Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 90

Chapter 90

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

salama da nadamaar *HALIN* da nake ciki, na yi al'kawari zan jure duk wani kalar fishinka, ba zan yi abun da za mu kai ga lalata auren mu ba". Tausayinta ya ratsa su dukkan su, gurin ya dauki shiru, sai fama suke da tausayin su, kowa ya lura laifin Sa'adah ne, amma Mk ya kafe laifin sa ne, su gafarce shi, haka aka tashi ana addu'ar, Allah ya daidaita su. Bayan tafiyar su Mk, kukan Sa'adah ya karu, sosai ta ke rusa kuka, yayin da iyayen ta suke fadin ba ki ma fara kuka ba, domin sai nan gaba za ki gane asarar da ki ka yi ba 'yar 'karama bace. Zazzabi mai zafi ya rufe ta, hakoronta suka dinga karo da juna, jikinta sai rawa yake tamkar mazari. Da farko shareta suka yi, sai da suka ga abin na sake 'kamari sannan Inna ta kai mata 'dauki, tana sa hannu a jikinta ta ji zafi zau. Har dare tana cikin wannan yanayin, kan dole Baffa ya 'kira wani jami'in lafiya, mai chemist a unguwar ya zo ya bata taimakon gaggawa. Haka al'amarin ya kasance da Mk, bayan sunje sun sauke Baba Isa, yace da Mahmoud gidan Hajiyar Bichi zai maida shi, suna shiga falon nata ya yanke jiki ya fadi, alma'arin da ya matu'kar tayar da hankalin su, 'Karfi ya fita a gigice, ya yi sa'a ya tarar da Abbas na gida, ya 'Kira shi suka ciccibi Mk zuwa wani asibiti mai zaman kansa mafi kusa, dole aka kwantar da shi sakamakon jininsa da ya yi mugun hawa, baya ga haka yana cikin damuwa da ya ke bukatar hutu.. Abbas ne ya zauna da shi, sauran yan'uwansu kullum suna zarya a asibitin, haka nan Mahmoud kullum sau biyu yake zuwa duba shi. Har zuwa wannan lokacin Jawad na gidan 'Karfi bai san me yake faruwa ba, takanas Mahmoudya je ya debo masa uniform da kayansa kullum da safe zai kai shi, idan anta shi kuwa mai aikin matar ke hawa adaidaita ta dauko shi, idan ya tambayi Mamin shi ko Malam sai ace sun yi tafiya ne, bai damu ba, tun tafiyarsu Abuja ya saba zama gidan Mahmoud Karfi. Kwanansa uku aka sallame shi, tare da gargadin ya rage damuwa, ya kuma kula da shan maganinsa. Haka ya tattare dakin Hajiya, tun tana ki, har ta ha'kura ta barshi, kan dole ta koma kwana a babban falon su, da suke zama ayi dab dabla lokacin Hajiya Babba. Kwanansa biyu a dakinta yana warware wa, a cikon na uku ne ganin ya dan sami sauki har ya ci abinci, yasa ta bijiro da maganar Sa'adah. "Matu'kar kana son mu shirya to ka dawo da matarka, rashinta ne duk ya susuta ka haka, idan kuwa ka 'ki jin maganata kar kuma takowa inda na ke, ko gaisuwar ka bana so". Hankalin sa ya tashi, ya fara 'ko'karin fahimtar da ita da hujjoji, amma fur ta hau dokin na 'ki. Ganin da gaske ta ke yi, shikuma a yanzu wani irin tsoro da firgicin zama da Sa'adah ne ya ke kama shi, bai ta'ba tunanin za ta yi abin da ta yi ba, mussaman yadda ya ke wadata da komai, uwa uba kuma yadda ya ke tarairayarta da gudun zuciyar ta, idan har hakan bai sa ta kiyaye masa amana ba, bai ga kuma me zai mata ba. Kansa har zafi yake wurin tunanin, me yasa ta yin hakan? Ya tabbatar shi baya ha'intar ta akan me ita zata ha"ince shi? Wani irin tsimin bacin rai ya taso masa, mai hade da kishin da ya haddasa tsanar Sa'adah, ya kasa bu'de baki ya yi magana