Chapter 98
Chapter 98
har fara karatu a makarantar, ba ta yi wani murna ba, amma dai ta gamsu ta fara karatun shine yafi mata alheri, zuwa wannan lokacin ta fara ha'kura da Mk! duk da zuciyar ta tafi son ta koma masa, ha'kurin na dole ne mussaman yadda Inna da Sumayya suke ta yi mata nasihar hakuri da karbar kaddara. Ana jibi zai tafi Uk, inda ya samu gurbi a Jami'ar Bhirmingham zai yi digirin digir gir (P H.D). duk akan harshen turanci. Baya so ya tafi bai yi sallama da Sa'a ba, haka kawai zuciyar sa ke ta azalzalar sai ya mata sallama, kunyar zuwa gidansu yake yi, ta yaya ya saketa, bai mayar da ita ba kuma ya je nemanta, me iyayenta za su dauke shi?. Dabara ta fa'do masa, dan haka lokacin tashin Jawad a makaranta na yi ya bar koami ya 'dauko shi da kansa bai zame ko Ina ba sai legal. gefe ya samu kusa da masallaci a jikin wata bishiyar darbejiya ya yi fakin. Ya jima a zaune a mota cikin rashin abin yi, tunda yanzu bata da waya, ko ta Inna ma bata sha'awar ri'kewa dama shi take nacin kira, zuwa yanzu kuma ta yi matu'kar rage 'kiran nasa, duk da dai idan abin ya juyo mata tana kiransa ko text me dauke da kalaman fatan alheri, da tuni akan girman ladan da me yin ha'kuri ke samu. Ya yi zurfi, cikin tunani ya ji Jawad na cewa "Mami" da 'karfin gaske. Ya zabura ai kuwa itace ta fito a masallaci sanye take cikin dogon hijab har kasa kalar albasa, ya sha guga, fuskarta dauke da farin glass, ba kwalliya ko ka'dan a fuskarta, sannan zuciyar ta ba sukuni amma sai ta yiwa Mk kyau. Da sauri ta 'karaso yayin da Jawad ya balle motar ya fice ya nufeta da gudu, ta tsugunna ta bu'de masa dukkan hannuwanta ya fa'da, sakwanni goma suna haka sannan ta dago shi, ta ce "Halan biyo Malam ka yi akan dole, Na ganka da uniform?" "A a dauko ni ya yi daga school ko gida bai kai ni ba! Ya zarce da cewa "Mami me yasa ba kya daga Ni sama irin yadda Malam ya ke mini?" Da murmushi a fuskarta ta ce "saboda bani da 'karfi Jawad". Maimakon ya yi shiru sai ya sake cewa "yau kin rungume ni, amma a gidan Inna ba kya yi mini haka". "Oh Jawad! to kunya nake ji kar Inna ta ce ban da kunya". Ya kalleta badan ya gane manufar ta ba. Mk da ke jinsu ya bude motar ya fito, suka kalli juna, a nutse Sa'a ta gaishe shi. Ya amsa yana cewa " ya karatun dai ?" Ta amsa da fa'din Alhamdulillah". Kai tsaye ta ce "wani abu zaka yi ne anan?" kai ya girgiza ya ce "sallama na zo yi miki duk yadda nake cikin bacin rai ba zan iya tafiya ban miki sallama ba, jibi idan ubangiji ya nuna mana zan tafi ingilah, Ina fatan za ki yi karatun ki da kyau, Ina miki fatan dukkan alheri a rayuwar ki" Da ga jin yadda ya ke magana kasan cikin rauni yake yinta. Ita kuma tuni hawaye ya goce mata, ta yi 'kasa da kanta ta kasa furta ko da kalma guda. Takaici ke cinta ta ko'ina, tafiyar da ya dinga cin burin dai ita da Jawad zai tafi, har ta yi karatu ta kuma haihu acan sai gashi tafiya ta zo amma ba ita. Kusan kullum sai ta ci karo da abin da ta rasa a dalilin rashin Mk. Ya nisa ya ce " duk hidimar ki ta makaranta