ta bar Zaineema a daki. Mairo ta shiga damuwa sosai,ta hade kai da guiwa tana tunanin yanda duk abunda ta Gina ke falling apart,bata ankara ba sai ganin Nana tayi ta fito daga dakinsu janye da dan trolly, ta sa mukulli ta rufe dakin tare da jefa mukullin Jaka, Sanye cikin wasu riga da skirt damammu, sai gyalen da be wuce girman Jallabiya ba, Mairo da murmushi tace "Nana,kin fito?" ba tare da gaisuwa ba tace "Eh Mummy, Jigawa zanje tare da friends dina, my Majeed baya nan, i dont want to miss him, shiyasa zanje in dan huta kafin ya dawo daga Abuja" bata jira cewar Mummy ba ta wuceta, ita ko Mairo ta bita da ido, tayi amanna AbdulMajid be san da tafiyar nan ba, ya san da ya sani da jiya kafin su wuce Abuja da Ziyada da ya sanar da ita tafiyan Nana,mamakin Shiga irin ta Nana takeyi, ita tasan ba ta damu da shigar kowa ba, amma wannan Shiga ta Nana sam bata yi kama da ta ma su aure ba, wannan shiga ta nana yafi kama da na Goggagun 'yan bariki. meke samun su ne haka? A baiyane tace "Meke faruwa da Rayuwar mu?". PH Ng "Zaid please, ya kake so inyi? Son ka zai kasheni, meyasa ka za6i ka wulak'anta ni, da kyauna da ajina da kudina? Tun France nake ta bibiyarka, saboda kai na dawo PH uni don kawai na kasance tare da kai, na watsar da rayuwar daulan da nake ciki don kai, Zaid meyasa kake min haka?". In Bangon dake jikin dakin ya amsa maganar da Nadiya tayi to Zaid ya amsa, kamar Allah beyi hallita a wurin ba, sam ko kallonta baya yi, harkan gabanshi kawai yakeyi,yana latsa Laptop inda yake karanta reports din da aka turo mai a Kano da Abuja, inda ya ga Majeed ya dawo da Ziyada Makaranta zata zauna a hostel har su gama exams next upper week,sai kuma Ganinshi da akayi a Dubai Embassy, Sannan tafiyar da Nana tayi Jigawa, Kallo daya Zaid ya ma Nana ya buga tsaki da k'arfi yace "yarinyar nan zata rusa min shiri fa" Nadiya rai 6ace ta rufe Laptop din, tace "haba Zaid, ina nan tsaye ina maka magana, hankalin ka na wuri wata 'yariska?" ran Zaid ya 6aci, shiyasa baya son mata, ba su iya komai ba sai distraction, ba ya son ayi distracting dinshi, rai a 6ace ya kalleta yace "bana son ana distracting dina, tunda kika zo kike distracting dina, i dont remember inviting you, banason warin jikinki, bana son kallon fuskanki" ido cike da hawaye tace "Zaid, me kake nufi?" a tak'aice yace "a sauk'ak'e-- Fita" tace "What?" a dakile yace "i wont repeat myself" fizgar jakkanta tayi hanyar k'ofa tana a"You'll regret this" murmushin gefen baki yayi ya bude laptop din yana tunanin yanda zai 6ullo ma Nana, don in bebi sannu ba, Asirin Nana zai tonu, Majeed ya saketa, ita kuma bata mai aikin da yake so tayi ba, wanda shine dalilin da ya sa yayi sandaiyar Auren Nana da Majeed, to wai me Majeed yaje yi a UAE Embassy? Ko tafiya zaiyi? Yana son sanin ina zaije. Bari dai ya kira Nana nan, daga bakinta zaiji Komai, Wayarshi ya dauko ya latsa numbern Nana, sai da ya mata missed calls uku kafin ta dauka da tsawa "wai wani daniskan ne yake kirana" cikin muryan shi yace "daniskan da ya koya miki yanda zaki sa Majeed Aurenki" tsaf ta ganeshi, to me yake so kuma, tunda kwalliya ta biya kudin sabulu ai bata da sauran bussiness dashi, tace "to ya akayi ne?" ya murmusa yace "Me Majeed zai jeyi Dubai?" tace "huff, mesa zan gaya ma sirrin Mijina?" yace "saboda nace ki gaya min, kar ki manta ni nayi sanadiyar aurenku, lokaci daya zan rusashi" tsaki tayi tace "you are very stupid, ba kai ka sa ya Aureni ba, kar ka kara kirana, Stupid" ta kashe wayar tana huci, waye wannan? Me ya dauki kanshi da zai dinga kiranta yana sata abubuwa ko tambayarta abubuwa?. Wayarta ya sake kira, da tsawa ta dauka da niyyar cimai mutunci, muryan nan dai ne, yace "Nana Nakowa, you'll apologise to me,ba a min ihu, ba a daga min murya, ba a zagina,apologise for calling me stupid, and finally ki gaya min mai Majeed zaije yi Dubai, i wont ask again". Tayi daria tace " i like your confidence, so ka matseni ka sani in fada maka" yayi murmushi yace "ba zan matseki ba, da kanki zaki gaya min, or maybe zaki ba Nimcy ko Salim su fada min". A firgice Nana ta kalli Nimcy da Salim din dake kan Gado suna aikata Alfasha, baki na rawa tace "ina ka sansu?" yayi daria yace "kina nufin ina na san Kwarton ki? Da dadironki Nimcy, duk Kano be isheki ba ke da Salim sai da kukazo Jigawa wurin Nimcy?, what will happen if Majeed gets to know his Wife is a hypocritical b*itch Ehh?". Da sauri tace "No,No, donAllah kayi hakuri,don't tell him, Zan gaya ma all you want to know". "Good, ina jinki" tace "Majeed zaije yin wani Interview ne a HILAL Construction Company on Monday, shine yazo Abuja neman Visa" Zaid ya jinjina kai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169