Chapter 129
Chapter 129
fararen shorts da top karama, ta dan muskuta tace "Bakayi bacci ba" cikin mintunan da sukayi kama da har abada yace "Erhm Eh banyi ba" ya karaso kan Gadon ya zauna, ta tashi zaune duk da cikin duhu ne amma tana hangenshi, tace "Lafiya? Kaje daki zan kwanta" da sauri yace mata "ina jin tsoro ne" ido a ware tace "Wani irin tsoro kuma?" yace "ba zan iya kwana ni kadai ba, ina tsoron dodo ne ko me ake cewa?" Ziyada ta fahimci ya ma raina mata wayau, ta juya mai baya tayi kwanciyarta tare da jan bargo. Sosai ya hau kan Gadon, Gabanta ya hau dukkan ukuuku, a bayanta ya kwanta tare da juyo da ita tana fuskantarshi, a kunnenta ya mata rada "Ni Mijinki ne, be kamata ki juya min baya ba kinji?" a hankali ta gyada kai alamun taji, kare matseta yayi yana binta da wasu kauna a jiki, ganin yanda yake matsowa jikinta ne ya sa ta daburcewa jiki na rawa tace "Zanje Makaranta" Murmushi yayi don ya san ta tsorata dashi ne yace "Yanzu zaki makaranta?" da sauri ta gyada kai tace "Gobe" a takaice yace "na cireki" za tayi magana yace "Makarantarki zaki Koma, baze ko? Chan zaki cigaba da karatunki bata iya amsa shi ba, ta mayar da idanunta ta rufe. A nutse yake nuna mata yanda yake jinta a zuciyarshi, cikin kwanciyar hankali yake nuna mata yanda soyayyarta tai mishi illa batare dayai amfani da kalamai ba. Cikin kwanciyar hankali yake hade zuciyoyinsu da ruhinsu waje daya cikin salon da bazai mantu a wajen su ba har abada. *** *Bayan Wasu yan Kwanakin da ba su kai Sati ba* Soyayya, Aminci da Shakuwa ta darsu a cikin zuciyoyin masoyan nan biyu, burin daya ya kyautata ma daya, a zaman da sukayi da juna sun fahimci halaiyar junansu, sun sake da junansu, sabida Kwanciyar hankali Zaid ya kashe wayoyinsa don samun hutu, shi fita kasashe bude ido be dameshi ba, niyyarshi ya dauketa su tafi chan Porthacourt su danyi hutu ba tare da hayaniya ba, a yanzu ne Zaid yasan cewa ya dade yana cikin bakin duhu, a yanzu ya san cewa akwai wani abu So, a yanzu ya san cewa mutum na zama da tsana da bakinciki a ranshi in yaso, in ko ya so cirewa zai cire ya musanya da So, Allah ne shaidarshi yana son Ziyada, yana son kyautata mata kamar yanda take kyuatata mishi, shiyasa jiya da daddare da ta zo mai da bukatar suje Gidansu be ce komai ba, amma duk da baya so, ba zai hana ba, dole ya hakura suje Gidan, wurin breakfast ya gaya mata ta shirya anjima su tafi, dadi ya kamata, ta tashi ta rungimeshi tana mai godia breakfast din da basu gama ba kenan. ** Aunty Aynarh ta shigo Gidan da Sallama, duk yaran su ka tashi suka rungumeta, fara'a take tayi, ta zube kasa ta gaida Hajjo, Daddy baki har wuya yaga Masoyiya, a mutunce aka gaisa, Mummy sai famar wurga mata harara take ko a jikinta, ta kalle su tace "Allah ya sa ba ku daura abincin Rana ba, na riga na mana Lunch" Zaineema ta murmusa tace "ba mu daura ba ko" tace "yauwa perfect" Key ta mik'a ma Abdulmajeed tace "Ka dauko Kayan Booth" Abdulmajeed ya karba ya kalli Najwa yace "muje ki tayani dauko kaya" tashi tayi ta bi bayanshi suka bar Parlorn, Mummy ta kalli Daddy tace "bari in daura mana Abinci kafin yara su fara jin yunwa" Daddy yace "Maryam bakiji Hajia Aynarh tace ta yo abinci damu ba?" Galala ta kalleshi, kwana biyun nan tsinkata yakeyi gaban jamaa, kar ya