Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Adade Ana Yi Book 1 Complete Hausa Novel 1,213 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

hankalinta ya tsaya a tunaninta na k'arshe, ta san abu ne mai wuya, amma hakan kawai zatayi Allah zai taimaketa, ta cigaba da rubutu "Diary, i've decided, i'll go to Nigeria, I'll find my brother, and i'll bring him home, So Help me God, Allah ka bani saa, ka kawo min komai a sauk'ak'e Amin".. Ta rufe ta mayyar ta gyara kwanciyarta kan gado bayan tayi Addua don yin bacci. Bacci ya k'aurace mata, sam ta kasa bacci, gabanta na ta fadawa, tsoro ya mamaye ranta, amma idan ta tuna abunda take shirin yi zai faranta ran mahaifiyarta, sai ta ji ta samu k'arfin guiwa, tana ji Mahaifanta suka turo k'ofa, da sauri ta rufe ido tayi kamar me bacci, tofeta sukayi da Adduoi suka juya suka fita, Adduar k'arshe tayi tana rok'on Allah ya sa ta iya baccin, ba dadewa ba bacci yayi awon gaba da ita. Asuba ta gari Najwa Sada Abu. KANO Nigeria. Karfe 6:30pm a k'asar Nigeria daidai yake da 10:30pm daidai a k'asar India, Hajjo ta fito daga bandaki dauke da buta a hannu, ta zauna a ganan kewayen idanunta suka kawo ruwa, rabon da taci abinci har mantuwa ta manta,sai Zogalen da take ci, Zogale shine abincinta, Ta siya Zogale, ta dafa ta saida ta kuma ci ma cikinta,ta daga kai ta kalli gidanta, kallo daya zaka ma gidan ka fahimci gida ne mai kyan gaske, amma zaka gane tsohon gida ne, don ba kula ba gyara, Allah ya jik'an Sada, Allah ya gafarta mai, da yana da rai ba zai taba bari ta wulakanta haka ba, Allah yayi wadaran Abba, Arzikki da dukiyarshi bai amfana mai komai ba, wai ace tana da D'a Kamar Abba, wanda sunanshi ya kauraye gidan Talabijin da Radio don dimbin Azzikinshi amma ya wofintar da Uwarshi Mahaifiya, ba komai, Akwai Allah, ko da yake bata fiye ganin laifinshi ba,tunda tun Asali shine mafi soyuwa a gareta,ta So shi kamar ta bashi ranta, gashi kuma Mace ta shiga tsakaninsu tayi musu Iyaka, AbdulMajid din da take gani tana jin sanyi kwana biyu ta bar jinshi, ta zama bata da kowa, ba ta da wani gawa, ina ma Mutuwa zai zo mata yanzu, da ta fi farinciki, sai da ta ci kukanta kafin ta hakura tayi Alwala don gabatar da Maghrib. Porthacourt Nigeria Bayan yayi Sallahr Asuba ya zaro wayarshi tare da chanza simcard, ya latso numbern Hajia Maryam. Abuja Nigeria Ringing biyu ta dauka tare da sa lasfika, dama jiran wayarshi suke, a lokacin suna nan zaune gabaki daya a Parlo har AbdulMajid, jiya da su Mommy zasu dawo gida ya saka daru sai da Dr ya sallamesu. Mommy tace "Hello", Zaid yace " Hajia Mairo Muna lafiya?ya mai jiki AbdulMajid, naji ance an Sallameshi". "Uhm" kadai Mommy tace, yace "Ina Kudina?" da sauri tace "ga su nan an hada komai" yace "Good, zaa zo har gida a karba, and Zeenatu will be returned to you" cike da Murna AbdulMajid ya gyada kai don zasuyi amfani da wannan damar su chafke wanda ya zo amsar kudin har ya kaisu ga Ogan su. Kamar yana gabansu ya sake shuumin murmushin shi yace "Hajia Mairo, barin baku dan guntun labarin wanda zai zo karban kudin, Sunanshi Dogara, Shi ba Musulmi bane, shi kuma ba Christian bane, bai da addini, hasalima bai da wani mamora, yana da Mahaifiya da yarinya mai shekara daya, wahalar duniya ta musu yawa har wata rana da yaga baida amfani a rayuwa yayi alwashin kashe kanshi, cikin ikon Allah sai gani nazo na cece shi na hana shi aiwatar