Chapter 41
Chapter 41
juyo kan motar, ga ta ita ce a gefen hannunsu, ma'ana tana bude kofa dole kowa ya gan ta. A tsarin mahaifinta ba ma MK kawai ba, bai kamata mutanen gurin su gan ta ta fito a motar saurayi a irin wannan lokacin ba. Ta rasa yadda za ta yi ta fita, musamman yadda kayan jikinta suka kamata sosai duk da mayafin babba ne. Sai dai shara-shara ne, hijabi ta saka da za ta fito, saboda Inna ba za ta barta ta fita da wannan dinkin ba wanda anko ne telan Safina ya dinka musu, da ma nufinta tana isa zaure ta maka Hijabinta baki alaikum. Kunya da tozarci iri-iri suka dinga bin ilahirin jikinta, ganin yadda ta kasa fita a motar ya sanya Khalil fita ya zaga, ido biyu su ka yi da MK ya hura hanci ya dauke kai, ya bude gaban motar yana fadin fito, da kyar ta fito fuskarta a kasa ta kuma ja mayafin har kanta aka bita da ido, mazan da suke gun dukkansu a ransu yaba surarta suke yi har daya a cikin su wanda dan kwaya ne ya kasa hakuri, a fili ya furta "Kai waccan baby an zuba mata halitta Billahillazi da ina da kudi da na yi kerwa da ita." Tun tsayuwar motar MK ya ji zuciyarsa ta tsinke musamman da ya ga mace a gaban motar ta kare fuskarta, haka kawai ya dinga fatan kar ta kasance Sa'adah ce, ya san zai yi wahalar gaske ta zama ita ce, amma sai ya kasa nutsuwa, a lokacin da ya ga Khalil ya fito da gadara sai ya tabbatar Sa'adatu ce, take ya ji wani irin matsanancin kishi ya kama shi, irin kishin da yake danne soyayya. Maganar da wannan saurayin ya yi na yabon surar ta sai ya sake ninka bacin ransa wanda bai taba Jin irin sa a tsawon rayuwarsa ba. Zuciyarsa ta yi zafi, take ya ji yawun bakinsa ya kafe makogaronsa ya bushe, kansa ya sara da wani irin ciwo mai tsananin gaske. Ashe Sa'adah da Khalil ta fita, ashe shi yasa ta kashe wayarta, don ta nuna masa tana tare da wanda ya fi shi, ta kuma yarda ya kawo ta har titin da take da tabbacin zai iya ganin su a tare, karo na farko da ya ji ya yi kuskuren barin Farida saboda Sa'adah. Ya tabbatar ta fi ta son sa kawai dai shi Sa'adah ce ta fi shiga zuciyarsa, kuma ta fi daukar hankalinsa. Ko ta kan gyaran mashin din bai tsaya ba, ya tari abin hawa ya nufi gidansu, kafin ya isa wani irin zazzabi da azababben ciwon kai sun masa mugun kamu. Alkalamin *SURAYYA DAHIRU* ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *TALLAH*. _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ 45-46 Tana shiga zauren gidan ta fito da hijab ta sanya, sukuku ta shiga gidan. A tsakar gidan ta sami iyayenta. Tsoron da ke cikin zuciyarta ya sake bayyana a fuskarta da jikinta. Baffa ne kawai ya amsa sallamar, da 'kyar ta tsugunna ta gaishe shi, ya amsa ba sakin fuska, ya kalle ta fuska ba wasa ya ce, "Daga ina ki ke?" Cikin rawar murya irin ta rashin gaskiya ta ce, "Zainab na raka gidan yayarta kuma sai da na tambayi Inna." A kufule Inna ta ce, "Tabbas kin tambaye ni amma ce mini kika yi ba za ku dade ba, don haka na gode miki da cika al'kawari." Ganin yadda ran Inna ya baci sosai sai shi kuma ya sassauta, ya mata nasiha tare da cewa, "yarinyar kirki in dai ta san kanta, killace kanta take yi a gida, bai kamata dare ya riske ta a waje ba." Har ya sallame ta sai kuma ya ce, "Yawwa dama zan fada miki, aurenki bayan sallah za a yi, nan da wata uku kenan. Bayan haka kuma na sanar da iyayen yaron cewar kar ya yi lefe, ni ma kuma ba zan wahalar da kaina wurin saya masa kayan daki ba, ke zan ba shi ina kuma da yakinin na miki tarbiyar da zai sami nutsuwa da ke. Uwarki kuma ta koya miki yadda zai yi alfahari da ke a matsayin uwar yayansa. Haka na yi wa Sumayya har yau din nan da ta kai shekaru goma a dakinta ban taba jin ance mini ga wani abu na kaico daga gare ta ba, mijinta kullum kara girmama mu yake yi, Ina fatan ki yi koyi da ita, Tashi ki je." Ta mike ta wuce dakinta cikin wani irin yanayi, tana zuwa ta fadi kasa ta fara kuka kasa-kasa, tana jin karshen tozarci an yi mata. Ta ya ya za a dinga hada Sumayya da ita, ai ba lokacin su daya ba, sannan ba iyayen mijinsu daya ba, a wannan zamanin ma an kai yarinya da kayan daki idan ba na alfarma ba ne, dangin miji suna yi wa yarinyar izgili da habaici, to ina kuma ita da za a kai ta tsurarta? Wanne irin raini da kaskanci za a janyo mata? Ba'kin cikinta ya ninku ta rasa inda za ta tsoma ranta. Ashe shi yasa MK yake mata gadara da isa, saboda an nuna masa sadaka za a ba shi an dauke masa lefe? Shima kuma kar ya sa rai za a je a yi masa jere. Ba ta san lokacin da ta bude murya ta dinga zunduma ihu ba. Daga Inna har Baffa a kidime suka mike suna rige-rigen isa dakinta a tuninsu wani abin tsoro ne a dakin, ko maciji ko kunama ta harbeta. Sai dai ganin ta ras illah kukan da ta bare baki tana yin sa tamkar yarinya yar karama yasa suka yi cirko-cirko! Baffa ne ya ce, "Mene ne ya saki wannan ihun sai ka ce wacce ba ta zuwa Islamiyya, ba za ki ambaci Allah ba! Sai ki cika mana kunne da kuka har da ihu?" Cikin kuka sosai ta ce, "Ka taimake ni Baffa! kar ka kai ni ba kayan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157