Chapter 17
Chapter 17
zaka barni da na nema aikin" kallonta yayi sosai sonta na shigar shi, yace "Anything for you, in har zaa dace, zan amince ki fara aiki" da sauri ta rungume shi tana murna". Fita Sada yayi yace bari ya nemo wanda zasu tayashi gyaran Gida, Yana fita ya ga wasu yara na wasan k'wallo, da hannu ya ya fitosu, su biyu ne maza matasa ba zasu wuce shekaru 18 ba, dama sunga wucewarsu a Motan Vikash sir, sun san sabbin shiga ne, Sada yace "I want you to help me clean my house?" duk sukayi daria, dayan yace "No English, Hindi , Hindi" Sada ya dafe kai ya ja hannunsu suka shiga Gidan, ya musu nuni da su gyara gidan, Wanda ya fi dan wayewan yace "Sweeping?" da sauri Sada ya daga kai yace "Yes sweeping" dayan da ya lura ba indiyawa bane, ya girgiza kai yace ma dayan "su tafi kawai yan pakistani ne, musulmai ne, su tafi kar su taya su komai" dayan ya girgiza kai yace "ba wani abu su tayasu kawai" dayan ya girgiza kai ya wuce ya bar dayan a ciki, dayan ya kalli su Yesmin yace聽 "Ek Minute" ya fita, Sada ya kalli Yesmin yace "toufa, me hakan ke nufi?" Yesmin tace na daiji wannan yace "(1 minute)". Kafin suce wani abu sai gashi ya shigo, da tsintsiya da Bokiti da liquid soap, ya kusta kai cikin Gidan, su kuka suka zauna a kasan Bishiya, Yesmin tace " Ina ganin kamar dayan yace ba zaiyi bane, don naga wani kallon da yake mana" Sada yace "aiko zan ma wannan Alheri Sosai". Yaron Ya dade yana aiki, ya shiga nan ya gyara, ya wanke chan, komai sai da ya gyara, Aiki dai yayi ba ha'inci, ya fito ya musu nuni da ya gama, suka lek'a, suka ga komai yana shining, Sada yaji dadi sosai, ya bude Wallet ya ciro 200 rupees ya ba shi,200 rupees daidaid yake da Naira dubu 1 a kudin Nigeria, sosai dan saurayin yaji dadi, daga yanda yakeyi zaka san yaji dadi, be iya cewa komai ba sai "thank you, thank you". Yesmin tayi murmushi tace da Sada "barin ga ko na iya indianci" ta kalli Saurayin tace "Aapka Naam kya hai?(Ya sunanka?)" da Murna yace "Mera Naam Vijhay(Sunana Vijhay)" nan ya shiga rantafo zanttutuka da Indianci, suko sai daria suke tayi. 聽 Vijhay ya rakasu Kasuwa sukayi siyyayan abubuwan bukatarsu, na Abinci, da sauransu. Washegari Vikash yazo ya tafi da Sada Maaikatansu, cikin ikon Allah aka daukeshi Aiki,Vikash yake tambayar shi, "ita Yesmin ba zata fara aiki ba? Ko su a country dinsu Mata ba sa aiki?" Sada yace "sunayi, in sunyi settling itama zata nemi aiki" yace "me take iya yi?" Sada yace mai "Medical Practitioner ce" Vikash yace "Wow, aikuwa zai kaita wani Private Hospital, idan sun mata Interview zasuyi employing dinta". Ko da ya gaya ma Yesmin yanda sukayi da Vikash taji dadi sosai. Washegari Vikash yazo ya dauke su suka tafi Indrasptha Appolo Hospital da yake a nan Sarita Vihar. Bayan wani dogon bayani da wasu abubuwa aka dauki Yesmin aiki a Asibitin. 聽 Tun daga ranar da suka dawo Unguwar, kullum Vijhay sai yazo yace "room sweep?" sai dai suyi daria, in akwai wani aiki sai Sada ya bashi ko wanki, ko makamancin haka, har suka fara sabawa duk da ba wani fahintar juna sukeyi ba, in ta dafa Abinci tana zuba mishi yaci. Haka Yesmin da Sada suka fara Sabon rayuwa ba tare da wani damuwa ba ko matsi. 聽聽 BAYAN WATA BIYU KANO NIGERIA. 