Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 61

Chapter 61

Adade Ana Yi Book 1 Complete Hausa Novel 1,195 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kamar ta sa ihu, tana so tayi waya da Maaman ta, jin Alamun ana takowa ta inda take ya sata deleting numbers din da sauri ta maida wayan a riga ta koma parlor, inda ta ga wayan ta maida ta ajiye, ta koma Daki. I N D I A Kwanaki 18 daidai kenan da tafiyar Najwa, in ka Alhaji Sada Abu da Matarshi sai sun baka tausayi, Rayuwa suke kamar Matattu, ba su da wani jin dadi da walwala, duk sun rame sun fita hayacinsu, barin ma dai Maaman Najwa, hardai shirin biyo ta Nigeria sukayi, kamar Kullum suka kasa, wannan karon Paapa ne ya sul6e ya fadi k'asa, ya karye k'ashi, yanzu haka suna Asibitin Apollo inda Maama ke aiki, Zafi dubu da goma wurin Maama, ga rashin sanin halin da diyarta ke ciki, ga Miji kwance a Asibiti ba lafiya. Da ta samu Bacci ya dauki Paapa, sai tace bari ta tashi taje Gida tayi wanka, sai su dawo tare da Vijhay. * Wayar Paapa yayi ta ringing har So uku kafin nata ya hau ruri, tana cikin gida, Wayoyin kuma suna cikin Mota inda ta barsu, sai da tayi wanka ta dan dafa musu Abinci, kafin ta kira Vijhay suka koma Asibiti, ba tare da ta duba Wayarta ba ko na Paapa, ko da suka isa Asibitin, Paapa ya farka, Maama tace "Papi kya huwa?" a hankali yace " Najw a-" ta karado gunshi da sauri ta riko hannunshi, yace "Yesmeenah, nayi Mafarkin Najwa na ta kwala min kira" da sauri ta tashi ta wawuro Jakkarta ta ciro wayoyinsu, Ikon Allah taga missed calls 3 ana Paapa, Biyar ana ta, kuma international call, callcode din Nigeria +234, kuka ta fashe dashi tace "Wallahi Papi Najwa ce, Najwa ce ta kira mu" yunk'urin tashi yakeyi Vijhay ya tareshi. Maama tabi bayan Missed call din ana dauka "Meri Beta(Diyata), Najwanatu Ke ce?" shiru ba amsa, Hello kinaji? Kiyi magana mana, bakiyi missing Maama dinki bane? Haba diyata ki min magana" nan ma Shiru, sai nishin da takeji sama sama, Maama ta fara shesheka tace " ba zakiyi magana ba, to ga Paapan ki ? Da sauri ta ba Paapa wayan "Papi tak'i ta min magana" Paapa ya amsa wayan "Hello, Hello, ba kya jine, kiyi magana mana" dif sukaji wayar ta katse, hannu na rawa suka sake dialing, sai akayi rejecting, da su ka kara sai ji sukayi wayar a kashe, Maama tace "Papi meke faruwa? Najwa ta kira mu taki magana" Paapa yace "kwantar da hankalinki, it shows that Najwa is fine, tunda har ta iya kiranmu, kila service ne, network ne, shiyasa baa ji, ko kuma chargy it can be anything, thing positively Yesmeenah, Najwa zata sake kiranmu kinji?" Da haka ya lallabata har ta dan kwantar da hankalinta. K A N O Ng Ta shigo Parlo dauke da plate din fruits, ta zauna tana cin Apple cike da tak'ama da isa, Hajia Mairo kenan, Uwar Gidan Abba Abu, tana chanza Channel taji wayarta na ringing, Janyo wayar tayi ta ga International Number ce, +91, da mamaki tace "toufa, wannan numbern wace k'asa ce?" tana dauka ta sa a kunne tare da fadin "Hello" Muryar da taji ne ya sa kirjinta Dukan Chalugude, gabanta kamar ya fashe don duka da sauri, tayi k'asak'e tana sauraron Muryan da ke Amo a kunnenta, ba zatace ga abunda matar ke cewa ba, amma hankalinta in yayi k'ololuwa to ya tashi, bata gama tsurewa ba, sai da taji Matar tace "Papi" hankalinta be kai ga