Chapter 153
Chapter 153
ka yafe musu, ka sa sun huta, ka haskaka k'abarinsu, domin Albarkar Fiyayyen Halitta. Wanda suke da rai kuma Allah ya kara musu nisan kwana Ameen). **** Zaune take kan stool din Madubin dakinta, ta ji shigowarshi, kamshin turarenshi ya fara sanar da ita da Jaan dinta ne. Kin dagowa tayi har sai da ya shigo dakin gabaki daya, wani abu take ji game dashi wanda ba zata iya bayaninshi ba. Ba kullum suke haduwa su ke6e don yin soyayya ba, ba kullum suke waya ba, amma Soyayyar gaskiar na dashe a cikin rayukansu, daidai Gadon da ke kallon Madubin ya zauna, ya kasance tana kallon madubi amma shi take kallo, shima Madubin yake kallo amma ita yake kallo. Murmushin k'auna suke aikawa ma junansu, kafin Abdulmajeed ya fara magana "PureHeart, bansan ta inda zan fara magana ba, randa na fara ganinki, tun a jirgi, domin Allah naji wani abu game dake, bansan ko meye ba, amma duk kukan da kike yi a Cikin Jirgi haka kurum na tsinci kaina da shiga damuwa, bansan dalilin da ya sa na kasa hakura ba har sai da na tanka miki, bayan nan, zan iya cewa wannan k'auna ce ta jini da bata yankewa, girman yanuwantaka na da girman gaske, saidai rashin sani ya sa a k'i fuskantarsa. "PureHeart na fuskanci cewa you are so innocent, and naive, zuciyarki me sanyi ce, in miki na wani Rafeeq Lema, yace "Baki da hayaniya, baki da damuwa" Najwa ta murmusa ta cigaba da kallonsh. Ya cigaba "Abun ne ya zame min biyu, Son 'yanuwantaka, da kuma So mai wuyar fassaruwa, Najwa, ina sonki, ina k'aunarki, akwai abubuwa da yawa da suka faru a baya, kuskuren Mahaifiyarta, ban san ko zaki dinga kallona da abun ba, ina--" katseshi tayi ta hanyar cewa "shhh, Jaaaan, ka bar maganar nan, kamar nace maka maganar nan ta wuce kar a sake dawowa da ita? Nace maka a bar abunda ya faru a baya, a maida hankali kan abunda zai faru a gaba. Bansan irinka ba, irin zuciyarka kadan ne a duniyarmu, kai Namiji ne da ko wace mace zatai burin Aura ko burin Samu, ka hada komai, to me zan jira? Me zai dameni? Ina da kai fa? Meri jaan, tumase pyar kharta---" bata karashe abunda tayi niyyan fada ba yayi saurin rufe mata baki yana girgiza kai, yace "Aa, aa donAllah, wannan Indiyancin na k'warata, karki boye min, ki gaya min da yaren da zan gane, PureHeart, ki fada min, ina so naji donAllah" runtse idonta tayi ta fara magana "Ina Sonka Ya Majeed, wallahi ina sonka, ina so na karashe rayuwata da kai, bansan me zanyi ba in babu kai, ba kyaun fuska kadai gareka ba, kanada kyaun zuciya, ina sonka da duk wata jijiya dake cikin jikina, ina sonka da duk wani Jinin da ke gudana a jikina, ina sonka da duk wata na'urar dake aiki a jikina". A hankali ta bude idanuwanta ta saukesu fes kan Abdulmajeed da bakinsa a hangame kamar yaga wani abu, mamakin kalamanta yake, be taba zaton tahi hausa har haka ba, babu cikin abunda ta fada wanda be shigeshi ba, sak'on da ta aiko mishi ya k'arba, ya kuma so ya maida mata ta martanin da zai fi baiyanar da abunda yake ji a ranshi, sai ji yayi ma jikinshi yayi sanyi, ya gyada kai, yace "Najwa, Allah shine Shaidana, ina sonki Dominsa" Murmushi me k'ayatarwa ta sakar mai, ya mike jiki ba kwar'i yace "bari naje na dauko Yara" Murmushin dai ta sake mai tace "muje nima ina zuwa" be ce mata komai ba yayi gaba, ta dauko Hijab din Sallahnta