Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 154

Chapter 154

Adade Ana Yi Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bayan 'yan gaishegaishe, ta mik'e don kawo musu abinci, Daddy ya dakatar da ita ta hanyar cewa "Aa Hajia Aynarh, mun hutassheki" Zama tayi tana fari da ido. Sada yace "To Hajia, dama so muke ki gaya mana inda zamuje neman aurenki, don ki zautar da Yayana, ko gaban Yara ne maganarki yake" daria tayi, ta sadda kai alamun taji kunya kafin tace "yawancin danginmu suna Kwara, but akwai uncle dina, Baba Abdoulfatah, a Kwanar Ganduje, shine madaurin aurena, shi ke aurar dani, a Gidanshi ma nayi Karatu, ya dade a Kano yana aiki bayan yayi retire be koma chan garinmu ba. Sada yace "to sai ki bamu Address da numbernshi mu biya mu kai gaisuwa, da kuma Buhun doya nawa zamu kai na neman aurenki?" dariya Daddy ya sa, ita ko throwpillow ta dauko ta wurga ma Paapa "Wallahi Sada ka rainani, da buhun doya zaaje neman aurena?" Dariya suke sosai. ** Tana dan kishingide taji muryan Daddy, to me yake a nan? Ta tambayi zuciyarta, k'ila yazo maidaki dakinki ne,da sauri ta tashi ta nufi Parlo da Sallama, amma kunnenta ya jiyo mata wani abu kafin sallamarta, "Wallahi Sada ka raina min Aynarta, to dole ka aje wasan k'anin mijinnan, ba zan yarda ka raina min Amarya ba" wani Yammm kanta yayi kafin ta fara jin idanuwansu a kanta, sun lura da ita, da mamaki suke kallonta, banda Hajia Aynarh da ta dauke ido, Daddy ya dan cin face ya kalli Aynarh yace "me takeyi a nan?" a takaice tace "Kwana" kafin waninsu ya k'ara magana tuni Hajia Mairo ta tako har gabanshi "Haba Daddy, haba Daddy, kana Fulanin usul, me jinin shuwa arab, me zakayi da Bayerabiya, Yoruba fa, Daddy dama sonta kakeyi?" duk da ba wai cikin tashin hankali tayi maganan ba, amma sai yaji ranshi ya 6aci, dubi matar nan, har tana da bakin magana, bayan abubuwan da tayi? Lallai bata da kunya, Banza yayi mata, tace "Daddy nafa ce na tuba, donAllah ka maidani dakina, na chanza, zamu zauna dakai da yaranmu lafiya, ba sai ka sake Aure ba, donAllah Daddy" bakinsa ya ta6e, Hajia Aynarh ta mik'e ta kalli Sada tace "Ka gaida Yesmin, ko kallon Daddy batayi ba tayi hanyar daki" meke nan? Kishi ake a kanshi? Daddy wani dadi yakeji amma be nuna ba, yace "kai tashi mu tafi" Mairo tace "Sada DonAllah ka bashi hakuri, wallahi na chanza halina". Tausayi a bashi ya kasa magana, sai gyada kan da yayi, kafin ya ankara har Daddy ya bar parlorn. Mairo ta durkushe tana jin zafin Hajia Aynarh hat ranta, zuciya ya sata shiga dakin Hajia Aynarh, wanda sai da tayi nadamar shiga din kunnenta suka jiye mata shagwabar da Hajia Aynarh ke ta narka ma Daddy, wato ya bata mata rai shine ya kirata don ya lallasheta?. Ganin Hajia Mairo ya sata daure fuska tare da cewa "Abbana, zan kiraka" Kamar an watsa mata ruwan zafi haka taji da kyar ta samu tace "Hajia Aynarh, kiyi hakuri, ba sai kin Auri Daddy ba, na son yana son aurenki ne don ya huce takaicina, amma wallahi ba sonki yake ba, ni yake so, sannan nasan kema haka, donAllah a bar wani maganar auren, ki taimaka min in koma dakin Mijina". Wani Dariar rainin wayau wanda ya k'ular da Mairo Hajia Aynarh keyi, wanda a da, in ta kuskura ta mata irinshi sai sun kwashi yan kallo, amma da yake yanzu tayi sanyi, kasan cewa komai tayi sai sadda kanta k'asa. "Hajia Mairo, wa ya ce miki ni da Abba bama son juna? Aiko