聽 聽 聽 聽 Yau Asabar, yau 'yan HIG ke hutu, Alhaji Abba Abu da Matarshi da Zaineema ne suka zo Hassan Gwarzo daukan su AbdulMajid, da gudu suka rugo suka rungume Alhaji Abba, Kafin suka rungume Mairo, Zaid ya dauki Zaineema da take ta tsalle tana fadin Zed Zed ko kallon Abdul batayi ba,abunda ya k'ona ran Mairo kenan,wai don me Zainee zata fi murna da ganin Zaid,ba Yayanta Abdul ba, Alhaji Abba yayi daria yace "Ahh, Zaineema baki manta Zaidunki ba, to ku shiga mota mu tafi gida" bayan sun saka Jakkandu cikin Booth, suka shige mota suka nufi gida. 聽 聽聽 Murna gun Zaid da ya ga an doso Gate din Gidansu, ya k'agara ya ga Maminshi da Babanshi, sosai yayi missing dinsu, Alhaji Abba na parking, Zaid ya bude murfin Motan ya dira ya sa gudu ya na kwala kiran "Maama, Baba, mun dawo" Abdul ma ya rufa mai baya da gudu, gaban Alhaji Abba ya fadi, yana tunanin ta yanda zai sanar da dan k'aramin yaron nan Rasuwar Mahaifanshi,tsayawa yayi yana tunani ya kasa shiga ciki, Mairo ko ta6e baki tayi ta shige ciki. 聽 Ko wani daki da sak'o na cikin Gidan Zaid ya bincika amma wayam, ina Maaman shi, ko suna gidan Kaka Hajjo ne? A Parlor ya iske Mairo, ya k'arasa gunta yace "Mama, ina Mamana da Babana?" a tak'aice tace "Sun Mutu" Ido ya fiddo, Zaid na da wayau, haba dan JS1 ai ya san Mutuwa ko? Cikin firgici da tsoro yace "Mama danAllah kiyi hakuri, suna ina? Ko sunyi tafiya ne?" ihu ta datsa mai tace "Ajiyar su ka bani?nace maka sun mutu ko?ko baka san mutuwa ba?" hawaye ke zuba a idonshi, kanshi na juyawa, Mamanshi ta mutu? AbdulMajid ma ya fara kuka, Alhaji Abba ya shigo, da sauri Zaid ya k'arasa gunshi yace "Baba Abba, wai Babana ya mutu?da sauri Alhaji Abba ya kalli Mairo, yace " haba Mairo, yanzu sai da kika gaya mai mutuwar nan? He's just a kid" tsawa ta daka mai tace "yi min shiru, ko basu mutu bane? Boyeboye na meye?gwara a gaya mishi ya sani tun wuri" Alhaji Abba ya fara hawaye, yace "ba dai ta hanyar nan ya kamata ya sani ba" tace "naje na gaya mai, don ma ban gaya mishi ta irin hanyar da suka mutu ba?" tambayar da Zaid ya mata ne ya basu mamaki, ita dai tasan Zaid yasan ba ta sonshi, bata son Yesmin, ta tsanesu duka amma bata taba zaton wayonshi zai kai ga ya mata irin tambayar nan ba Kallonta yayi ido tsaye yace "Ke kika kashe su ko?" tamkar saukar Aradu Mairo taji abun, haka kurum taji tsoro ya kamata, yaro k'arami kamar Zaid ya sa ta fargaba karo na farko. Baba Abba yace "Zaid, kar kace haka, ka bari kaji, nine Babanka Maryam itace mamanka yanzu, AbdulMajid kuma Yayanka, Zaineema kanwarka, kar in k'ara jin maganar nan a bakin ka" Kuka yakeyi sosai, AbdulMajid ya matso kusa dashi yana share mai hawaye, Zaid ya sa duka hannayenshi ya ture AbdulMajid ya fadi kasa warwas,"Mamanka ta kashe min Mama, nima sai na kasheta in na girma, kuma wannan Gida na ne, sai na koreku duka, bana sonku ku fita ku barmin Gidan Babana, Allah sai ya saku a wuta dukanku" Alhaji Abba ya daka mai tsawa yace "Zaid ka min shiru, baka da hankali ne? Wayace maka mu muka kashesu? Baka san kowa zai mutu ba? Lokacinsu ne yayi, nima da na ji rasuwarsu i acted like you did, nasan kai yaro ne, you wont understand, amma Baba Abba is here for you kaji yarona?" da k'arfi Zaid yace "I hate you
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169