kawai ya kife kansa akan guiwowinyasa ya fashe mata da kuka tamkar yana cikin shekarun 'kuruciya. Wannan kukan ya matu'kar ta'ba zuciyar Hajiya, ta shiga ru'dani da wasiwasi akan lamarin Sa'adatu, kan dole, ta ha'kur'kurtar da zuciyar ta, ta ce ta janye takunkumin dolen da ta yi masa. Amma a zuciyarta sai hasashen wanne irin abu ta yi mai muni haka?. Sati guda da faruwar wannan lamarin, amma har lokacin Sa'adah na kwance ba lafiya., saboda ta 'kuntata zuciyar ta, ta 'ki cin abinci, kullum cikin kuka ta ke, ta yi wata irin rama mai tayar da hankali, kuka ta yi shi irin wadda ba ta yi tunanin akwai mahalu'kin da ya yi irinsa ba, ko ya ya ta ayyana Mk ya saketa, shikenan sun rabu? sai dai Inna ta jiyo ta 'barke da kuka tana fadin na tafka asara, na yi nadama. Sannu a hankali zance ya shiga kunnuwan dangi, kowa ya ji mutuwar auren sai ya shiga alhini saboda yadda aka shaida soyayyar da Mk ya ke yiwa Sa'adah, mussaman Auntyn Lagos, Maman Gombe da Samira, hankalinsu ba karamin tashi ya yi ba, da kuka Antin Lagos ta 'kira Hajiya tana tambayarta gaskiyar magana, cike da tausayi Hajiya ta tabbatar mata sun rabu tabbas. Da rawar murya take fadin "Hajiya ki matsa masa ya dawo da ita, na tabbatar duk inda ya ke, ba ya cikin nutsuwa, yana sonta". "Hmmm kawai ki musu addu'a amma lamarin na su akwai tashin hankali." Inji Hajiya . Wata guda Mk ya 'dan wartsake, ya koma harkokinsa da 'karfin zuciya irin ta namiji, sai dai abin na nan ma'kale a zuciyar sa yana jin har ya koma ga mahallicinsa ba zai manta ba, idan ya tuna dalilan da zai hana Sa'adah ta bashi wayar nan sai ya ji bugun zuciyar sa ya karu, wani lokacin har jiri ke dibansa. Ga Sa'a kuwa wannan watan ta cinye shi ne a kwance tana 'dan'danar azabar ciwon so da nadama, tunda gyatumarsu ta kawo ta duniya bata taba fuskantar tashin hankali irin wadda ta ke ciki ba, fata take mutuwa ta dauketa ta huta da wannan zugin da zuciyar ta take mata, inama ta bashi wayar nan ya gani? Wata'kila da ba zai zafafa lamarin har haka ba, tun shekaranjiya da ya aiko mata wasu cikin kayanta shake cikin akwati babba, yini ta yi a ranar tana kuka, ba abin da ta ke fata irin ta ji ko da Muryar Mk, amma abin ya faskara, ga tunanin Jawad rabon da ta ganshi tun ranar da suka rabu da Babansa, ta yi dalilin da suke rayuwa a wuri daban daban, wannan kadai ya isheta ladabtarwa. Cikin wannan 'kangin ta sake cinye wani watan har da 'karin kwanaki goma, zullumi ya ishi Sa'a, saboda kwanakin iddarta na gab da kammala, duk wadda ya ganta yanzu, muddin ya santa a wattannin baya, sai ya tausaya mata, gashi dai ba ta rasa komai ba, amma ta rasa kwanciyar hankali, satin ta biyu a gidan Mk ya aiko da kayan abinci kala kala wadda za su kwashe rabin shekara suna ci, sai kuma ya mata siyayyar komai na bukatunta tun daga kan kayan shayi har sabulai, da tarkacen abubuwan da zata bu'kata, amma ko taba su ba ta yi ba, hakanan abinci sai Inna ta tausaya mata, ta zauna kusa da ita, ta matsa mata sannan za ta yafita . A lokacin Sa'adah ta fahimci ba abin da yafi nutsuwar zuciya da'di, addu'a ta ke sosai akan ta sami sau'kin tashin hankalin da take ciki, idan ta ji yo su Baffah na hira har da raha shi

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});