Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 11

Chapter 11

Adade Ana Yi Book 1 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wasa, da gudu ta dauko Zani ta nufo Zaid dashi, da yake itama sosai take son Zaid, cikin gwarancinta take cewa "Zaid, Zaid ka min babu" tashi yayi daga wasan da sukeyi da AbdulMajid, yace "Zo in goyaki" AbdulMajid yace "danAllah kazo mu cigaba da wasan mu, Zaineema kai ma Mama zanin ta goyaki" Ina Zaid beji ba, ya durk'usa ta hau ya zo daura zani kenan Zaineema ta subuce mishi ta fadi gwaram a k'asa, wani irin Ihu tayi wanda da ta ja ihun, sai da tayi seconds kafin ta sake shi, Zaid tuni ya kidime, nan da nan ya fara kuka, AbdulMajid yayi saurin zuwa ya dagota, yana cewa "sai da nace miki kije Mama ta goyaki,yi shiru" ina sam Yarinya ba tayi shiru ba, ihu takeyi sosai. Zaid ya kasa motsi, kuka yakeyi yana bin AbdulMajid a baya suka yi cikin Gida, daga ciki Mairo taji kukan Zaineema, da gudu ta fito, mai ya faru? AbdulMajid yace "Faduwa sukayi da Zaid" ba ta tsaya jin meye ba'asin ba ta hau Xaid da duka, duka bana wasa ba, dukan da ko kai babba akayi ma irinshi sai kaji jiki, balle yaro dan shekara 9, AbdulMajid ya dire Zaineema k'asa yaje yana kama hannun Mamanshi, saidai ta hankade shi, kuka sosai sukeyi duka su ukun, Zaid yana ta kuka har muryanshi ya dishe, kiyi hakuri "Mama, ba zan sake daukanta ba" ina Mairo bata bar dukanshi ba, duk fushi,kishi, jin zafi, hassada, da bak'incikin Yesmin da Sada da ta ke ta fa dashi fiye da shekaru goma, Mairo ta fanshe shi a jikin Zaid yau. "Kashe min ita zakayi? Eyi?in ta mutu ya zakayi? Zaka iya biyana? Ko an gaya maka juyar uwarka zata iya haifa man wata?(Tun bayan Zaid, Yesmeen ko 6atan wata bata sakeyi ba, Mairo ko kafin Zaineema, 6arinta 3, sa ma kanta damuwa da hassadar Yesmin ke barar da cikin). Kamar daga Sama, Allah ya jefo Alhaji Abba, da alamu duk maganganunta a kunenshi, da gudu yaje don ceton Zaid, harda Mari lafiyayye ya ba Mairo, a razane ta kalleshi, yace "ba tun yau ba na san kin tsana Zaid, ko me ya miki wannan dukan yafi k'arfin shi, Allah zai saka mai" ya dauki Zaid ya sa6eshi a kafada, yayi lamo jikin Baba Abba, yana kuka a hankali, AbdulMajid na kuka ya bi Babanshi a baya. Bakinciki ya turnik'e Mairo, itama daukar Zaineema tayi tana mulmula mata goshinta da ya dan kumbura, amma har yanzu bata daina kiran "Zaid ba". Gidan Hajjo Baba Abba ya wuce dasu don chan ya baro Yesmin, a Mota AbdulMajid ya gaya mai abunda ya faru, girgiza kai yayi yace "Mairo akwai Azzaluma, kayi hakuri Zaid Allah zai saka maka" yanda ya shiga da Zaid a hannu ne ya sa Yesmin faduwar Gaba, Alhaji Sada na nan shima zuwanshi kenan daukan Yesmin. A tsorace suke su duka 3, Hajjo tace "lafiya? Me ya samu Zaid din?" karaf AbdulMajid yace "Mamanmu ce ta dukeshi don sun fadi da Zaineema" Yesmin ta kawar da kai don jin ba'asin dukan, ba tun yau ba ta ke lallashin shi kan hakuri da daukan Zaineema sai ya girma, amma bayaji, rai a bace Hajjo tace "sai ta bugeshi? Da gangan zai kadata ne? Meyasa Mairo bata da tausayine? Anya kuwa Abba, anya nan gaba zaa je gidanka?". Zuciyar Sada duk ba dadi yace " Aa Umma, ai laifi yayi, don ta hukuntashi ba wani abu bane, shima ina shi ina daukan Zaineema" Alhaji Abba yace "Sada Maryam bata da kirki, hakuri na ya k'are, wallahi nagaji da ita, ta