Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 136

Chapter 136

Adade Ana Yi Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da Gidan da suke zaune sun saida, Paapa ya samu wani Agent dan Kano suna communicating, nan ya tura mishi kudi ya siya mishi dankareren Gida a Tarauni, don shi baya tunanin zai koma Gidanshi na da, yafi karfin ya tada Yayanshi a gidan da yake, ya bar mai Gidan nan har abada, Maama ta dinga shiga Gidajen Neighbors dinsu tana musu sallama, Vijhay Bhaiya yayi kuka sosai, Maama tace "InshaAllah zasu zo wani lokacin" bayan sun mishi Alheri me yawa, ko da ta shiga Gidansu Kaveri nan suka bata lokaci da Maman kaveri suna jimamin rabuwansu, Kaveri kuwa bata fito ba tana daki tana cizgar Kuka. N I G E R I A. Rigima Ziyada ke ta ma Zaid tun tashin su yau da safe don ya sanar da ita Tafiar gaggawa ta kamashi zuwa Taraba, zai biya Kaduna ya ga Gidan Marayu kafin Jirginsu ya tashi zuwa Taraba's state. Ziyada tace ya tafi da ita, hakuri ya bata cewar tayi hakuri, ya dawo, da ya dawo zai musu processing Visa suje any country of her choice, sannan in sun dawo Gida zasu yi Parking su koma Gidan Babanshi na Asali a Kaduna, dolenta ta hakura amma taso ta bishi don bata son yayi nisa da ita. Alfarma ta rokeshi da ya barta a koma Gida har sai ya dawo, da farko k'i yayi, yace tayi hakuri ta zauna har randa zai dawo, tace "itadai aa, ba zata iya kwana ita kadai ba " ba yanda ya iya ya amince mata da taje Gidan, a daren da zai tafi, makale suke da juna kamar cingam, baya so ta bishi sabida bussiness zaije yi, da wuya ya samu time dinta. Washegari da kanshi ya rakata har Gida bayan an musu siyayya a Shoprite, sunfi Minti 20 a gaban Gidan cikin Mota suna manne da junansu kamar kar su rabu, shagwaba take ta zuba mai, shi ko yayi ta biye mata, "i'll miss you i'm My Forever" rungumeta yayi yace "i'll miss you more" sun dade a haka kafin daga baya ya rakata har Cikin Gidan, suka gaisa da yan Gidan banda Mairo da ba wanda ya lura be gaisheta ba. Daddy ya masa godian Hidiman da yakeyi dasu. Ziyada a boye ta share hawayenta da zai tafi, shima duk yaji ba dadi, ta zama wani bangare na jikinshi. **** Najwa sunyi waya da Su Maama sun gaya mata Jirginsu zai tashi a ranar da daddare, but zasuyi transit a Dubai washegari su iso lagos, dadi ya ziyarci Najwa, ta musu fatan a iso a lafia. B A Y A N K W A N A B I Y U Tun daga garin Allah ya waye yake jin nauyin jikinsa, ya kanji kunnenshi yayi wani irin Yammm, hannunshi kan mai nauyi wurin dagawa, Da k'yar yaje Sallahr Asuba da taimakon AbdulMajeed ya dawo Gida, duk da shima yace be jin dadin jikin nashi, Hankalin Yaran Gidan ya tashi, Daddy da Ya Maji basu lafia, duk da ya Majin ba kwance yake ba, duk suka zauna suka rafka tagumi suna kallon Daddy. Mummy ta lallabasu suka koma dayan dakin tace "a bar Daddy ya samu bacci" da kyar suka fita suka barshi shi kadai. kishingida yayi kan Katifarsa yana tunano abubuwa da suka shude shekaru sama da 20, ya tuna Mutuwar kaninshi da Matarshi, gawarsu da ya kasa shaidawa Saboda k'una, ya rufe kaninshi da Matarshi da hannunshi, wani side na kanshi ya buga kamar an kwala mai darma, da sauri ya girgiza kansa, runtse idanunshi yayi ya na son tunano exact abinda ya faru, sai ya gano Me ya faru da Sada da Yesmin in ba mutuwa sukayi