munfi Indiawa soyayya, in muna tare ji muke kamar mu hade juna, to in ma tunani kike Auren huce haushi zaayi dani, na miki kama da irin matan nan da zaa auresu don guce haushi? Soyayya zai sa mu aure, kuma nima ai zanso ki koma dakinki, don ba zan so duniya tace na firdaki daga dakinki don na auri Mijinki ba, ni zan ma fi so ki dawo dakinki don ki koyi yanda ake zama da miji, jidai abunda kike cemai, wai "Daddy, Babanki ne?" kafadu ta daga alamun ina ma ruwana, ta dora da cewa "Some hausa girls sha, wanda ya biya allonsa ya wanke" ta raba ta gefen Mairo ta bar mata dakin, Anan ji take kamar ta shak'o Hajia Aynarh ta mata dukan tsiya, don wallahi Hajia Aynarh ta mugun rainata, ta ga gadon baccinta, amma ba wani abu, ita tayi abunda ya sa ta rainata•. ** Shafa kanshi tayi tace "Zaid, tashi na dafa mana Abincin rana, munyi latti, yaushe aka gama har aka kaima Umma" kamar karamin yaro ya mak'e kafada tare da sake gyara kanshi kan cinyarta, ya ciro wayarsa daga Aljihu ya latso Idi, ringing daya ya dauka "Idi, Lunch muke so" daga bangaren Idi yace "me kukeso?" "Random foods dai" yace "To, bari inyi ordering, zaa aiko yanzu" "Ehen, harda tuwo, a tsaya gidan Hajjo a kai mata nata" Idi yace "Angama Oga, sai me kuma?" Yana jin dadin yanda Idi ke mishi abubuwa, bari ya faranta mai rai Zaid yace "Shikenan, Thank You Idi, nikam Idi, ina brother dinka da kace ya gama Secondary School?" Idi yace "Anas, yana nan, be samu Jamb ba" Zaid yace "baka gaya min ba, Oya ka mai processing School a Cuba, naga akwai wani sabon School na manta sunan, kayi searching, ka mai processing ka gaya ma Faisal" Idi ya gane cewa Oganshi na wani yanayi na nishadi, zai fara godia yaji yace "Shuttup Idi get us lunch" sukayi daria tare kafin suka kashe wayar. Maama ta sake shafa kanshi, tace "ina alfahari da kai, sosai" yace "Haka nake sonji" tace "to still dai ka tashi muje mu hada So6o, Babanka na so" shagwabe fuska yayi yace "cant we just buy?" mikewa tayi wanda tasa dole shima tashi tace "Nope, ni zan mishi" tayi gaba, yana binta a baya yana bubbuga k'afa kamar dan yaro har suka isa kitchen. Da mik'o kaza, dauko wanchan suka dafa Sobon wanda yaji kayan kanshi su Na'ana, citta da karamfani, tana tacewa a dan Jug, yana bata labarin komai da Allah ya hore mishi, ta san Sada yana da kudi tun tuni, amma bata taba zaton danshi zai samu Arzikin ninkin ba ninkin na babanshi ba, Allah kenan, buwayi gagara Misali. "Maa,me kike ganin zan ma Danuwana?" Maams tace "Zaid, abunda zakana AbdulMajeed ai ba sai na gaya ma ba" yace "Amma ai shawara da dadi" tace "kayi mishi abunda ya dace, Zaid, Abdulmajeed ne, ka mishi komai" jinjina kai yayi yana amincewa da duk abunda tace, ba wai don ya san abunda zai ma Abdulmajeed ba. Hayaniya suka danji daga Parlo, alamun sun dawo, yaran suka shigo suna rungume Maama, tace "Zeenah, Muhsin ya School? Suka amsa tace "Najwa, kuje ku musu wanka, kafin a kawo lunch" Muhsin ya fita gun Najwa a guje, don yana sonta, Zaid ya dauka Zinatu a kafadarsa ya fito daga kitchen din, inda yaga Najwa na kiciniyar cirema Muhsin kaya, yace "Baby a parlo a ke cire kaya?" tace "No Bhaiyy" ba tare da ya amsata ba ya kashe ma Ziyadan da ke zaune ido, tare da wurga mata kiss ta iska, a kan Idon Abdulmajeed, ya wurga musu harara

Table of Contents

Chapters

169 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});