mata haka yanzu ta wayance tace"wai sai a kara ko?" Daddy yace "Aa, am sure Abincin da yawa, ki bari da daddare ayi, yanzu dai muci wannan" zama tayi tana wurgar Hajia Aynarh da harara, ita ko hararar mugunta take mata. "PureHeart, i cant wait naga su Maama don nace su bani ke na aura" Murmushi tayi tace "suna nan tafe cikin kwanaki" yace "Allah ne shaidana, ina sonki dominsa" Murmushi tayi tace "main tumase karta hoon" idonshi ya juya sama cikin salon banji me kikace ba, tayi daria tayi gaba, ya bi bayanta yace "Nidai a bar min magana da Indiyanci" dariya tayi tace "Aunty Aynarh na jira" ya bude Booth ya fiddo kayan ciki duka har su carpet, plates da cups, sai Flask kusan kala uku, suka dau iyakan iyawansu suka kai ciki, suka dawo suka dauka sauran. Carpet din suka shimfida a tsakar Gidan, suka jera komai a kai, sai da sukayi Sallahr Azahar suka fito waje kan Carpet din, daidai nan Ziyada ta shigo Gidan da Sallama, duk sukayi kanta suka yayyabeta suna murnan ganinta, Oyoyo Oyoyo, daga baya Zaid ya shigo, baki Mairo ta washe, shi kuwa kamar an aiko mai da Sakon mutuwa, faraar fusakrshi ya dauke dif, Abdulmajeed a karaso gunshi ya mika mai hannu don suyi musabaha, ba yabo ba fallasa ya karba, tare da dan durkusawa ya gaida da Daddy da Hajjo da Aunty Aynarh da ke zaune kan Carpet, duk ya bi yaran gidan da kallo inda suke gaisheshi, tausayinsu ya kamashi, Zaineema yarinyar da yaso kamar me, be manta kaunar da ke tsakaninsu ba, yarinyan da Mairo ke rankwashinshi in ya dauketa, rashin imaninshi ya sa ya rabata da Mijinta, ya zaiyi ya gyara mistake dinnan? Idonshi ya kaiga Najwa wanda take wurga mishi wani mugun kallon "na san ko waye kai" da sauri ya dauke kai yana me jin tsoronta, kar fa ta ganeshi, kar ta tona mai asiri Ziyada a rabu dashi, Allah sa bata ganeshi ba, ji muryar Mairo yayi tana cewa "Ku shigo Parlo sannunku da zuwa" Ziyada tace "Aa Mummy, bari mu zauna a nan so kike ayi picnic din banda mu?" Mairo ta tabe baki tace "ba wani picnic, dangin yarbawa ce tayi son iyawanta wai ta dafo mana Abinci, kamar munce ba mu da abinci". Ziyada tace "Yayy, dama nayi missing Abincin Aunty Aynarh" Mairo takaici kamar ya shideta, tace "Alhaji Zaid kai ka shigo Parlo ka zauna" banza yayi da ita, ba wanda ya lura da ko gaishe da Mairo beyi ba, ya samu wuri kusa da AbdulMajeed ya zauna, wanda Hajjo ke gefenshi Najwa na nata gefen, Mairo tace "Lah, Alhaji, zaman kasa be kamace ka na, please ka shigo ciki" ko kallo bata isheshi ba, Daddy yace "Maryam ki barshi ya zauna cikin Yanuwanshi mana" "'Yanuwanshi" kalmar da Zaid ya fada kenan, ya kalli gefen shi ya ga su Hajjo da Muhsin da Zaineema zaune, dayan gefen Daddy da AbdulMajeed da Zinatu da Ziyada a zaune, sai ya ji shi kamar daya daga cikinsu, ba abunda ya kai bond din Yanuwan jini karfi, ba abunda ya kai feeling din dadi, tabbas yaji wannan connection din, ya ji shi among them, ko yaki ko ya so "they are his Family" yayi Alkawarin gyara laifinshi, "I will fix this , i will fix everything " ya fada a ranshi.. Daddy yace "Oya a bamu mu ci" Hajia Aynarh tace "ai ga yara na nan, su zuba mana" Mairo kamar ta mutu ganin yanda Hajia Aynarh ke fi'ili gaban Daddy. Zaineema ta bude kulolin, Faten Wake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169