Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 147

Chapter 147

Adade Ana Yi Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

saka na aikata Sabo da Zunubai, saboda ita na sha Giya, duk na zabure saboda son daukan Fansa, saboda ita nayi hurting dukanku ba tare da saninku ba, daga kai Baba Abba, Abdulmajeed, Zaineema, Ziyada even innocent Zinatu, ba wanda cikinku be dandani Azabata ba, saboda tsananin Mugunta na, har a matsayin Kurma na zo musu ina kuntata musu ba tare da saninsu ba" durkushewa yayi yana kuka me ban tausayi yayin da dakin yayi shiru kamar ba kowa cikin Dakin, kowa da tunanin da yake a ranshi, barin ma Abdulmajeed da Nura Kurma ya fado mishi. Gaban Maama ya fadi, jikin ta yayi sanyi sakamakon jin kalaman da suka gama fitowa daga bakin Zaid, gabanta ya fadi, me yaronta ya Zama? Me daukar fansa ya maida mata Yaro? Me ya zama? Duk yanda take son share ma danta hawaye, duk yanda take son rungumarshi ta shafa bayanshi ta gaya mishi komai zai wuce yayi kamar ba ayi ba, duk yanda take son tabbatar mishi da she's here, ba zatayi ba, sai ta tabbatar da ya wanke zunubanshi ta hanyar tuba, sai ya nemi yafiyan duk wanda ya k'untatawa, sai ya gyara laifikanshi, in ba haka ba, shi da Mairo duk daya suke, ta san da wuya ta iya abun da take tunanin yi, amma Allah zai bata iko, don har ranta bata son Danta ya kasance cikin marasa Rungumar k'addara" A hankali ta taka gunshi ta sha mur wanda har ranta zuciyarta karyewa take, a kausashe tace "Zaid" da sauri ya dago daga durkuson da yayi, nan da nan bakincikin fuskarshi ta sauya zuwa farinciki, Murmushi ya darsu a fuskarshi da sauri ya mik'e yana kokarin rungumarta tare da fadin "Maaa" ja baya tayi kamar wanda dodo ya tunkaro, da mamaki suka bita da ido, banda shi da be damu ba k'ara nufarta yake, ita ko sai baya take kamar wanda abun tsoro ke bin ta daga k'arshe ta daga mai hannu tare da fadin "dakata Zaid, kar ka tabani" gabanshi kamar zai fadi k'asa, tsoro ya cika kirjinshi, hawaye dama ba su tsaya ba, baki na rawa yace "Maaa" duk binsu ake da kallo, Najwa ta karasa gun Maama, ta riko hannunta tace "Maama, me kikeyi haka? Baki ganeshi bane? Your Zaid? Wanda kike kuka kullum saboda rashinshi a India, Maama meyasa kike mishi haka, donAllah ki bari" kamar ta fashe da kuka haka takeji amma sai tace "Haka ne Najwa, amma nayi asarar hawayen da na zubda sabo dashi, bansan yana nan Nigeria yana zubda tarbiyan da na mai, bansan yana nan yana cutar 'Yanuwanshi na jini ba" Zaid ya zube k'asa kan guiwowinshi yana kuka kamar ba namiji ba yace "Kiyi Hakuri, Maaa, banda wani Zabi da ya wuce aikata hakan, tun ina karami na k'uddurta Niyyan tarwatsa Gidan Baba Abba don a ganina da saninshi aka kasheku, na san nayi laifi, amma wallahi dana san kuna da rai, da banyi abubuwan da nayi ba, da na bi ku India munyi zaman mu, Maa, kar kiyi fushi Dani" be tsaya jin wank magana ba, kamar me tabin kwakwalwa ya bude hanayenshi biyu yace *Wani Dan Halak zai ki yin komai in ya ji an kashe mai Mahaifa, an hau kan dukiarshi kuma shima ana neman hanyan kasheshi? Wani dan halak zai folding hanayenshi ya zuba ma Matar da tayi sanadiyar hakan idanuwa? Balle kuma Danhalak din na da Wadatan maida zaune tsaye a duk lokacin da ya so, wallahi ko da talaka ne ni sai na bi duk hanyar da zanbi na dau fansa, balle da kudina*. Da alama kwakwalwar