Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 62

Chapter 62

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

abin ba ne, kullum ni nake bin ki dakinki for more than a year, ke mai yasa yau ba za ki zo nan ba, ko kin zo na kore ki?" Jikinta ya yi sanyi da jin kalmar Sa'adatu a bakinsa ta san fushi yake da ita. A hankali ta furta, "So nake ka fasa tafiyarku Lagos". "Ba zai yiwu ba, na riga da na fada mata gobe tasa a tare ni a Airport, kuma sai na koma nace na fasa zuwan?". Ta fara kuka tana fadin, "Ba na son tashin hankali Uncle, na roke ka kar ka raba ni da yarona". "Yau kusan sati ina fama da ke, ba irin ha'kuri da rarrashi da ban miki ba, amma kin runtse ido kina mini diban albarka, ko daukar yaron nan sai na miki wuta-wuta kike yi, dazu ga ki, ga shi, amma kika bar shi yana tsala kuka, zan zauna kullum a gida ne? Dole zan fita. Bayan haka kin daina yin komai a gidan nan tun daga kan shara, da girki, duk ban ce komai ba, ina yi, duk da haka ban tsira ba, duk maganar da ta zo bakin ki fada mini kike yi, har ki kalli idona ki sa mini sharadi idan ina son zaman lafiya sai na yi kaza". Jikinta ya sake yin laushi, bai ba ta damar yin magana ba ya zarce da fadin, "Kin yi strike din wanka, da yi mini magana, akan cikin da ba ni kadai na samar da shi ba, ikon Allah ne. Kin san adadin matan da suke jika filon su duk dare a dalilin rashin haihuwa? Kin san adadin matan da suke fuskantar tashin hankali akan rashin haihuwa, ALLAH kadai Ya san adadin ba'kin cikin da irin wadaccan matan da suke cikin jarrabawar rashin haihuwa suke ciki, ke Allah ya ba ki, ba tare da kin sha wahala ba, ya sake kara miki, maimakon ki zama cikin bayi masu godiya, sai kika zama cikin masu butulci". Zuciyarta ta yi sanyi, salama ta shige ta, ta fara fadin, "Astagafirillah!" A zuciya. A fili kuma sai ta tsinci kanta da cewa "Ka yi hakuri". Dadi ya lullube shi, amma bai nuna ba, ya ce "Ya wuce." A gajar ce. Ya zuba mata ido yana ganin yadda idonta suka fada ciki, bayan rashin lafiya ya tabbatar har da yunwa ke sakadar ta. Kafin ya yi magana ya ji tana cewa yunwa na ke ji. Ya basar ya ce, "Babu kayan abinci ne a gidan?" "Kwana biyun nan fa ba ni da lafiya, na san kuma idan ba na jin dadi kai ne kake dafa mana". Ya harareta kadan sannan ya furta, "To na daina yi tunda ba kya gode mini, ba kya ganin kokarina". Ta yi kasa da kai, sai kuma ta mike ta shiga toilet din dakin, ta yi wanka sosai, tana ayyana yau kwananta uku ko hudu ba wanka, ta fito ta tafi dakinta, ta shirya cikin Riga da wando iya guiwa na barci, ta feshe jikinta da turararukanta masu tsuma zuciya, sannan ta koma dakinsa. Inda ta tashi nan ta sake zama, ya dago ya kalle ta, yana jin tamkar ya rungume ta, fiye da sati bai ganta a nutse haka ba, kamshinta, sai ratsa shi yake yi. Ya dan kalle ta kadan sannan ya ce "Ba za ki kashe fitilar ba, na ce miki barci nake son yi kada na makara". Kafin ta yi magana Jawad ya farka, ya fara kukan neman abinci. Da sauri MK ya dauke shi, sannan ya fara