tana hannun Mahmoud, zaki bude account, fatana kar ki tambayi Baffah kome, ke kanwata ce, ko ba ma tare zan miki komai Dan rayuwar ki ta inganta, ina miki fatan alheri a rayuwar ki ta gaba, na yafe miki dukkan kurakuran da kika mini, fatan nima zaki yafe mini inda na musguna miki". Ta 'dago idanuwanta cike taf da 'kwalla ta ce "Baka mini komai ba sai alheri, ban san wani abi da kai mini ba face mutunci da karramawa, nima ina maka fatan alheri, Allah ya bada sa'a ya tsareka a duk inda zaka samu kanka". Sai kuma kuka sosai ya 'kwace mata, bai yi yun'kurin hanata ba, domin shi kansa da yake namiji ji yake tamkar ya yi ta zunduma ihu ko a fahimci Halin da yake ciki. Idanuwansa sun yi jawur tabbacin yana cikin damuwa mai yawa. Tsawon lokaci tana kuka kafin ya ce "it's okay ya isa haka zuwa yanzu ai kin dan samu relief, kukan ya isa haka share fuskar ki Jawad na kallon ki fa". Ta dago ta sake kallonsa ta ce "Da gaske ka yafe mini Malam". Da sauri ya'daga kansa yana fa'din har zuciyata". Murmushi mai ha'de da hawaye ya subuce mata ta ce " zan yarda ka yafe mini ne, idan har ka mayar da Ni, zan gamsu da gaske ni 'kanwarka ce idan ka mini adalci irin yadda yaya zai yiwa 'kanwarsa na duk girman laifinta ba zai janye jinin da ya hada su ba. Ka mayar da ni zan jiraka ko da baza mu bika". Ta yi shiru tana shanye kukan da yake son kwace mata. Ta nisa ta ce "Har gaban abada ba zan ri'ke waya ba, ba zan sake mu'amala da su Halima ba, sai abin da kake da dama shi zaka yi mini Dan Allah kar ka tafi ka barni a haka". Ya nisa yana jin wani irin abu ya shake shi, ya ce "Sa'adatu ki barwa Allah ya mana zabi kin ji, ina son ki har yau, idan 'kaddarar zaman bata 'kare ba ubangiji zai sake hada mu, amma ni yanzu fatana ki cire damuwa a ranki, ki fuskanci karatun ki, shi zai taimake ki a ko ina zaki samu kanki, duk abin da ya taso miki ki fada mini kai tsaye ki ji tamkar Nima Sumayya ne a gurin ki". Ta kasa yin magana sai goge fuskar ta take duk ta bata Hijabin nata, haka ya shiga mota suka tafi Jawad ya yi lakwas, ya zama marar kuzari adalilin Halin da ya ga uwarsa a ciki. A hanya ya dinga fa'din"Malam sai yaushe Mami zata zo ta dauke ni, mu koma gidan mu, me yasa kullum sai ta yi kuka? ko abinci bata ci sai Inna ta zauna kusa da ita, me take yi anan din?" Ya 'kasa bude Baki ya amsa masa, ganin da Jawad ya yi bai kula shi, yasa shima ya yi shiru dan yasan idan ya dame shi zai mammake shi ne. A kofar gidan Hajiya ya ajiye shi, ya juya karban wani sakon, sukuku Hajiya ta ga Jawad ya shigo Mata, ta dinga tambayar me ya same shi a Ina kuma ya Da'de ?. Ai kuwa ya marairaice ya ce "Mami ce take ta kuka". "A ina ka ga Mamin?" "Malam ne ya kai mu, tana wani waje babba har da masallaci, tana ta kuka, tana ce masa ya mayar da mu gidan mu". Jikin Hajiya ya mutu ta ayyana idan Mukhtar bai yi taka tsan tsan ba zai jefa 'kinsa a zuciyar 'dansa. Wacce irin zuciya ne da shi haka mai tauri bata sani ba, kana son
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157