tashi ba kamar yanda taji Muryan Namijin da ta fara So a rayuwarta, ba zata iya mance Muryarshi ba, tsoro da fargaba ya sata latse wayar, a guje ta fada dakinta, ta shige toilet da gudu, shower ta sakar ma Kanta, bata damu da kayan da ke jikinta ba, ya akayi haka? Shine tambayar da ke kai kawo a kanta, ta ya akayi suka kirata? Ya akayi suka samu numbern ta? Sada? Yesmin? Ya akayi suka ita kiranta wai? Ita da aka bata tabbacin zasu guje duk abunda zai sadasu da Nigeria, ta ya zasu iya kiran Nunbern Nigeria? Tsigar jikinta duk suka mimike, ina ma zata iya kuka, ta kasa, Kar fa su dawo, ta ya akayi, Mamaki da tsoro sun hanata yarda da cewa su dinne suka kirata, da gangan ta k'aryata kanta, ba su bane, it cant be them, ba Sada bane, ba Yesmin bane, ba su bane, kar ku min haka, kar ku dawo, kar ku dawo donAllah, ba kunya ba tsoron Allah Mairo ta daga hannu sama tana rokon Allah, Allah ya k'ara nesanta Sada da Matarshi da Nigeria, amma fa kamar taji sun fadi Sunan Najwa, what if sune Parents din Najwa? What if-?" da sauri ta kawar da tunanin nan, a fili tace "No, it cant be" ita fa duk yanda zata kawar da tunanin nan sai ta kawar dashi, ta gama da babin Sada da Yesmin, abunda ya faru sama da shekara 18 shine zaace sai yanzu zasu baiyana? Be yiwuwa, kawai banzan tunani take tayi, ba su bane, Mairo da taurin Zuciya, ta kan kitsa ma kanta abunda take so ta yarda dashi, haka tasa Zuciyarta yarda da ba su din bane, ta fito daga toilet ta chanza kaya, kai tsaye ta dauko wayarta ta kunna, tayi blocking numbers din da aka kirata dasu ta fito Parlor. * Tana fitowa ta ci karo da Najwa, gaban su a tare ya yanke ya fadi, ita Najwa tana tsoron ganin Mummy, ita kuma Mummy ganin Fuskar Najwa tayi ya rikide mata ya koma mata na Yesmin. Kiris ya rage ta fadi k'asa amma da yake Mairo Mace ce mai kama da Maza sai ta cije tace "ke zonan" jiki na rawa Najwa ta k'arasa gaban Mummy ta durk'usa, Mummy tace "tambayan ki zanyi, in kika sake kika min k'arya sai na miki mugun duka kinaji na" Jikin Najwa ya hau karkarwa, ta gyada kai, Mummy ta dauko wayarta ta nuna mata last call tace "ke ki ka kira numbern nan?" da sauri Najwa harda rintse ido tace "aa" Mummy ta jinjina kai tace "danubanki ke 'yar wace k'asa ce?" muryan Aisha ta tuna inda take ce mata "Najwa you must not trust anyone" baki na rawa tace "Ghana" cikin tsawa tace "ina Iyayenki suke zaune?" tuni Najwa ta gama tsurewa, wani tsawa da Mairo ta daka mata sai da ya sata ciwon kai lokaci guda, "suma 'yan chan ne, 'yan Ghana ne" "k'arya kikeyi" "dagaske" Mummy tace "karbi wayan nan, sa numbern Iyayenki, ki kirasu in tabbatar" Najwa ta tsure tace "ban rik'e number dinsu ba" Mairo ta jawo ta ta hau kilarta, k'arya kikeyi, Najwa ta hau kuka a hankali yanda ba kowa zai ji ta ba. * Kamar daga sama sai ga Majeed, da sauri ya k'arasa gunsu, cikin Zafin nama yace "Mummy me nace miki game da Najwa?" cikin Hargowa tace "wannan yarinyar Makaryaciya ce, shes not what she says she is, wayana ta dauka ta kira Iyayenta, na tambayeta ita yar wace k'asa ce tace wai Ghana, kuma numbern da aka kira ni da shi irin Asian countries din nan ne, nace ita ta kira numbern ta k'aryata, dan uwarta nace ta ban numbern Uwarta,

Table of Contents

Chapters

169 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});