Zaid ya tabu, tunda ga Mahaifanshi ga kuma kanwarshi ba ya bukatar kowa da komai, he's got Nothing to lose, indai zai kasance tare dasu, be damu ya rasa kowa da komai ba, su kadai ne Farincikinshi, zai gaya musu komai, be damu da abunda abun zai haifar ba, shi dai yana so a gama komai a gurin nan once and for all. Kujera ya samu ya zauna don basu labarinshi, farawa yayi daga randa ya gudu daga Gida, da haduwanshi da Alhaji Sadam Audu, da gajeren Tarihin Gatan marayu, da yanda ya nuna mai so kamar dan Cikinshi, da yanda ya ke kaunarshi, da yanda ya maida komai kan sunanshi, da yanda yake mai nasiha kan shan giya da daukar fansa da yake cewa zaiyi, da yanda yake shiga damuwa in yaga ranshi ya baci, komai ya gaya musu har bayan rasuwan shi. Kuka kowa keyi, sun tausaya ma Zaid matuka, Maama kuwa ji take kamar taje ta lallashe shi, ta bashi hakuri kan komai da ya faru, amma ta kasa, sai ta gama jin komai, Mairo kuwa, kunyar abubuwan da tayi takeyi, tayi nadama matuka, ina ma zata iya dawowa da lokaci baya ta gyara kurenta, amma kash, Bakin Alkalami ya bushe, Ya Cigaba da cewa; "Tun da na mallaki hankali na, na ke da labarin Gidan Baba Abba a tafin hannuna, na san shige da ficen kowannensu, na sa da suwa sukeyin Bussiness, nasan Alakar su da mutane, sannan abunda na sani shine, Matar Baba Abba bata hada Yayanta da kowa ba, daga son Yaya, sai son Kudi, a Porthacourt na girma, na son lungu da sakon bullo ma lamura, a nan na gane cewa, in kana so ka ga tashin hankalin Hajia Mairo to ka taba mata abubuwa biyu da suka fi komai mahimmanci a rayuwarta 'YA'YA, da KUDI, a hankali na fara taba Dukiyarta wanda ba nata ba da kuma Yaranta a lokaci guda, da Babban na fara". Karasawa inda Abdulmajeed ke tsaye yayi, Kuka Abdulmajeed yakeyi sosai yace "Ka tuna Yarintar mu?bana tunanin zaka tuna, ina dai so ka sani, Na tsani kaina da na sa k'afa na shure abubuwan yawa dake tsakanin mu a da, na tsani kaina da na cutar da kai don son ganin Mummynku cikin bakinciki, kana tunanin ta ina na cuceka? Bari in gaya ma, A hanyarka ta zuwa Abuja daga Kano a motarka Mercedez Benz akwai Ownership Documents na Abba Abu&Sons Furnishing Company, da wasu signed contracts na other shareholders, daidai Zuba akwai Yarana da suka tareka, suka kwace maka Mota wanda duk wani abu me amfani na cikin Motar wanda yayi causing dinku asarar almost 20%, in har zan tuna da kyau, harta kayan da ke jikinka sai da ka tube musu". Da mamaki suke kallonshi, AbdulMajeed ya bude baki, Daddy ko jinjina kanshi yayi, Mummy ta tuna bakincikin da ta shiga a lokacin ashe Zaid ne. Zaid ya dan dafa Abdulmajeed yace "dont be shocked bro, wannan ba komai bane. A hanyar dawowan Zinatu da Muhsin daga Makaranta, na sa an dauke min Zinatu, wanda akayi requesting 10mil, har mukayi waya" ya juya ya kallesu yace "kun tuna? Ya kalli Ziyada yace, "Har nace miki Ziyaa i'm coming for you?" Well lokacin ne dai, sannan kun tuna Nana Nakowa ai?" be jira amsa ba ya cigaba "Ni na azalzala mata ta hura wuta akayi aurenku, ranar auren Yarana suka je Gidanku, duk wani abu masu amfani suka kwashe, wannan shine Karayar Arzikin ku na farko, wanda sai da kuka saida Gidanku na Abuja wanda ni na siya ba tare da saninku ba don a ganina Gidan Baba na ne, kawai na karbi

Table of Contents

Chapters

169 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});