Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 72

Chapter 72

Adade Ana Yi Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

"da sauki tunda ba su mishi komai ba, kaje ka ganshi ko?" Majeed yace "eh naje, daga chan nake yanzu" Mummy ta lula duniyar tunani kawai tace "Alhaji Nakowa ne ya turo mishi barayin nan" duk suka bita da ido tace "haba, ga abu a baiyane, Alhaji Nakowa ne, ya zaayi ace Armed Robbers su tare ka, su karbi wayanka suyi wiping komai? Su maida maka wayanka ba tare da ko dunguran ma kai sunyi ba? Wallahi they were after that recording" Daddy yace "Maryam, ki tsarkake tunaninki, kila ba haka bane, maybe they were after something else" Hmm Mairo tace, ita dai tana da tabbacin Alhaji Nakowa ne yayi aiken nan, saboda recording dinnan, su Daddy ba zasu gane ba, don ba su san wainar da ake toyawa ba, saboda an kai mai sammaci shiyasa yake neman hanyar salwantar da evidence dinsu ko? Dole tayi taka tsantsan, kawai dai su hadu Kotu, sunci nasarar kwace na hannun Aliyu, amma ita ba zata bari ba, bari ta kira Lawyer dinta ta tura mai, komai ta fanjama fanjam kawai. B A Y A N K W A N A B I Y U Kullum sai sunyi waya da su Maama, ta sa Kaveri ta nemo mata numbern Aisha, suna chatting sosai, ta bata labarin abubuwam da suka faru da ita bayan rabuwarsu, Aisha tace "i told you so ai, yanzu you need to be very careful, ki kula da kanki" nan ta sake bata shawarwari. kwana biyu ta na cikin walwala, ba ita kadai ba, duk Ilahirin Familyn Abba Abu, ba su da wata damuwa, kwana biyu, suna zaman su lafiya, ina ma wannan farinciikin dawamame ne? Ina ma su kasance haka har karshen rayuwansu, ba su da damuwa, ba su da wata matsala. Kullum Majeed ke kai Ziyada Makaranta ya daukota, da Muhsin ya dawo Makaranta, zai rugo da gudu wurin Najwa wai ta koya mai Homework, zata karba tayi guiding dinshi, in bata gane ba sai ta tura shi wurin Ziyada, ita kuwa Zinatu tafi k'arfin Najwa ta koya mata Homework, haka take damun Daddy ko Ya Majeed su koya mata, don ta san ko kallonta Ziyada baza tayi ba. ** Kamar mara gaskia, Mummy na fita da Mota yayi Sallama dakin Hajjo, Hajjo tace "Abdallah, har ka dawo daga kai Ziyadatun Makaranta? Yace " Eh Hajjo, jikarki zaki ara min, zamu dan fita" Hajjo na lura da Najwa, tunda Majeed ya shigo dakin bata da sauran sukuni, Hajjo ta murmusa irin yanda manya keyi, tace "a dawo lafiya" Najwa tayi kamar bata ji me suke cewa ba, sai da Majeed yace "Muje ko Pure Heart?" kanta a kasa ta tashi, dama akwai Hijab a jikinta, tace "naje" Hajjo tayi dariya tace "bahausa, kin tafi zakice ba naje ba" sukayi dariya. Kasancewar Daddy ya fita da dayan Motar ya sa Majeed tsaida musu keke Napep, ya dan kallota yace "kin ta6a hawa?" kai ta gyada mai, yace "Oh hakane ko? Tuptup kuke ce mai a India" murmushi kawai tayi, yace "PureHeart, ki dinga bude baki kina min magana kinji?" ta dan turo baki, yace "you look cute" ta sa Hannu a fuska ta rufe, yayi daria, yace da me adaidaita sahu, "Rijiyar Zaki zaka kaimu, ta wurin Islamiyan Mallam Sanda?" suka shiga suka fara tafiya, shiru shiru ba wanda yayi magana sai Majeed yace "baki ce ina zamu ba?" tayi shiru yace "Ehen Ina jinki" a hankali tace "i trust you" murmushin jin dadi yayi. Daidai Islamiyan suka tsaya, naira 500 ya ciro ya ba mai adaidaitan, yace "jirani ina zuwa" gyada mai kai tayi, yayi gaba ta bishi da ido. "Assalam Alaikum" Majeed yayi Sallama a gaban shago, Wani