Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya kasa. Don haka sai ya tsaya a gabansu, bai fito ba, sai ya lalubo lambar da Jawad ya kira shi da ita dazu, ya san tabbas layinta ne duk kuwa da ba ainihin layin ta ba ne daya santa da shi. Ya danna alamar kira, yana hango ta tana ta kici-kici da jakarta wurin lalubo wayar, amma abin mamaki ya ga ta fito da wayar amma ba ta dauka ba har ta katse, mamaki ya kama shi wai yaushe Sa'adah ta ko yi jarumta akan lamarinsa ne? Ya yi jim yana tunanin rabon da Sa'adah ta shiga harkarsa, ba shakka ba lokaci ne Mai tsayi, ba ta sake neman shi ba, ba ta sake duba dukkan lamarin sa ba, ta yi fatali da shi da dukkan soyayyarshi, abin da ya dade yana mamakinsa. bai daddaraba, ya sake 'kira tana gab da tsinkewa ta daga ba ta yi magana ba, amma dai ta kara a kunnen ta, sanin halinta da ya yi na ba za ta fara magana ba, yasa shi cewa, "Ke na gani a titi a na muku gyaran mota?". Cikin rashin nuna damuwa ta ce "A a ba ni ba ce." Bai yi mamakin amsarta ba ya ce. "Amma ba ke ce nake hangowa a tsaye kina amsa wayar nan daidai jikin Alheri bread🍞 ba?" Shiru ta masa sai ji ya yi ta ma ka'tse wayar gaba'daya. Shiru ya yi ranshi na suya ya na sake jaddada halayyarta a jininta ne ba za ta sauya ba. Har ya ta da motar da niyyar barin wajen ta je ta 'karata, sai kuma ya tuna uwar Jawad ce tilon 'dansa, ya tabbatar da tare yake da Jawad din, ba zai yarda su tafi su bar Maminshi a bayan gari jejin Allah ba, ga yamma ta yi likis sosai, sanyin da ake 'dan busawa ya sake taimaka wa garin ya yi dan duhu, don haka sai ya fito bayan ya kulle motar ya nufe su. Yana zuwa ya ga har da Zainab Ma'aji da wasu mata biyu da bai gane su ba. Ita ko Zainab tana ganin shi ta saki fuska."Lah! Uncle kai ne ashe." Ta gaishe shi irin gaisuwar da dalibi ke yi idan ya ga malamin da ya koyar da shi a baya. Shi ma ya amsa da jin dadin girmama shi da Zainab ke yi tun fil azal. Hannu ya mi'ka ya dauki yaronta Walid ya masa wasa sannan ya ce, "Motar taku lalacewa ta yi ne?". "E wallahi ga mu nan dai ana ta faman gyara". "To ku zo mana mu wuce tun da ba tabbacin za ta gyaru yanzu". Kallo ta kai ga Sa'adah da ta koma baya ta yi kamar ba ta gan shi ba, ta kuma cika ta yi fam kamar kububuwa. Zainab ta ce "To uncle bari na yi wa abokan tafiyar tamu magana." "Okay" Kawai ya ce, yana ci gaba da wasa da Walid dake ta bingila mishi dariya tamkar ya san shi. Bayani Zainab ta musu kamar yadda ya bu'kata, dukkan su sun amince, su bi shi, amma ban da Sa'ada. Don haka Zainab da 'yan uwanta su ma suka janye tun da dai ai sun san saboda ita ya tsaya har ya nemi ya taimake su, to kuwa ta ya ya za su ce za su bi shi alhalin ita ta yi rantsuwar gara ta kwana a nan da ta shiga motarsa! A matu'kar kunyace Zainab take ba shi ha'kuri tare da ba shi uzirin direban ba zai ji dadi ba, ya san sarai Sa'ada ce ta'ki amincewa, amma sai ya ce ai zan sallame shi ku zo mu tafi kawai. Nan ma sai ta sake dora wa 'yan uwanta laifi akan yayarsu tace ba zasu sab'awa direban al'kawari ba. Ya jinjina hankali da Zainab ke da shi, duk da ya san 'kawar ta ce ta'ki amincewa, amma ba ta fadi hakan ba, sai kariya take ta bayarwa, ina ma tun farko Sa'ada ita ta ri'ka a matsayin 'kawa, ba bara gurbi irin su Halima da Safina ba? Wanda 'kawacenta da su bai amfane ta da komi ba sai muguwar asara da nadama, tunda sun mata ingiza mai kantu ta yarda har ta tsinke igiyar aurenta, a yanzu kuma sun bar ta sun koma suna zunden ta. Don haka sai yace "To shi kenan ba damuwa ya matsa ga bakaniken dake ta iyakar kokarin shi don ya ga motar ta tashi. magana suke yi da direba, cikin ikon Allah ba a wani dauki lokaci sosai ba motar ta gyaru, amma har an yi sallar Maghriba, dan haka malam da direban suka yi jam'i suka yi sallarsu, yayin da matan suka shiga wani kewaye su ka yi ta su. Bai yarda ya tafi ba sai da ya ga tashin su sannan ya taka ya isa inda motarsa take shi ma ya bi su a baya. A cikin motar kuwa yayyen Zainab sai caccakar Sa'ada suke da rashin kirkinta, "A haka kike son komawa gidan nasa? Ba kya girmama shi, a gaban kowa za ki iya keta shi?" Cikin turo baki ta ce "Ni fa Anty da ne na yi haukan banza na son sai ya mayar da ni, yanzu kuwa ko ni da shi muka rage ba na sonsa ba zan koma ba" Cikin fushi ita ma Anty Asiya wadda ita Zainab ke bi, kuma da ita duk a ka yi gwagwarmayar su Sa'adah, ta ce, "Ai shima ba son naki yake ba, shashasha da ba ta san me ya kamata ba." Dattijon dake jan motar ya ce, "Um'um fa! Ba'a shiga lamarin mace da namiji, ai koni da yau na fara ganin su na hango soyayyarta mai yawa a idonsa da gangar jikinsa, ita ma kuma duk wannan kumburin da take yi da fiffi'ka duk soyayyar ce, da alama dai kishi ne ke dawainiya da ita a kansa, dan na ga fishi take mai tsanani da shi!" Dukkan motar a kasa dariya a na cewa Baba ashe duk ka gano su? Yace , "Haba yara mu da muka ga jiya muka yau, ku duba fa duk iya shegen da ta yi akan ba za ku bi shi ba, bai fa iya tafiya ba har sai da ya ga tashinmu, wannan kadai ya isa kowa yasa lunzami a bakinshi akan lamarinsu, suna da yara ne?" Zainab ce ta ce "Yaro ne daya har ya fara girma, shi suka jewa visiting" Ya ce, "Ai shike nan magana ta 'kare, ko kowa bai musu sulhu ba, yaron zai zama tsanin afuwa a tsakaninsu, mu yi musu addu'ar fatan alheri, amma soyayya akwai ta" Aka sake sa dariya ban da Sa'ada da ta yi kicin-kicin da fuska. Tsohon ya sake cewa, "Ina cewa da za mu zo ita ce a gaban motar nan haka da za mu dawo,har muka zo inda motar ta lalace ita ce a gaban?amma ina ganinsu da za ta shiga gaba ya galla mata harara sai kawai naga ta shige baya." Gabadaya aka sake dariya har da Sa'ada wadda ita ta karfin halin wannan bawan Allah ne, ita ba ta ga harara ba, ta san kuma tabbas bai yi 'karya ba, kaifin idon Malam ne yasa ta kasa shiga gaban motar wani akan idonsa, sai ta bige da cewa

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});