ba? A hankali komai ya soma kwaranyo mai, Kalamanta da abubuwan da suka faru suka so mai sintiri a kwalawa kamar a lokacin ake yinsu "ina so ka maida sunan duk Takaddun nan daga Sunanka zuwa sunan Abba" ya tuna Sada be mata gardama ba yayi yanda tace yace "nagama" shi karan kanshi yaji mamaki, ya tuna da tsoro ya tambayeta "Meyasa? Don me zaiyi haka?" ya tuna tsawar da ta mishi tace "shuttup, baka son ka mallaka Dukiyoyin Sada?" yace "ai yana bani dukkan abun da na buk'k'ata, hakan yayi" ya tuna yanda ta girgiza kai tace "aa, beyi ba, kana son dukiyan Sada" ya tuna yanda ya maimaita abunda tace kamar karatu" beyi ba, ina son dukiyan Sada" murmushi tayi ta kallo Abba tace "good". Ba a kwana ba ya tuna lokacin da ya ganta tayi nisa da tunani, ya tuna tambayarta "Maryam tunanin me kikeyi haka?" a takaice ta bashi ansan "tunanin Kashe Sada da Yesmin nikeyi" ya tuna yanda hankalinshi ya tashi cikin rudu yace "Saboda mene Maryam? Sun ba mu duk abunda muke da burin samu a rayuwa" "hakane, amma zamansu a doron k'asa barazana ce a rayuwata, shiyasa na yanke hukuncin kashe su" Ya tuna yanda ya durkusa kan guiwowinshi ya na kuka yana rokonta gafara"Kiyi Hakuri Maryam, ba sai kin kashe su ba DonAllah, Sada danuwa na ne, kuma ina sonshi sosai" Ya tuna yanda ranta ya baci tace "sai ka za6a ko ni ko shi" Ya tuna yanda beyi dogon tunani ba yace "ke na za6a uwar 'yayana, ina sonki, kece farincikina, zan iya rabuwa da kowa don in zauna dake, amma Sada danuwana ne, akwai Babba Alaqa tsakaninmu, ina neman Alfarma da ki barshi raye,in bakya bukatar ganinsu zan sa shi su bar garin,amma kar a kashe su donAllah Maryam" A kausashe tace? "in kuma hakan zai bani farinciki fa?" Ya tuna muryarshi me cike da tsoro da rashin jarumta yace "da hannuna zan kasheshi don baki farinciki, amma ina rok'onki da kiyi hakuri" shiru tayi kafin tace "Zasu bar k'asan, zasuyi nisa da mu, ba zasu taba dawowa ba har duniya ta nade" Ya tuna tashin hankalin da ya shiga da tace haka, ya tuna yanda ta daka mai tsawa tace "Ko ka fi son a kashesu?" Ya tuna yanda ya girgiza kai da sauri yace "a saka su suyi nisa damu" Ya tuna yanda ya durkusa har k'asa yana mata Godia kan amincewarta na ba zata kashe su ba. Ya tuna Komai, Ya tuna Wallahi, Maryam ta dadw tana zaluntarshi, Maryam ta shiga tsakaninshi da k'aninshi, wai kuma sai gashi bayan kwana biyu a ka kawo Gawarwaki guda biyu wai Yesmeen da Sada, Anya sun mutu? a baiyane yace "aa ba su mutu ba". Maryam ta ha'ince ni, maryam ta zalunce ni, Kuka yakeyi sosai, be sama ma Yaranshi Uwa ta gari ba, k'arshen zamanshi da Maryam yazo, ba zai iya ba, a hankali ya tashi ya na dafe da bango ya fita waje, besan yanda zaiyi ba, amma yasan ba zai iya cigaba da zama dashi ba, don albarkacin yaransu, da ya maka ta Kotu. A waje AbdulMajeed ya ga Daddy, yayi saurin karasawa gunshi yace "Daddy, ka bar jin jirin ne? Ka koma ka kwanta" Mommy ta fito da sauri jin muryarsu, Duk yaran suka biyo bayanta har Hajjo, Mummy tace "Ah Daddy, har kaji sauki ne? Ta karaso gunshi zata taba shi yayi saurin janyewa, yace "kar ki sake ki tabani, muguwa Azzaluma" yaran suka kalleshi da mamaki, Abdulmajeed ya shiga rudu a hankali yace "Daddy..." Mairo bakinta a

Table of Contents

Chapters

169 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});