ta bi bayanshi. A parlo suka iske Ziyada tana ta Murmushi ita kadai, abunda ya faru tsakaninta da Zaid dak'iku da suka wuce yana sata nishadi, Abdulmajeed yace "Yadai Zuzu?" shashantar da maganar tayi don ya bata kunya ta hanyar cewa "Ina zuwa?" Najwa tace "Su Zeenah zamuje daukowa a School" Ziyada ta mike tace "nima zanje" yace "Aa, je ki gaya ma Mijinki" shagwabe fuska tayi tace "YaMaji fa yana cikin dakin Mama tun dazun fa" Shiru yayi kafin yace "Keke Napep fa zamu hau, su Paapa sun fita da Motar" Ziyada tace "Ooo, inada Miji kamar ZSA dangi na zasu hau Napep? Muje waje akwai Drivers" Najwa ta kalli Abdulmajeed suka tabe baki a tare suka ce "Ahhh Allah ya baki hakuri Matar ZSA" daria tayi tace "ku fada ku k'ara" muje tayi gaba, suna binta a baya Najwa ta bude murya yanda su Zaid zasu jita tace "Maama mun tafi dauko su Zinatu".. *** Hannunsa ya cire zai rik'o nata, da sauri ta janye kamar wuta zai tabata, da mamaki ya kalleta, ya k'ara kai hannu zai ta6ata, da sauri ta sake daukewa, nan ya gane abunda take nufi da yin haka. Ya kalli Driver yace "DonAllah kayi parking ka dan bamu wuri zan yi magana da matata" ba musu Driver ya samu wuri yayi parlking ya fita, Khaleed ya sausauta murya yayi yace "Zainee Nah, kina fushi dani ne?" banza tayi dashi ta kawar da kanta gefe, hannunsa ya sa ya juyo da habarta yanda zasu fuskanci juna yace "ki min masifa, nayi kewan fadanki, ki min" shiru tayi sai ma ta kawar da kanta gefen windown mota. Dungurin kanshi ya farayi yana marin kanshi, hakan da yakeyi ne ya jawo hankalinta gareshi, Lankwashe murya yayi kamar ita yace "Don me Dee? Ashe baka yarda dani ba? Ashe in duniya zasu zargeni da mummunan zargi zaka tayasu gurin zargina? Ashe ba son gaskia kake min ba? Baka yarda dani ba? Baka tsaya kaji ta bakina ba? Kayi watsi da komai ka sakeni? Ka wahalar dani? Ka maidani bazawara" ya cigaba da dunguri da marin kanshi har sai da Zaineema ta fara kuka tana dukkanshi a kirji ya daina, be hanata ba, kuka take tana dukkan kirjinshi da hannu biyu tana cewa "Dee, ka wahalar dani" dama zai iya kuka da yayi, yace "Zainee nah, na sani, kiyi hakuri, ki dauka hakan a matsayin ajizanci na dan adam, kowa a matsayina zaiyi abunda nayi, abunda ya wuce ya wuce amma ki min uzuri, nikuma zan nuna miki yanda nake sonki, da yanda nayi kewanki, kinsan ina sonki, and i miss you so much" hawayenta suka k'ara yawa ta gada jikinshi, shiko ya rungumeta, tana kuka a kan kafadunshi, ita tasan tana son Khaleed sosai. Shafa bayanta ya shiga yi yana cewa "Ki bar kukan nan, kinsan banaso" tunawa tayi fa basu da aure yanzu, a hankali ta dago daga kan kafadunsa, yayi niyan sake rungumarta ta yi daurin cewa "Ba fa a daura mana auren ba" Khaleed ya dafe kanshi yace "Ya Illahi, now i cannot even hug my wife" dariya tayi tace "Nope!" turo baki yayi ya dan tashi ya ratsa ta kujerun gaba ya ma driver horn alamun sun gama. Driver ya dawo Motar ya ja ba tare da sanin inda suka nufa ba. ***** Maigadi ya sanar da Hajia Aynarh tayi bak'i maza, ganin akwai mayafi Jikinta ya sa tace "su shigo" bata fasa filing nails dinta ba suka shigo da Sallama, Murmushin su ya fadada, mazauni suka ma kansu, ita ko ta gyara zama yanda zata fuskanci masoyinta yanda ya kamata,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169