da abunda yayi niyya, na bashi kudi mai yawa nace yaje ya ciyar da Mahaifiyar shi da diyarshi, tun daga nan,he does everything i ask him to, he owes me his life" Zaid ya tsuke muryanshi ya cigaba da cewa "Dalilin da ya sa na baku labarin nan shine, idan har kuka kuskura kukayi gigin setting dina up by informing the police don nace zaizo gida ya amsa, akace zaayi Interrogating Dogara don ya tona min asiri, ba zai ta6a ba, kun son irinsu ba butulu bane, sai dai ku kashe shi, he has nothing to loose don nayi mai Alkawarin kula da Maman shi da diyarshi, kama Dogara will be the biggest mistake of your life, don zan kashe Zeenatu bayan maza 3 sun mata fyade" Mommy da Ziyada suka sake k'ara don ko tantama babu zai iya abunda yace, Mutumin nan be da Imani ko kadan, AbdulMajeed wani irin Zufa ke keto mai, Daddy mai saukin zuciya har ya fara guntun hawaye. Farinciki ya ziyarci Zuciyar Zaid da yaji Firgici tattare dasu, Babban burinshi shine ya k'untata ma Familyn Abba Abu, yayi murmushi yace "So abun nufi shine, Ba zaku ga Zeenatu ba har sai Dogara ya kawo min Kudina, ku ka sa aka kamashi to a bakin ran Zeenatu, So Hajia Maryam, dont mess with me" da sauri Mommy tace "Wallahi we wont, safely zaa maka delivering kudinka" yace "good,6am Dogara zai zo karban Kudin" dif ya latse wayar. Shiru sukayi gabaki daya kowa da sak'e sak'en zuci. AbdulMajid yace "Mommy, yana wasa da hankalinmu ne, a gaya ma Police" da sauri tace "No Boy, wallahi ba za a gaya musu ba, ba zanyi chacha da rayuwar diya ta ba". Daddy ya jinjina kai yace "gaskia ne, mu basu kudin kawai" AbdulMajid ya gyada kai,Mommy ta yi Zipping Biggest sized Ghana Must Go da Wani Jakka. 6:00am Maigadi ya k'wank'wasa parlorn k'asa, jiki ba k'wari Daddy ya mik'e ya bude, Yace "yadai Bagobiri?" cikin hausanshi yace "Akwai bak'o a waje, nace mishi kuna bacci yace kun san da zuwanshi" kafin Daddy yace komai sai Mommy tayi saurin cewa "Ka barshi ya shigo" da hanzari ya juya Gate. Bayan sun bashi jikkunan kudin,ya loda su a yar motarshi Golf 3, da yake har rakiya suka mai, ba wanda ya mai ko kallon banza, har ya kunna mota zai wuce, a tsorace Mommy tace "zeenatu fa?" Dogara yace "Oga Zaiyi waya, make sure you dont do anything foolish". Mommy ta gyada kai. Ya ja Mota ya wuce, su kuma suka wuce ciki suna jiran Tsammani. "Oga, kudin are in possesion, i'm cleared" daga bangaren Zaid yace "Good, ka zo PH yanzu" "Okay Oga". 11am "Ki tsaya nan, Mommyn ki zasu zo daukanki, kar kije ko ina kinji? Cewar Idi, Zeenatu baki ya mutu, tace "DonAllah ka kirasu" yace "kar ki damu, zasu zo nan ba da dadewa ba" ya wuce warshi, Tsohon Gidan Mai ne, amma ba kowa, jefi jefi take ganin gilmawan mutane, daga mafaka Idi ke kallonta, kiran Zaid yayi yace "suna Gidan Mai" Zaid yace "i'll make the Call" Zai Wayan Daddy ya kira wannan karon,da sauri ya dauka ganin ba suna, Zaid yace "Kuje Total Filling Station na shehu shagari Way,Zeenatu na chan na jiranku" da sauri suka fita ba tare da an kashe wayar ba, yace "kuyi Sauri temperturen garin da Sanyi kar tayi Mura" Ziyada tace "daniska kamar ka damu" yayi Murmushi, yace "Hello Again Ziyada, i will see you soon" dif ya latse wayar, ta Allah bata ka ba. Haka suka dunguma cikin motar Daddy, Daddy ke tuk'in. Ko da suka iso gidan Mai, tana chan ta dunkule guri guda,

Table of Contents

Chapters

169 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});