maidani sakaran Namiji, don taga ina mata shiru-shiru, zan sauwak'e mata gaskia". Hajjo tace " ka sawwak'e mata, tayi hankali" da Sauri Sada yace " Aa danAllah, hakurin zaka cigaba da yi, da Nasiha da lallami zata daina InshaAllah " Hajjo ta kumbura tayi fam ba tace komai ba. Sada ya da cigaba da bashi baki har ya hak'ura,聽 kafin yace da Yesmin "Ki shafe shi da Robb, ai sai ku tashi ku tafi kafin Maghrib yayi, AbdulMajid mu tafi gida" Abdul ya mak'e kafada Alhaji Abba ya gane nufinshi, cikin bacin rai yace"zaka zo mu wuce ko sai na sa6a ma" Alhaji Sada yace "kasan dai ba zai yarda ba ko, kai dai kawai ka tafi". Bayan komawarsu Gida, Yesmin ta dafa ruwan zafi, ta ma Zaid wanka dashi, lokaci zuwa lokaci yake sakin Ajiyar Zuciya, duk shattin hannuwan Mairo a jar fatarshi, muryarsa a dishe yace "Maama, ki haifa min jaririya kinji? Ba zan kada miki ita k'asa ba" wani kuka ya kubce mata, ta rungume danta, tana tausaya mai, tana tausaya ma kanta, ta son Mairo bata sonta bata son danta, Mairo na kishi da ita, Kishin Sauri wanda hausawa kece ma yafi Kishin kishoyoyi masu auren Miji daya Zafi (Kishin sauri:Kishin da Matan 'yanuwa{Matan Ya da Matan K'ani} ke yi da junansu). 聽 聽 聽 聽 聽 聽聽 BAYAN聽 SHEKARA DAYA Alhaji Sada Abu mutum ne mai Amana da Gaskia,ga aiki da kwazo ba Ha'inci, Alheririkan Allah sai samunshi suke tayi ta k'ofofi da dama,baya ganin k'yashi yake taimaka ma gajiyayyu, duk mai ya ta6a Allah na dafa mishi. Alhaji Abba na aiki a wani board na Trust fund wanda samun aiki a gurin sai kana da mai maka Alfarma, Alhaji Sada ya sama mishi aiki gun, don yana da connections da yawa. 聽Bayan聽 gama Primary dinsu Abdulmajid, Alhaji Sada ya saka su a secondary boarding, makaranta ce mai ji da kanshi kuma sai dan wane da wane ke ciki wato HASSAN IBRAHIM GWARZO, yanzu haka suna chan JSS1 komai dinsu daya. Cikin Abubuwan Alherin da Alhaji Sada ya samu a shekarar nan sun k'unsa da Tamfatsetsen gidanshi da ya gama ginawa a hotoro, Gida ne Wakeke, wanda zaa iya ginin gida uku ciki,randa ya gama Ginin, rannan Ya Mallaka ma Alhaji Abu gidan ya tashi daga ciki, bayan ya mai gyaregyare duk da ba wani abun da ya samu gidan don du du gidan be wuce shekara 6 ba. Sannan ya siya Shaguna 5 a bakin Titi ya rushe su ya Gina k'aton Shago inda zai zuba kayan Kafintoci, Shawara yayi da Abba na yana son Fita k'asar waje inda zai Siyo kayan aikin Kafinta, da kattakon su, ya zuba a shagon" nan da nan Abba ya bashi goyon baya na cewa ya tafi Italy su ke da irin kayyayakin nan, kuma ya bashi shawara ya tafi da Yesmin suna dawowa kawai sai su wuce sabon Gida, Sada ya Amince da batun Abba ko da ya gaya ma Hajjo ta sa ma abun Albarka, Yesmin ta ji dadi sosai, zata fita kasar waje, duk da tana zuwa Makka. A ranar da Mairo taji cewa Yesmin zata tafi k'asar waje, Ihu ta saka don ji take kamar tayi hauka, kasa boye bakincikinta yayi har Abba na mata dariar mugunta yace "ba yanda zakiyi uwar Hassada, haka zaki ta kallo har zuciyar ki ta fashe". 聽聽 Haka sukaje K'asar Italy sukayi sati biyu kafin sukayi sarin abubuwan da suka kaisu aka turo ta Ship, tsaraba sosai tayi ma Zaid da Abdul komai iri daya, daga Italy suka wuce Makka sukayi Umra kafin suka dawo Nigeria kai tsaye Sabon Gida suka tare. Washegari

Table of Contents

Chapters

169 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});