hada masa Madararsa da take kan side drower, tun dare ya ajiye komai na bu'katar Jawad kusa da shi, jego ya same shi a kwatsam😃 A kunyace ta matsa kusa da shi sosai, ta mi'ka dukkan hannu ta ce "Kawo shi". Bai musa ba don kuwa, so yake ta ba shi nono, amma ya riga da ya kudire ba zai kuma rokon ta ta shayar da shi ba. Ya mika mata, yana ci gaba da kokarin hada masa madara, rabin hankalinsa kuma na kan Sa'adah da I'm ya ga ta kwantar da Jawad a jikinta ta na kiciniyar shayar da shi. Da'di ya kama shi, amma sai ya waske da cewa "Gaskiya da ba ki ba shi ba, tunda dai ya saba yinin yau bai sha ba, da an bar shi, tunda gobe ai ba sha zai yi ba". Tura baki ta yi, sannan ta ce "Zan ba shi mana". "Lagos din za ki bi shi, ki ba shi?" Cikin shagwabe fuska da kuma hawaye ta ce "Na ba ka hakuri fa, ka ce ka ha'kura, ba sai a fasa tafiyar ba". Ta yi shiru yana kallon ta, yana kuma kallon yadda Jawad ke ta faman shan nono ba kakkautawa. Tsintar kansa ya yi da tambayar ta mai za ki ci?" Kanta a kasa ta ce "Komai na samu zan ci, amma mai zafi" Ya kalli waya ya ga shadayan dare, ya mike ya shiga kicin ya dade a tsaye yana tunanin mai zai mata mai sauki? Ya bude fridge ya ga akwai ragowan ferfesun naman kaza duk da ba shi da wani yawa, ya fito da shi, a tunaninsa ta cinye tunda yasan ta da son kaza, sannan ta ki yin girki. Ya dumama ya juye a bowl, ya hada tea sannan ya dauko bread, duk ya shirya a kan tray, ya dauka ya kai mata dakin. Har a lokacin kuma Jawad sha yake yi. Kusa da ita MK ya zauna, ya ce "Kawo shi ki ci abincin kar ya huce, a hankali ta dago yaron da yake shirin yin barci, ta mi'ka masa, Jawad jin an raba shi da abincin sa, yasa kuka, sai dai da yake ya koshi, dan jijjiga shi kadan Babansa ya yi ya koma barcinsa, yayin da Sa'adah take ta cin abinci tamkar tana ci da wani. Sai da gama ta gane jirin da ta yini da shi na yunwa ne. "Uncle ba ka ba ni ruwa ba, ya sake zuba mata wata irin hararar kauna ya ce, "Kar ki sha ruwan, ke wannan abincin ma dana hado miki biyan ki na yi, kin shayar min da yaro na, saboda adalcina, ni ma na miki ya kamata". Dariya ta kama ta sai ta bige da cewa, "Ke nan dai Jawad ya fi ni a gunka?" Ta fada cike da shagwaba. Shiru ya mata, ga mamakinsa, sai ji ya yi ta kafa masa kuka, ya tashi ya zauna, ya kalle ta sosai ya ce "Kin koshi ba! Shi yasa za ki dora daga inda kika tsaya? To Allah ya baki sa'a". Ta kara karfin kukanta tana fadin, "Ruwa zan sha, wayyo cikina". Kan dole ya tashi ya dauki tray din gabanta, ya fice, ya dawo da ruwan ya dangwarar, yana fadin "Ki ci gaba da yi mini iyashege". Haka ta dauki ruwan ta sha, sannan ta ce, "Thank you dear!" Bai kulata ba, ya ce "Idan kin gama sai ki kashe mana fitilar". Da rarrafe ta isa gefen gadon da yake kwance, a durkushen ta kamo hannuwansa ta ri'ke, cikin rauni ta ce, "Am sorry dear, na gane ban kyauta ba, ka yi mini afuwa, ka manta duk wani inconveniences da ya faru pls". Bai ja ba , ya ce "Shike nan

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});