dan Dattijo mai sanye da Alkyabba fara da Charbi zungurere ya amsa mai da "Waalaikum Salam, Bismillah" Majeed ya dan sunkuyar da kanshi don K'ofar bata da tsayi ya shiga, bayan 'yan gaisuwa, Mallam Sanda yace "saidai ban ganeka ba" Majeed ya dan Murmusa yace "AbdulMajeed ne, na wurin Alhaji Abba Abu" Mallam Sanda ya fadada fararsa, "to to, AbdulMajid ne? Haka ka koma? Ka zama magidanci, rabona da kai tun randa kazo min bankwana zaka tafi Makaranta Turai" Majeed ya Murmusa yace "gaskiya ne, an kwan biyu" nan suka sake kwasar wani gaisuwan. "Allah gafarta Mallam, tare nake da wata a waje, Mahaifanta na tare da wani Matsala, haifaffun Nigeria ne, amma rana tsaka suka hada kayansu suka bar K'asar, yanzu ba su iya tuna komai game da Nigeria, ko Garin da suke ba zasu iya tunawa ba, kuma duk randa suka shirya zuwa Nigeria, InshaAllahu sai wani abu yayi sanadiyar rashin zuwan su, shine nake so in akwai taimakon da zaa iya yi?" Mallam Sanda ya danyi shiru, chan yace "Shigo min da yarinyan" Majeed ya tashi ya fita, tana nan rak'ube, yace "PureHeart, ki shigo, munzo wurin Mallam ne, zai miki tambayoyi, ki bashi amsa kinji? Trust me, everything will be fine". Ta bi bayanshi, suka shiga Shagon, kusa da AbdulMajeed ta zauna, ta gaishe shi, Mallam Sanda ya dinga mata tambayoyi tana bashi Amsa iya saninta, Mallam Sanda ya kalli Majeed yace "Kurciya ce aka musu" Majeed yace "Kurciya?" Mallam ya gyada kai alamun eh yace "Kurciya ce, ana yin shine a lokacin da ake so a nesanta mutum da wani wuri, ko a musu farakku, maana a musu katanga, an shiga tsakaninsu da Mahaifarsu, Yanuwa da Abokan Azziki, yana iya yiwuwa wani ke hassadarsu, ko k'yashinsu" kan Majeed yayi zafi, yana mamakin mutanenmu, how can someone be so heartless? Sai yaji ya k'yamaci hassada a zuciyarshi, ya kyamaci me hali irin na Hassada. Majeed yace "Mallam, yanzu me abun yi?". Mallam Sanda ya dan Muskuta yace "Addua, Addua zamu tayi, da Ikon Allah da yardan Allah Sihirin zai karye, kila ayi k'aik'ayi koma kan Mashekiya, maana abun ya koma kan wanda ya musu, ni da Dalibai na zamu sauke Alkurani Maigirma har lokacin da zasu baiyana, ba zamu bari ba, har sai randa suka iya tuna ko da sunan garinsu ne, Yayanta kuma, da Yardan Allah, indai yana cikin K'asa Nigeria, in har da ransa, da Izzar Allah zai baiyana kanshi a duk inda yake, kar ku sama zuciyoyinku komai, Ikon Allah ya wuce tunaninku, da Ikon Allah zai baiyana Yayanta, a Mace ko a Raye". Ya k'ara da fadin suma su dage da Addua, k'arfin Addua zai bayanasu duka, Majeed ya hau Godia, ya ciro 5000 ya ba Mallam, Mallam ya girgiza kai yace "aa Abdul, dauki kudinka, taimako ne, aka ma wasu bare kai?" Majeed ya girgiza kai yace "Aa kar muyi haka da kai Mallam, Sadaka ne, a sai ma masu Sauka ruwan Sanyi" Mallam yayi Murmushi yace "Allah ya saka da Alheri Allah ya sa a dace, Najwanatu Allah ya Baiyana miki Yayanki, Allah ya sa Mahaifinki suci galaba kan masu son ganin bayansu" duk a tare suka amsa da "Ameen". A lokutta da dama, Allah na daura ma bayinsa Soyayyahn junansu, balle ma in suka maka abunda ba zaka taba mancewa ba, zakaji duniya ba wanda kake so sosai matuk'a kamarsu, hakan takasance da Najwa, tana jin AbdulMajeed Abba har cikin ranta, tun kafin ya furta mata So, bayan ya furta mata kuma sai soyayyarsa ta ninku a Zuciyarta,

Table of Contents

Chapters

169 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});